Amurka ta buƙaci jami'anta su bar Abuja: Me hakan ke nufi?

Asalin hoton, Getty/X
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 6
Gwamnatin Amurka ta buƙaci jami'anta da ke aiki a Najeriya su yi gaggawar barin ƙasar, saboda dalilai na tsaro. Amurkar ta ce duk waɗanda ayyukansu ba su zama wajibi ba, da ke a ofishin jakadancinta a birnin tarayya Abuja, su tattara kayansu da iyalai domin barin ƙasar.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Amurkar ta ce wannan umarnin ya fara aiki ne daga ranar Talata, 8 ga watan Afrilun 2026.
Bayanin ya ce "an samu ƙaruwar aikata miyagun laifuka, ta'addanci da garkuwa da mutane da sauran tashe-tashen hankula a Najeriya".
Amurkar ta kuma lissafa wasu jihohin Najeriyar 23 daga kudu da arewacin ƙasar, inda ta ce suna da haɗari, kuma ta gargaɗi ƴan ƙasarta su guji tafiya zuwa waɗannan jihohin da ta ɗora su a mataki na huɗu na gargaɗi.
Amurka ta ce masu kai hare-hare a ƙasar suna farmakar makarantu, kasuwanni, asibitoci da wasu wuraren shaƙatawar da ta san cewa ƴan ƙasar na zuwa.
"Ko ta halin ƙaƙa, kada ku yi tafiya zuwa waɗannan jihohin," in ji sanarwar shawarar da ta fitar.
"Idan tafiya ta zama wajibi, a tafi da na'uororin bin diddiga da yadda za a iya tuntuɓar ofishin jakadanci cikin sauki".
Najeriya dai ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, inda ƴanbindiga a sassan ƙasar da dama ke kai hare-hare da kashe mutane tare da kama wasu domin neman kuɗin fansa.
Ƙungiyoyin ƴanbindiga irin su Boko Haram da ISWAP da ƴan fashin daji ne ke yawaita kai hare-hare.
Jihohin da Amurka ta yi gargaɗi a kan su

Asalin hoton, FB/Multiple
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jihohin da Amurkar ta yi gargaɗin cewa kada ƴan ƙasarta su je saboda ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane a arewacin Najeriya sun haɗa da Borno, Jigawa, Kogi, Kwara, Niger, Filato, Taraba, Yobe, da kuma arewacin Adamawa.
A jihohi irin su Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, da Zamfara kuwa, Amurkar ta ce an samu ƙaruwar aikata laifuka da garkuwa da mutane.
A kudancin Najeriya kuwa, Amurka ta lissafo jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo, da kuma Rivers (amma ban da birnin Fatakwal) a matsayin jihohin da ake yawan samun tashe-tashen hankula da aikata manyan laifuka.
Sanarwar ta ce wuraren da ta lissafa ana yawan aikata munanan laifuka, da suka haɗa da fashi da makami, satar motoci, da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, kuma ana ganin ƴan ƙasar Amurka a matsayin masu arziƙi shi ya sa ake yawan kai musu hari.
Ta ƙara da cewa daga cikin dalilan da ta ke ganin ya zama wajibi ƴan ƙasar su bar Najeriya, har da yanayin da asibitocin ƙasar ke ciki, waɗanda ba irin na ƙasashen turai ko Amurka ba ne.
Me wannan matakin ke nufi?

Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a yankin Sahel, wanda ke zaune a Birtaniya, ya ce kamar Najeriya, ita ma Amurka takan fitar da irin wannan sanarwar gargaɗi idan ta ga alamar barazana ga ƴan ƙasar ta.
Ya ce babu wani sabon abu game da matakin da Amurkar ta ɗauka, amma wataƙila akwai wasu bayanan sirri da ta tattara da ke nuna yiwuwar kai wa ƴan ƙasarta hari waɗanda ba ta bayyana ba.
Masanin ya ƙara da cewa, rikicin Gabas ta Tsakiya ma zai iya tasiri, musamman yadda wasu ƴan ƙasashe ke nuna ƙiyayya game da rawar Amurkar ta taka, da barazanar kai musu hari saboda goyon bayan Iran.
"Waɗannan abubuwa da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, na ƙara ruruta tsanar ma'aikatan gwamnatin Amurka da wasu ƴan ƙasar a Najeriya, kamar yadda haka ke faruwa a wasu sassan duniya,"in ji shi.
Sai dai Barista Bukarti ya nuna takaicinsa kan yadda Amurka ke fitar da irin waɗannan sanarwa lokaci bayan lokaci, ba tare da ta fayyace abin da ta gano na barazana domin taimaka wa hukumomin Najeriyar ba.
Ya ce: "A baya Amurka ta sha fitar da irin wannan sanarwa, amma kuma babu abin da ya faru".
Ko hakan zai shafi alaƙar diflomasiyya?
Bulama Bukarti ya ce ba lallai matakin ya shafi alaƙar ƙasashen biyu ba, saboda abu ne da kowace ƙasa za ta yi idan ƴan ƙasarta na cikin haɗari.
"Wannan sanarwa ba tana nufin yanke hulɗar diflomasiyya ba ne, ko kuma alaƙar diflomasiyya, kuma ba tana nufin tsamin alaƙa ne tsakanin Amurka da Najeriya ba," in ji shi.
Duk da yake ya ce gwamnatin Amurkar ta sha yin irin wannan gargaɗi kuma daga baya babu abin da ya faru, ba shi ke nufin hukumomin Najeriya su naɗe hannayensu ba tare da ɗaukar mataki ba.
"Wannan ba yana nufin kada mu dauki mataki ba..., amma kada mutane su tayar da hankalinsu, su ɗauka kamar duniya ce za ta tashi saboda Amurka ta yi wannan magana".
An kashe mutum 2,360 a Najeriya a wata ukun farkon 2026 - Rahoto
Wani rahoto da Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited mai nazarin matsalolin tsaro a yankin Sahel ya fitar ya ce an ƙara samun taɓarɓarewar al'amuran tsaro a Najeriya cikin watanni uku farkon 2026.
Cikin rahoton wata-wata da kamfanin ke fitarwa ya ce duk da matakan da jami'an tsaron ƙasar ke ɗauka har yanzu matsalar ba ta sauya ba.
Rahoton na Beacon Security ya ce mutum 2,360 aka kashe a Najeriya cikin watanni ukun farkon shekarar 2026 da muke ciki.
Jihohin da aka fi samun kashe-kashe a Najeriya
Rahoton ya nuna cewa yankin arewa maso gabashin Najeriya ne kan gaba a samun kashe -kashen cikin wata ukun farkon wannan shekara. Beacon Security ya ce mutum 801 aka kashe a yankin cikin watannin uku.
A cikin wannan shekara kaɗai an samu manyan hare-haren da waɗannan ƙungiyoyi suka ƙaddamar kan sojoji da fararen hula, ciki har da wanda suka kai garin Ngoshe a cikin watan Maris.
Yankin da ya biyo baya a samun kashe-kashen shi ne Arewa ta Tsakiyar ƙasar mai fama da rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya, inda rahoton ya ce an kashe mutum 762.
Yankin arewa maso yammcin ƙasar - mai fama da matsalar hare-haren ƴan fashin daje masu garkuwa da mutane - ne ya zo na uku a samun kashe-kashen, wanda aka kashe mutum 508,
Sai kuma kudu maso gabashi, inda aka kashe mutum 157, da kudu maso kudu mai mutum 64, sai kuma kudu maso gabas da aka kashe mutum 58 cikin watanni ukun farkon 2026.
Rahoton ya kuma fayyace jerin jihohin da ke kan gaba a inda aka samu kashe mutanen a farkon wannan shekarar.
Beacon Security ya ce jihohin da aka fi samun kashe-kashe sun haɗa da:
- Borno da aka kashe mutum 546
- Filato mai mutum 203
- Kwara mai mutum 198
- Benue mutum 174
- Katsina mutum 125
- Kebbi mutum 122
Jihohin da aka fi sace mutane a Najeriya
A cewar rahoton, jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammcin ƙasar ce kan gaba a sace mutane a watanni ukun farkon wannan shekara.
Beacon Security ya ce a jihar Kaduna kaɗai an sace mutum 296, sai jihohin:
- Zamfara da aka sace mutum 191
- Borno mai mutum 125
- Katsina mutum 95
- Kwara mutum 93












