Ko farashin man fetur zai sauka a Najeriya bayan tsagaita wuta a yaƙin Iran?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 5
A yanzu dai da alama hankula za su kwanta bayan da Amurka da Iran suka sanar da tsagaita wuta na tsawon mako biyu, bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar kai wani gagarumin hari kan Iran, jim kaɗan kafin cikar wa'adin da ya bayar.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa za su buɗe mashigar Hormuz domin jiragen ruwa su riƙa wucewa a lokacin tsagaita wutar, amma da rakiya daga sojojin Iran.
Rahotanni sun nuna cewa an cimma yarjejeniyar ne mintuna goma kafin cikar wa'adin da Trump ya bayar na kai hare-hare.
An sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar ce da misalin ƙarfe 6:32 na yamma agogon Washington, wanda ya yi daidai da ƙarfe 11:30 na dare a agogon Najeriya.
Firaministan Pakistan ya sanar da fara aiki da yarjejeniyar nan take, inda yayi maraba da matakin tare da gayyatar dukkan ɓangarorin da su hallara a wani babban taro a Islamabad ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu, domin ci gaba da tattaunawa da nufin samun fahimtar juna.
Yaushe za a samu sauƙin man fetur a Najeriya?
Masu sharhi a Najeriya sun fara tsokaci kan tsagaita wuta a yaƙin Iran da Amurka, inda ake hasashen samun sauƙin farashin man fetur ɗin a ƙasar.
A hirarsa da BBC, Farfesa Ahmed Adamu na jami'ar Philomath da ke Abuja, masani kan harkokin man fetur ya ce matakin tsagaita wutar zai yi tasiri saboda farashin man fetur a Najeriya yana daidaituwa ne da na kasuwar duniya.
Ya ce saukar da gangar ɗanyen mai ya yi zuwa ƙasa da dala 100, zai sa a ga canji saboda buɗe mashigar Hormuz.
"Ɗanyen man fetur da ya taru ya daɗe a cikin wananan tekun, yanzu zai shigo cikin kasuwa, zai yi yawa, kuma farashinsa zai yi ƙasa," in ji shi.
Farfesan ya ƙara da cewa wataƙila ma farashin man fetur ya yi ƙasa da yadda yake kafin a fara yaƙin.
"Dama ita kasuwar ɗanyen man fetur ta gaji hawa da sauka".
'Sai nan da wata ɗaya za a ga canji'
Masanin ya ce ba lallai a fara ganin sauyin da ake tsammani nan take ba, domin an tsagaita yaƙin na tsawon makonni biyu kawai.
Farfesa Ahmed ya ce wasu ƴan kasuwar za su iya kafa hujja da cewa sun saro man da tsada a lokacin da ake yaƙin, kafin su yarda su saukar da farashin.
"Za mu iya cewa nan da wata ɗaya, idan har dakatar da yaƙin ya ɗore..., farashin zai iya komawa yadda yake a da ko ƙasa da haka," in ji shi.
Farfesan ya ce ya kamata Najeriya ta yi nazarin abin da ya faru sakamakon yaƙin, domin ɗaukar matakan da a nan gaba ƴanƙasar ba za su sha waahala irin ta yanzu ba.
"A ɗauki matakin da za a ba ƴan Najeriya zaɓi a lokacin da tataccen man fetur ya yi tsada, suna da zaɓin in sun ga dama su ƙi siyanshi, kuma su yi amfani da wasu damarmaki na sufuri, ta yadda ba sai sun saye man fetur ba," a cewar Farfesa Ahmed.
Yadda yaƙin Iran ya shafi farashin man fetur a Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farashin man fetur dai ya ƙaru sosai a Najeriya tun bayan da aka fara yaƙin Iran, inda yawanci aka dogara da matatar man Dangote ko kuma shiga da shi ƙasar daga ƙasashen waje.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, a baya ya yi gargadi kan rikicin na Gabas ta Tsakiya inda ya ce lamarin na iya tilasta wa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka sake ɗaukar matakan komawa yin aiki daga gida kamar na lokacin COVID-19 idan ba a samu sassaucin rikicin ba.
Dangote ya yi wannan gargaɗin ne a watan Maris bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Ikoyi a Legas.
Ya ce: "Idan wannan abin bai lafa ba, ku sani, yawancinmu a Afirka ba mu da wani babban tanadi. "Za mu yi kamar lokacin COVID, inda mutane za su riƙa aiki daga gida."
A farkon watan Maris, matatar ta kara farashin man fetur da Naira 101, daga Naira 774 zuwa Naira 875 kan kowace lita.
Matatar ta ce hakan ya faru ne biyo bayan rashin tabbas da aka samu a farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya. An samu tashin farashin ɗanyen mai a duniya, wanda ya haura $80 kan kowace ganga a cikin dare ɗaya.
Wannan karin ya jefa 'yan Najeriya da dama cikin matsin tattalin arziki, musamman a bangaren sufuri da farashin kayayyaki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da matakin
Mai magana da yawun shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya ce ya yi maraba da sanarwar tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka da Iran.
Ya bayyana cewa, Guterres yana kira ga dukkan ɓangarorin da ke da hannu a rikicin Gabas ta Tsakiya da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa tare da bin sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar, domin buɗe hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa da cikakken kwanciyar hankali a yankin.
Haka kuma, ya nuna godiya ga ƙoƙarin da ƙasar Pakistan da sauran ƙasashe suka yi wajen taimakawa wajen cimma wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta.
Ƙasashen duniya na mayar da martani
Ƙasashen duniya sun yaba da yarjejeniyar da aka cimma ta tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila, lamarin da zai bayar da damar buɗe mashigar Hormuz mai matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin duniya.
Saudiyya ta ce tana sa ran yarjejeniyar za ta yi sanadiyyar samar da cikakken zaman lafiya mai ɗorewa.
Babbar jami'ar diflomasiyya ta Tarayyar Turai Kaja Kalas ta bayyana lamarin a matsayin ƙoƙarin daƙile faɗawa karaya da zai bayar da damar warware rikicin ta hanyar tattaunawa.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce yana fatan za a yi cikakkiyar biyayya ga yarjejeniyar.
Firaiministan Birtaniya Keir Starmer zai kama hanya zuwa yankin Gulf domin yin tattaunawa ta diflomasiyya kan yadda za a tabbatar da tsagaita wutar.
Amurka da Iran na iƙirarin samun nasara
Amurka da Iran na iƙirarin samun nasara a yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon mako biyu da suka cimma a tsakaninsu.
An sanar da yarjejeniyar ne kafin cikar wa'adin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa Iran na ta buɗe mashigar Hormuz, ko kuma ta fuskanci mummunan hari da zai iya lalata ƙasar baki ɗaya.
Iran ta ce za ta ba da damar wucewar jiragen ruwa cikin aminci ta mashigar na tsawon mako biyu, amma ƙarƙashin kulawar sojojinta.
Isra'ila ta ce tana goyon bayan matakin da Amurka ta ɗauka na dakatar da hare-hare kan Iran.
A cikin sabon saƙonsa a shafukan sada zumunta, Trump ya bayyana ranar a matsayin babbar rana ga zaman lafiya a duniya, yana mai cewa yarjejeniyar na iya kai wa ga wani sabon zamani mai armashi a Gabas ta Tsakiya.
Sai dai har yanzu akwai manyan ƙalubale da ke gaban samun dawwamammen zaman lafiya, inda daga cikin buƙatun Iran akwai biyan diyya da kuma ɗage takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba mata.












