BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
'Zargin ƙwace babura 17 na ƴanbindiga ne ya yi sanadin sace mutane a Kajuru'
A game da adadin mutanen da aka sace, sarkin ya nanata cewa lallai an yi garkuwa da mutum 177 ne a ƙauyen, amma mutum 11 sun kuɓuta.
KAI TSAYE, Sojoji sun gano makeken kabarin ƴan Boko Haram a yankin Timbuktu
Wannan shafi ne da kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 21 ga watan Janairun 2026.
BBC ta samu hotuna da bidiyon yadda aka kashe masu zanga-zanga a Iran
Hotunan waɗanda ba su da kyawun gani, sun nuna gawarwaki sama da 326 cikin jini da fuskoki a kumbure - ciki har da mata 18.
Yadda 'yansanda suka yi amai suka lashe kan sace mutane a Kaduna
A ranar Litinin aka fara samun rahotannin cewa wasu mahara sun shiga ƙauyen na Kurmin Wali tare da sace mutane kimanin 170 a yankin mai fama da matsalar tsaro, lamarin da ƴansanda suka musanta da farko.
Mene ne hukuncin wanda ya shiga azumi da ramuwar bara?
Azumi na cikin shika-shikan musulunci guda biyar, wanda hakan ya sa ibadar ta zama dole ga dukkan musulmin da ya cika sharuɗanta.
Yadda ƙasashen Turai ke shirin yin fito-na-fito da Trump kan yunƙurinsa na mallakar Greenland
Donald Trump ya ci gaba da jajircewa kan batunsa na son mallakar yankin Greenland. Ya bayyana a ranar Litinin cewa Amurka na son tsibirin ne kan dalilai na tsaro.
Ya kamata a gaggauta ceto mutanen da aka sace a Kaduna - Amnesty
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 20 ga watan Janairun 2026.
Abin da aka tattauna tsakanin Abba da Tinubu
Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke ƙara bayyana batun yunƙurinsa na sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar APC.
Rawar salsa: Hanya mai sauƙi ta warware ciwon baya
Wannan atisayen zai iya taimakon dattawa waɗanda suke fama da ciwon baya, ko kuma waɗanda suke wahalar tafiya bayan tiyata.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 22 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 21 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 21 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 21 Janairu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Ƴan wasan City za su mayar wa magoya baya ƙungiyar kuɗin tikitin kallon wasan Bodo
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 18 zuwa 30 ga Janairun 2026
Man U na zawarcin Kovac da Tuchel a matsayin sabon kocinta, Crystal Palace na son Guessand
Kocin Borussia Dortmund Niko Kovac da kocin Ingila Thomas Tuchel da Roberto de Zerbi na Marseille na cikin wadanda Manchester United ke son ta dauka a matsayin kocinta.
Sadio Mane: Daga ƙwallon ƙafa a layi zuwa jigon tamaula a Afirka
Sadio Mane ya lashe kofuna da dama, ciki har da zakarun turai da Afcon guda biyu.
'Abin kunya' da 'takaici' - hargitsin da ya lalata nasarar Senegal
Senegal ta ɗauki kofin Afirka karo na biyu, bayan doke Moroko a wasan ƙarshe - to amma wasan na cike da abubuwa, ciki har da ficewa daga fili da ƴan wasan Senegal suka yi bayan bai wa Moroko bugun fenareti ana dab da tashi daga wasan.
Me ya sa koci ɗan Ingila bai taɓa lashe Premier League ba - wa zai fara ɗauka?
Menene dalilin da ya sa kociya ƴan Ingila ba su taɓa lashe kofin Premier League - yaushe ne za kuma su ɗauka?
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Abin da muka sani kan 'sace mutum 160' a Kaduna
A ranar Litinin jaridun Najeriya da dama sun bayar da rahoton sace mutane fiye da 100 a wuraren ibadah daban-daban na ƙauyen Kurmin Wali, inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 18 ga watan Janairu.
'Yadda aka kashe matata da yarana shida'
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da lamarin, sannan ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike domin tabbatar da adalci.
Ko katse intanet a Iran zai zama na dindindin?
Gwamnati ba ta sanar da ranar da za a mayar da intanet ɗin ba, amma rahotanni sun yi nuni da cewar akwai yiwuwar hukumoni za su taƙaita amfani da intanet a ƙasar.
Yadda za ku hana masu kisan gilla kutsawa cikin gidajenku
AMB. Capt. Abdullahi Bakoji Adamu (mai ritaya), Mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya ya bayyana wa BBC dabaru bakwai da ya kamata magidanta su ɗauka domin kare iyalansu.
Ƙaruwar masu kashe ƴan uwansu abin fargaba ne - Sheikh Daurawa
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/01/2026
Waɗanne makamai Najeriya ke buƙata don yaƙi da ƴanbindiga?
A lokuta da dama an sha jin wasu jami'an tsaron ƙasar na ƙorafin rashin isassun makamai a matsayin ɗaya daga cikin matsalolin da suke fuskanta.
Kisan gilla biyar na baya-bayan nan da suka tayar da hankali a Kano
A lokuta da dama da suka gabata, an riƙa samun labaran yadda ake yi wa mutanen kisan gilla a jihar, da ke zama cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar.
Yadda za ku kauce wa kamuwa da ciwon zuciya?
Matsalolin kan faru ne sakamakon kitse da ke taruwa a jijiyoyin jini da kuma ƙaruwar wasu abubuwa da ke janyo curewar jini.
'Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga fiye da 40 a Borno'
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Abin da ya sa PDP ta koma neman kuɗi a hannun ƴaƴanta
Jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, ta bayyana dalilin da ya sa za ta fara neman kudi a hannun 'ya'yan jam'iyyar a wani mataki na kawo ƙarshen siyasar ubangida a jam'iyyar.
Yadda Amurka, China da Rasha ke ƙoƙarin mamaye duniya ta ƙarfi
A daidai lokacin da Trump ke ƙoƙarin faɗaɗa ƙarfin ikon Amurka a duniya, a ɗaya ɓangaren kuma China da Rasha na ƙara yunƙurin nuna ƙwanjinsu.
An kama mutumin da ya ƙera 'jirgin Annabi Nuhu' a Ghana
Ƴan sanda sun tuhumi Ebo Noah da wallafa labaran ƙarya da ya haifar da tsoro da fargaba, bayan da ya ce ya na ƙera jirgin ruwa ne domin ceto mutane lokacin da Allah zai halaka duniya a ranar 25 gawatan Disamba ba.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.



































































