Me ya sa wasu marasa addini ke yin azumi a watan Ramadan?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sanaa Al-Khoury
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Lokacin karatu: Minti 5
Galibin mutane na yin azumi ne saboda wajibcinsa ko gwaɓin ladansa a addininsu.
Haka ma wasu na yin azumin a kowace shekara domin kusanci ga ubangijinsu.
Sai dai wasu na yin azumin ne saboda wasu dalilai kamar don jin kunyar mutane, ko tsoron cin abinci a cikin jama'a.
Amma ga mutane da dama, azumi muhimmin abu ne a addinansu, ga Musulmi azumi ibada ce ta sirri da suke yi domin neman kusanci da ubangijinsu.
To amma me ya sa marasa addini, waɗanda ba sa bin koyarwar Musulunci, ke azumtar Ramadan a kowace shekara?
A wasu ƙasashen Larabawa ana kiran waɗannan mutane da ''Masu bautar Ramadan", ma'ana waɗanda ba sa ibada a shekara sai da azumin Ramadan.
Sashen Larabci na BBC ya tuntuɓi wasu mata da maza daga ƙasashen Larabawa daban-daban kan dalilansu na aikata hakan.
Mun ɓoye addinansu saboda wasu dalilai, amma sun amince su yi magana ba tare da bayyana addinan nasu ba.
Ga mafi yawansu, amsar da suka bayar kan dalilansu na yin azumi ya taƙaita ga dalilai biyu: Tunani da addini da kuma iyali da zamantakewa.
Neman albarkar shekara
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Fouad daga Lebanon ya faɗa mana cewa yana azumtar Ramadan ne domin neman albarkar shekara, kamar dai na sabuwar shekara.
''Kamar yadda mafi yawan mutane ke yin azumi a farkowan kowace sabuwar shekara domin neman albarkarta, ina ɗaukar Ramadan a wannan matsayi domin inganta lafiyata da koyon sabbin ɗabi'u'', in ji shi.
''Azumin wata guda zai bani damar koyon sabbin ɗabi'u, kamar haƙuri da juriya'', kamar yadda ya yi bayani.
Fouad ya faɗa cewa bayan "ya bar addininsa," ya koma zama a wajen Lebanon, amma ya ci gaba da azumi.
"Ba domin ibada nake yin azumi ba, amma ina son yanayin Ramadan, da kuma sabon da na yi da shi, kuma a wurin da nake zaune a ƙasar waje ina yin azumi domin tunawa da dangina da ke Lebanon.''
Bayan danginsa da yake tunawa, ya kuma ce azumi kan tuna masa talakawa a wannan lokaci.
"Yana da kyau mu tuna da talakawa a cikin shekarar, amma yanayi na yafiya da kyauta ga marayu a lokacin azumin na matuƙar burgeni''.
Bayan komawarsa Lebanon Fouad ya dakatar da azumi.
''Idan an yi azumi a nan, zai zama kamar munafurci, kamar ina nunawa makusantana cewa ban sauya addini ba. Zan zama kamar ina ɓoye musu gaskiyar aƙidata, ni kuma bana son hakan.''

Asalin hoton, Khaled DESOUKI / AFP
Sabawa da azumi
Ga wasu da dama ba Fouad kawai ba, yin azumi a ƙasashen waje tamkar wani abu ne na al'ada da ɗabi'a.
Basma, ƴar asalin Tunisia, da ke zaune a Turai ta fara shirin Ramadan makonni kafin zuwan watan duk kuwa da cewa ba ta bin tafarkin kowane addini, ba kuma ta yi kowace irin ibada a kowace shekara.
Ta ce ba za ta tsananta wa ƴarta ba kan bin kowane addini da yin nau'in kowace ibada.
"Mahaifiyata mai addini ce, kuma mai yawan ibada, amma bayan na taso na bar gida na bar addini. Bayan mutuwar mahaifina da bulaguron da na yi zuwa Turai, nakan yi azumin Ramadan ne domin tunawa da dangina ."
Basma na son azumi, takan shirya wa watan ta hanyar gyara wurin cin abincinta da sayen sabbin kwanukan cin abinci da jera fulawoyi tare da tuntuɓar dangi domin gaishesu tare da tambayarsu abincin da suka shirya a kowace rana domin buɗe-baki.

Asalin hoton, Yassine Gaidi/Anadolu Agency
Horas da kai da samun nutsawar zuciya
Samun nutsuwar zuciya na daga cikin abubuwan da ke saka Ragheda - daga Lebanon yin azumin Ramadan.
Ta ce "Azumi na taimakawa wajen samar da nutsuwar zuciya da ƙarfin tunani. Yakan taimaka wa mutum ya samun nustuwar tunani a zuciyarsa ta hanyar kore tunanin cin abinci da guje wa zuwa wasu wuraren hayaniya.''
A lokacin ƙuruciya da girmanta, Ragheda mai tsananin bin addini ce, amma daga baya ta yi watsi da duka ayyukan ibadar, amma ta ci gaba da yin azumi saboda ta saka shi matsayin ''wata riba da take samu''
Ta ce: "Alaƙa ta da azumi ta zuciya ce, a ɗaya gefen kuma saboda yadda dangina ke taruwa a lokacin bude-baki. Ƴaƴana ma ba sa yin kowane nau'in ibda amma, amma suna son azumi. A taƙaice ina ɗaukar azumin a matsayin wani abu na al'adarmu da nake matuƙar so.''
Ragheda na ƙarfafa wa ƴaƴanta gwiwa su yi azumi, saboda ''zai taimaka wajen samar da nutsuwar zukatansu tare da koya musu haƙuri da juriya, wanda hakan zai taimaka musu idan suka gamu da wta matsala a rayuwa''.

Asalin hoton, Saqib Majeed/SOPA
'Kyautata alaƙa da juriya'
Shi kuwa Rawi daga Lebanon na yin azumi ne a matsayin koya wa kai juriya.
Baya ɗaukar kansa a matsayin mai bin wani addini, ''in da na rayu a zamanin mu'utazilawa da baa bin da zai hanani shiga aƙidarsu.
Ya ce "Ina ɗaukar azumi a matsayin wata dama gare ni, a amtsayi na ɗan'adam da zan horas da kaina juriya da haƙuri da kuma tunawa da sauran mutane''.
Ita kuwa Iman daga Masar cewa ta yi takan yi azumi ne domin kyautata alakarta da ubangiji, kamar yadda ta bayyana.
Iman ta fara salloli a wasu lokuta a baya, kafin ta fara azuin Ramadan said ai takan yanke sakamakon Rashin lafiya.
Iman na da wata lalura mai tsanani da ke Sanya ta jin kamar ta rasa wani ɓangare na gangar jikinta, don haka yin azumi kan sa ta ji kamar ta samu saukin lalurar.
Duk da cewa ba ta yarda koyarwar Musulunci ba, Iman ta ce tana jin daɗin azumi domin koya wa kanta juriya da haƙuri.











