Na'ukan abinci da ya kamata mai azumi ya riƙa ci

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 2
Watan azumi lokaci ne da mutane suke ƙaurace wa abinci tun kafin ketowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Hakan yana sanya mutane jin yunwa da kuma ƙishirwa.
A lokacin azumi, masu azumi su kan ci abinci nau'o'i daban-daban a lokutan sahur da na buɗe baki.
Mutane sun bambanta yayin da wasu ke shan wahala wajen yin azumi, wasu kuwa ko kaɗan ba sa jigata.
Sai dai, likitoci sun bayyana irin nau'in abincin da ya kamata mai azumi ya ci da kuma wanda zai kaucewa.
Dangane da haka ne muka tuntuɓi ƙwararren likita a fannin cimaka da ke jihar Kano, Auwal Musa Umar don jin irin abincin da ya kamata masu azumi su riƙa ci.
'An fi son mutum ya riƙa cin abinci mai dusa'
Likitan ya ce wani na'uin abincin da ya dace mai azumi ya ci shi ne "Lokacin Sahur ana son mai azumi ya ci abinci mai ɗauke da dusa wato fiber. Mutum ya ƙaucewa abincin da zai yi saurin narƙewa," in ji shi.
Ya ce kada mai azumi ya yawaitan cin taliya ko kunu saboda ci ko shan su zai janyo abinci ya narke da wuri.
Ya ce lamarin zai sa mutum ya fara jin yunwa tun da wuri kamar karfe bakwai ko kuma takwas na safe.
"Da zarar mutum ya samu ingantaccen abinci kamar abinci mai dusa ko shinkafa mai ganye da sauransu yana da muhimmanci. Wannan shi ya dace a yi sahur da shi," in ji Dakta Auwal.
Me ya kamata a ci lokacin buɗe-baki?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abu ne da aka sani cewa lokacin shan ruwa an fi so a yi buɗe baki da dabino kamar yadda addini ya bayyana.
Daga nan kuma sai a bi shi da abubuwa masu ruwa da sikari, kuma wannan ce hanyar da Manzon Allah S.A.W ke shan ruwa da ita.
Dakta Auwal ya ce yana da muhimmanci amfani da ƴaƴan itace lokacin bude baki.
"Babu kyau mutum ya fara shan abu mai sanyi ko mai zafi lokacin shan ruwa, ko kuma wane abu da aka soya ko aka gasa. Abin da ya fi dacewa shi ne amfani da kayan itace irinsu kankana, abarbara, tuffa, gwanda, guava da makamantansu. Su ne suka fi dacewa," in ji likitan.
Ya ce babu laifi mutum ya bi waɗannan abubuwa da shayi ko kuma ruwan sanyi.
Ya ƙara da cewa wajibi ne al'umma su rage ci ko shan lemukan kwalba ko na roba ko na gwangwani da sauransu.
"Ya kamata al'umma sun ƙaurace wa ci ko shan abubuwan da aka sarrafa.
"Bincike ya nuna cewa ana ƙara musu wasu sinadarai waɗanda ba su da muhimanci ga jiki, musamman idan aka dauki tsawon lokaci ba a ci wani abu ba," in ji Dakta Auwal.
Ya kuma ce mutane su takaita zirga-zirga a cikin zafin rana domin su kare kansu daga jigata.











