KAI TSAYE, Yaƙin Iran da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 09/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf

  1. Iran da Saudiyya sun tattauna ta waya a karon farko tun bayan fara yaƙi

    Ministan harkokin Wajen Saudiyya, Prince Faisal bin Farhan Al Saud, ya tattaunawa ta waya da takwaransa na Iran, Abbas Araqchi, a karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙi da hare‑haren Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Wannan shi ne mataki na farko na hulɗa kai tsaye tsakanin ƙasashe biyu a cikin wannan rikici.

    Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana a shafin ta na X cewa ministocin biyu sun tattauna kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin, tare da bincikar hanyoyin rage tashin hankali don dawo da tsaro da kwanciyar hankali a yankin

  2. An sake buɗe masallacin Al-Aqsa da saura wuraren bauta a Birnin Kudus

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    ‘Yan sandan Isra’ila sun sanar cewa za a sake buɗe wuraren ibada a Birnin Kudus ga masu ziyara da masu ibada bayan cimma tsagaita wuta na wucin gadi a rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Waɗannan wurare sun haɗa da Masallacin Al-Aqsa da Western Wall, da Cocin Holy Sepulchre a Tsohuwar Birni, wadanda suke daga cikin wuraren ibada mafi muhimmanci ga Musulmai da Yahudawa da Kiristoci.

    Sakamakon yaƙin da Iran ke yi da Amurka da Isra’ilan ne aka rufe wadannan wurare.

    Birnin Kudus ta kasance wurin da kullum cike take da mazauna, masu sayayya a kasuwa da masu yawon bude ido, da masu ibada.

    ‘Yan sanda sun ce za a buɗe wuraren ne a safiyar Alhamis, kuma za a tura ƙarin ‘yan tsaro da dama don tabbatar da tsaro.

  3. Farashin mai ya sake tashi saboda rashin tabbas a tsagaita wutar Amurka da Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin mai ya sake tashin gwauron zabo a kasuwannin Asiya da safiyar yau Alhamis saboda rashin tabbas a yarjejeniyar tsagaita Wutar Amurka da Iran, bayan ya faɗi saboda tsagaita wuta na makonni biyu.

    Farashin mai nau'in Brent ya tashi da kashi 2.2 cikin 100 zuwa dala $96.70 kan kowanne ganga, yayin da farashin ɗanyen man Amurka na West Texas ya tashi da kashi 2.8 cikin 100 zuwa dala $96.90.

    Bayan ci gaba da harin Isra’ila a Lebanon, an fara samun rashin tabbas a yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka.

    Farashin mai nau'in brent dai ya faɗi da kashi 15 cikin 100 zuwa ƙasa da dala $92 kan kowanne ganga a farkon ranar Laraba bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta, amma a ranar kuma ya sake tashi

    Farashin mai har yanzu ya fi na kafin barkewar yaki a ranar 28 ga Fabrairu tsada.

  4. Spain ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Álvarez, ya sanar da cewa ƙasar za ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Tehran, wanda aka rufe a watan Maris saboda yaƙi, bayan cimma matsaya ta tsagaita wuta tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran.

    "Na umarci jakadanmu a Tehran da ya koma Iran," in ji ministan a lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Madrid.

    Mista Álvarez ya ƙara da cewa da komawar ƙasar za ta ba da gudummawa ga ƙoƙarin zaman lafiya ta duk hanyoyin da suka dace

  5. Ana gangamin cika kwana 40 da kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Iraniyawa da dama suna gudanar da gangami a birane daban-daban na ƙasar don tunawa da cika kwana 40 da kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei kamar yadda gidan talabijin na gwamnatin ƙasar ya ruwaito.

    A cikin hotunan, za a ga ɗimbin magoya bayan gwamnati na nuna alhini a titunan biranen Hamedan da Yazd da Khorramabad da Shiraz da Yasuj da dai sauransu.

    An kashe Ali Khamenei ne a ranar farko ta yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran a ranar 29 ga Maris kuma har yanzu ba a yi jana'izarsa ba a hukumance.

  6. Amurka ta umarci jami'anta su fice daga Najeriya

    Shugaban Amurka Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta umarci jami'anta na diflomasiyya su fice daga Abuja, babban birnin Najeriya, yayin da tsaro ke ''ƙara taɓarɓarewa'' a ƙasar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce ta umarci ma'aikatan gwamnatin Amurka a ofishin waɗanda aikinsu bai zama wajibi ba, da kuma iyalansu su bar ƙasar.

    Haka kuma gwamnatin Amurkar ta shawarci ƴan ƙasarta da ke so ko kuma suke shirin zuwa Najeriya da su sake shawara, saboda matsalar tsaro - wadda ta haɗa da satar mutane da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga.

    A jiya Laraba ne hukumomin Najeriyar suka fara shari'ar sama da mutum 500 da ake zargin su da hannu a hare-haren ƴan bindiga, da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a musamman a arewacin ƙasar.

  7. Yarjejeniyar tsagaita wuta ta haɗa da Lebanon - Ƙasashen Turai

    Ƙasashen Turai sun ce wajibi ne Lebanon ta kasance cikin yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Iran.

    Ministan harkokin waje na Birtaniya Yvette Cooper ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai kan Hezbollah a Lebanon a matsayin mummunan ɓarna - sannan ya ce ƙin amincewa da Lebanon a cikin yarjejeniyar zai iya dagula lamurra da kuma rikita yankin.

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce harin da aka kai ƙasar ya kashe sama da mutum 180 a ranar Laraba.

    Masu ceto na ci gaba da neman wadanda ke da sauran numfashi a ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe.

    Isra'ila ta ce an yi wa Hezbollah mummunar illa.

  8. Amurka ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta - Iran

    Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, Tasnim

    Bayanan hoto, Jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei

    Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan Isra'ila ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a ƙasar Lebanon.

    Shugaban majalisar dokokin Iran Mohammed Bagher Ghalibar ya ce an karya tanade-tanaden sassa daban-daban na sharuddan yarjejeniyar da Iran ta gabatar.

    A matsayin martani, mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya nanata cewa babu Lebanon a cikin yarjejeniyar da aka cimma.

    Ya kuma ce bai kamata Iran ta bari yarjejeniyar ta lalace ba a sanadiyyar Lebanon.

  9. Sojojin Amurka za su ci gaba da kasancewa a kusa da Iran - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sojojin ƙasarsa za su ci gaba da zama a kusa da Iran, yayin da ake nuna fargaba kan yuwuwar durkushewar yarjejeniyar zaman lafiya.

    Shugaban ya ce dakarun za su zauna a yankin har zuwa lokacin abin da ya kira bin yarjejeniyar sau da kafa.

    Ya ce muddin ba a yi haka ba to kuwa hakan ka iya sa Amurka ta koma kai hari - wanda a kalamansa ya bayyana da cewa - zai fi na baya girma da kuma illa.

    Iran ta ce, ci gaba da kai harin da Isra'ila ke yi a kan Hezbollah a Lebano saba wa yarjejeniyar ne, bayan sojin Isra'ila sun kashe ko raunata sama da mutum dubu daya a jiya Laraba.

    Wannan wani mawuyacin hali ne ga Iran, wadda ba za ta yi watsi da Hezbollah ba wadda ta shiga yakn domin mara mata baya Iran din ta ce za ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz.

    Amma kuma jami'an Amurka sun ce batun Lebanon ba ya cikin yarjejeniyar.

  10. Barka da warhaka!

    Ofishin BBC da ke Abuja, Najeriya

    Barka da zuwa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, inda muke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026.

    Za ku iya yin sharhi kan labaran da muke sakawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram da kuma YouTube.

    Sannan ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗumi.