Mece ce illar shan zuma ga jarirai da ƙananan yara?

.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A watan Disambar da ya gabata, an kai wani yaro ɗan shekara huɗu mai suna Nitin Balasekar daga gundumar Sivaganga asibiti bayan ba shi zuma domin maganin ciwon ciki.

Bayan shan zumar, sai yaron ya suma, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibitin gwamnati na Sivaganga, inda ake ci gaba da kula da lafiyarsa.

Shugaban Kwalejin Kiwon Lafiya ta Gwamnati da ke Sivaganga, Srinivasan, ya shaida wa manema labarai cewa abin da ya jawo matsalar shi ne sinadarin da ake kira botulinum wadda ake iya samu a cikin zuma.

A cewarsa, "wannan sinadarin na iya shafar ƙwaƙwalwa da jijiyoyin jiki, ta kuma kawo matsala ga numfashi da zagayawar jini."

Ya ƙara da cewa an saka yaron a kan na'urar taimaka wa numfashi tare da ba shi maganin riga-kafi na musamman da ake kira immunoglobulin.

Wannan lamarin ne ya dasa ayar tambaya ko za a iya bai wa yara musamman jarirai zuma?

Bincike daban-daban ya nuna cewa bai wa jarirai zuma nan da nan bayan haihuwa ko kafin a fara ba su nono al'ada ce da ta yaɗu a wasu ƙasashen Kudancin Asiya, ciki har da Indiya.

Haka kuma, binciken da aka wallafa a shafin intanet ta Babban ɗakin karatun kiwon Lafiya na Amurka ya nuna cewa bai wa yara ƙanana zuma ya zama ruwan dare a wasu ƙasashen yankin Gulf kamar Saudi Arabia.

Haka kuma, a wani bincike ta intanet da aka gudanar a shekarar 2022 tsakanin iyaye mata mazauna Saudiyya, kashi 52 cikin ɗari sun ce suna da ɗabi'ar bai wa yaransu zuma.

Binciken ya yi gargaɗin cewa wannan na iya jawo matsaloli tun daga ciwon hanji har zuwa matsalar numfashi.

Kodayake tashin zuciya da amai da rashin cin abinci su ne manyan alamomin cutar, binciken ya kuma bayyana wasu ƙarin alamomi, kamar haka:

  • Matsewar tsokokin fuska
  • Rashin yin ba haya
  • Tsukewa ko jan tsokokin baki
  • Ciwo a ƙwaƙwalwa
  • Jijjiga (Seizures)
  • Saukar yanayin zafin jiki
.

Asalin hoton, Getty Images

Za a iya bai wa jarirai ɗaya zuma?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Amurka ta bayyana cewa bai wa yara da ba su kai shekara ɗaya ba zuma na iya haddasa wata mummunar cuta da ake kira botulism.

Hukumar ta ce bai kamata a ba jarirai zuma kai tsaye ba, ko ma a gauraya ta da abinci ko ruwa da ake ba su ba.

Wata likitar yara mai suna Vidya ta ce bai kamata a bai wa jarirai komai ba face nonon uwa har sai sun kai watanni shida.

Ta bayyana cewa jarirai ƙanana na da ƙarancin garkuwar jiki, sannan hanjinsu da tsarin narkar da abinci ba su gama ƙarfi ba.

Ta ce ana fayyace wannan lamari a asibitoci, kuma ana kula da tsarin ciyar da yara bisa ƙa'idojin lafiya.

Hukumar kiwon lafiya ta ƙasar Birtaniya ta kuma yi gargaɗi cewa ƙwayar cuta daga ƙwayar Clostridium botulinum da ake iya samu a cikin zuma na iya samar da guba a cikin hanjin jariri.

Wannan na iya jawo wata cuta mai tsanani da ake kira infant botulism, wadda ke iya zama barazana ga rayuwar jariri.

Binciken da aka wallafa a shafin Babban ɗakin karatun kiwon Lafiya na Amurka ya nuna cewa cutar infant botulism cuta ce mai haɗarin gaske, kuma na iya haddasa matsaloli masu tsanani ga jijiyoyin jiki da ƙwaƙwalwa.

Dokta Vidya ta ce gano wannan cuta da wuri ba abu ne mai sauƙi ba.

Ta ƙara da cewa dole ne a fara magani cikin gaggawa, domin cutar na shafar hanjin jariri.

Alamomin farko da ke nuna wannan cutar sun haɗa da

  • Jariri ya ƙi shan nono
  • Kasala
  • Kumburin ciki.

Ta kuma jaddada cewa yana ɗaukar kusan watanni 12 kafin hanji da tsarin narkar da abinci na jariri su gama bunƙasa yadda ya kamata.

Wannan ne ya sa Hukumar lafiya ta duniya ke ba da shawarar kada a ba yara da ba su kai shekara ɗaya ba zuma.