Shin rashin yin sahur na da illa ga lafiyar jiki?

Asalin hoton, Getty Images
Sahur dai wani lokaci ne da ake cin abinci a ƙarshen dare musamman ga wanda ya yi niyyar yin azumi, lokacin shi ne gabanin fitowar alfijir.
Sahur abu ne da addinin Musulunci ya ba da umarnin a yi, sai dai umarnin ba ya nufin wajibci,
Umarnin an yi shi ne ta fuskar 'mustahabbi' wato an so duk wanda zai yi azumi ya yi hakan, amma rashin yin sa bai zama laifi ba.
Sai dai, galibi akwai wasu mutane da ba su cika yin sahur ba lokacin azumi saboda wasu dalilai nasu.
Amma ta yaya rashin sahur zai shafi lafiyar mai azumi?
Mun miƙa wannan tambaya ga dakta Hassan Ibrahim na asibitin Biba da ke jihar Kaduna.
Likitan ya ce rashin sahur gaba-ɗaya zai iya shafar lafiyar mutum saboda akwai ma'aunin abin da jiki yake da shi idan an ci abinci, to idan ba a ci komai ba lokacin narkewar abincin zai wuce.
"Abincin sahur na aiki ne daga sa'a huɗu na farko, daga nan sai ya fara amfani da abin da jiki ya ajiye. Sahur ɗin ka yi shi zai yi maka aiki a sa'a huɗun farko, idan kuma ba ka yi ba, jiki zai fara amfani da abin da aka ajiye tun da farko shi yake sa mutum ya galabaita lokacin azumi," in ji Dakta Biba.
Ya ce idan aka yi sahur lokacin azumi hakan na ƙara wa mutum ni'ima saboda ba a ƙure lokacin da abin da ke jikinka zai fara ɓarna ba.
"Rashin yin sahur kuma zai sa wasu su riƙa ramewa. Amma idan kana yin sahur daidai gwargwado zai sa ka tafi da lafiyarka.
"Rashin sahur ƙwata-ƙwata zai iya iya kawo rauni a jikin mutum," in ji likitan.
Shan ruwa kaɗai ya wadatar?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Hassan Biba ya ce za a so haɗa ruwa da wani abu lokacin azumi, dauk da cewa ruwan yana da alfanu sosai.
"Amma so samu a ci wani abu bayan ruwa saboda hakan yana da amfani sosai. Ba wai sai an ci abinci an ƙoshi sosai ba saboda zai zube cikin lokaci kaɗan ya kuma wahalar da mai azumi," in ji Dr Hassan.
Ya ƙara da cewa abin da ya kamata mai sahur ya ci shi ne abinci mai nau'in sinadarin protein.
Wato dangin abinci da suka ƙunshi alkama, kosai, wake ko kuma kunu.
"In ka ci waɗannan na'ukan abinci suna narƙewa ne a hankali. ya fi juriya kuma zai daɗe yana amfani a jiki lokacin azumi maimakon a ci tuwo saboda lokaci ɗaya yake narƙewa," in ji likitan.
Ya ƙara da cewa masu azumi su guji shan abu mai zaki lokacin sahur.
'Yin sahur yana da alfanun gaske'
Likitan na asibitin Hassan Biba da ke jihar Kaduna ya ce mutane su riƙa kula wajen ganin sun yi sahur lokacin azumi.
"Ba burgewa bace mutum ya ki yin sahur saboda ko a shari'ance akwai falalar yin sahur. Azumi yana da muhimmanci wajen gyara lafiya ta fannoni daban-daban.
"Yin sahur da buɗe-baki kowanne yana da amfani. Jikin mutum ba zai lalace ba.
"Amma idan mutum baya yin sahur duk da cewa jiki zai saba da shi, amma illarsa shi ne zai riƙa rare duk wani abu na lafiya a jikin mutum wanda zai sa a shiga yanayi idan ana azumi.
"Amma sahur zai yi wa mutum shimfiɗa wajen tsarkake jiki da yin ibada cikin sauki da ƙara lafiya. Muna so a yi koyi irin wannan," in ji Dakta Hassan Biba.
Ya ce shan abu mai zaƙi zai saka mutum ya riƙa jin ƙishirwa.











