Hukuncin azumin yaran da suka balaga da wuri

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Duk da cewa azumin Ramadana bai zama wajibi a kan ƙananan yara ba, akan kwaɗaitar tare da fara koya musu yin azumin tun kafin su balaga.

Azumi na ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci biyar, abin da ke nufin wajibi ne a kan kowane Musulmi baligi mai ƙoshin lafiya.

Azumin na bana zai kama ne daga ƙarshen watan Fabrairu zuwa ƙarshen watan Maris, kuma ana sa ran za a yi shi cikin yanayin zafi.

Azumi na daga cikin abubuwan da yara ke ɗokin yinsu tare da Sallar Idi. Sai dai wasu iyayen kan hana su cika azumin kamar na manya duk da cewa sun kai munzalin balaga.

Ko me addinin Musulunci ya ce game da azumin irin rukuni na yara? Kuma ta yaya ya kamata su dinga yin azumin?

Matakan balaga a Shari'ar Musulunci

Wata yarinya tana shuka itaciya

Asalin hoton, Getty Images

Akasari wannan yanayi ya fi shafar yara mata, waɗanda kan fara jinin al'ada da ƙananan shekaru.

Idris Mainasara Gandun Albasa malamin addinin Musulunci ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, kuma ya yi bayanin cewa akwai matakai da ake bi wajen gane ko yaro ya ya balaga.

"A mazahabar malikiyya, yarinya mace tana balaga ne daga lokacin da ta kai shekara. Hakan na nufin sallah da azumi sun wajaba a kanta. Amma idan ta fara jinin al'ada kafin shekara taran, to sallah da azumi sun wajaba a kan ta," in ji shi.

"Na biyu, akan gane mace ta balaga idan ta ɗauki ciki ko da ba ta fara jinin al'ada ba. Idan haka ta faru ana yi mata hukunci da ta kai munzalin balaga ko da ba ta fara jinin ba."

Na uku kuma, akwai abin da ake kira "attamyeez", a cewar malamin, wanda ke nufin kaiwa shekarun hankali a bayyane.

"Ana nufin idan alamun girma suka bayyana a jikinta, kuma aka lura tana da hankali to ana ɗaukar ta balaga. Shi ma namiji irin wannan hukuncin ya faɗa kan sa matuƙar alamun girma sun fito masa, kamar gemu ko gashin baki."

Mene ne hukunci?

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Domin jin hukuncin da shari'a ta tanada game da wannan batu, mun tuntuɓi Malam Abubakar Abdullahi Goron Namaye daga jihar Kaduna.

Malam ya ce Musulunci bai damu da girman jikin yara ba wajen tantance balagarsu.

"Matuƙar mace ta fara al'ada to komai na wajabci ya hau kanta," kamar yadda malamin ya yi bayani.

"Idan ka duba ko auren Nana Aisha da Annabi, ba ta wuce shekara tara ba. Sannan akwai hadisin da ke cewa ku umarci 'ya'yanku da yin sallah tun suna shekara bakwai, kuma ku doke su a kan yin sallar idan suka kai shekara 10.

"A taƙaice dai, indai balagar ta bayyana to azumi ya wajaba a kansa matuƙar dai lafiyarsa ƙalau ba tare da wata larura ba, ko da kuwa girman jikin yaro bai kai ba."

Sai dai Malam Idris Mainasara ya ce akan bai wa iyaye shawarar su dinga ƙoƙari wajen koya wa yaran azumi tun kafin balagar ta same su.

"Abin da malamai suka shi ne, iyaye su dinga kwaɗaitar da yara wajen yin azumin, ba wai lokaci guda ba a ce su fara yin azumi," a cewarsa.

"Sannan wani lokacin yana da kyau a nemi shawarar likitoci domin duba yanayin yaro. Sannan kuma a nemi fatawar malamai kan kowacce wata matsala domin duba ta ita kaɗai da zimmar neman mafita."

Dabarun koya wa yaro azumi

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen koya wa yara yin azumi, ko da kuwa bai kai cikakken azumi ba.

Ɗaya daga ciki ita ce ɗaukar azumin daga farkon rana zuwa tsakiyar wuni, kodayake wasu yaran kan nemi a ƙyale su su kai har ƙarshe. Amma ana shawartar iyaye da su bi abin a hankali saboda kada yaro ya galabaita sosai.

Kazalika, idan yaro ɗan tasa ta yadda zai iya ɗaukar azumin daga farko zuwa ƙarshen wuni, akan saka su su dinga yin tsallaken kwana ɗaya-ɗaya, ko biyu-biyu.

A gefe guda kuma, wasu iyayen kan bari yaran su yi na wani tsawon lokaci amma kuma sai su huta a 10 ta ƙarshe.

"Tun da dama azumin bai wajabta a kansu ba, akan bai wa ladan ibadar yaran ga iyayensu ne," in ji Malam Abubakar Goron Namaye.