Su wane ne shugabannin da ke gudanar da mulkin Iran?

.

Asalin hoton, Rouzbeh Fouladi / Middle East Images / AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei (tsakiya), Shugaban Iran Masoud Pezeshkian (hagu), shugaba majalisar Mohammad Baqer Qalibaf (hagu), babban alƙalin ƙasar Justice Mohsen Ejei (dama), da wakilin Hezbollah a Iran Abdullah Safieddine suna karatun Alƙur'ani a ranar Juma'a a Tehran
Lokacin karatu: Minti 5

Jagoran addini

Kiongozi wa kidini wa Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Asalin hoton, Iranian Leader Press Office/Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Iran's religious leader, Ayatollah Ali Khamenei.

Mutumin da ya fi kowa iko a Iran shi ne jagoran addinin ƙasar tun bayan juyin juya-halin ƙasar da aka yi a 1979 da aka hamɓarar da mulkin sarauta ta Mohammad Reza Pahlavi.

Zuwa yanzu ƙasar ta yi jagororin addini guda biyu ne: Ayatollah Ruhollah Khomeini (wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci a ƙasar) sai wanda ya gaje shi, marigayi Ayatollah Ali Khamenei

Shi ne jagoran ƙasa kuma babban kwamandan tsaron ƙasar. Yana da iko a kan rundunar ƴansanda da kuma jami'an Hisbah na ƙasar.

Jagoran addinin ne kuma yake da iko a kan dakarun juyin juya-hali ta ƙasar, wadda ita ce rundunar da ke kula da harkokoin tsaro na cikin gida, tare kuma da ɓangarenta na sojojin sa-kai da ake kira Basij.

Wannan runduna ta sojin sa-kai ta sha murƙushe tarzoma da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Iran.

Jagoran addinin ne kuma yake naɗa alƙalai da rabin majalisar shura da limamai da shugabannin gidajen rediyo da talabijin.

A shekarar 1989 ne Ayatollah Ali Khamenei ya zama jagoran addinin ƙasar bayan rasuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini.

Rais wa Iran Masoud Pezeshkian.

Asalin hoton, John Lamparski/Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian

Shugaban ƙasa

Shugaban ƙasa, shi ne babban jami'i na biyu bayan babban jagoran addinin kuma shi zaɓaɓɓe ne.

Shi ne ke da alhakin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati kuma yana da tasiri sosai a kan manufofin ƙasar na cikin gida da kuma waje.

Sai dai kuma duk da haka ana iya cewa ikonsa yana da iyaka musamman idan ana maganar harkokin tsaro.

Haka shi ma kwamandan rundunar sojin juyin-juya-hali da kuma ɓangaren wannan runduna na sojin sa-kai wato Basij duk suna ƙarƙashin ikon jagoran addinin ne.

Shugaban ƙasar na yanzu shi ne Masoud Pezeshkian, wanda aka zaɓa bayan mutuwar Ibrahim Raisi a haɗarin jirgin sama a watan Mayun 2024.

Majalisa

Bunge la Iran.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Majalisar Iran

Majalisar Iran na da mambobi 290, waɗanda ake zaɓa su yi shekaru huɗu.

Majalisar ce ke yin dokoki da nazari tare da tabbatar da kasafin kuɗi da naɗawa ko cire ministoci, sannan suna iya cire shugaban ƙasa.

Sai dai duk dokokin da suka yi, dole sai majalisar shura ta ƙasar ta amince da su kafin su zama doka.

Tsohon hoton Ahmad Jannati, sakataren majalisar shura ta ƙasar

Asalin hoton, ATTA KENARE/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon hoton Ahmad Jannati, sakataren majalisar shura ta ƙasar

Majalisar shura

Majalisar shura ta ƙasar na da matuƙar ƙarfin gaske, musamman wajen nazari tare da amincewa da ƙudurorin da majalisar ta amince da su kafin su zama doka, kuma tana da ikon watsi da ƙudurorin, musamman idan sun saɓa da shari'ar Musulunci.

Haka kuma majalisar na iya dakatar da mutum daga shiga takarar majalisa da shugaban ƙasa da sauransu.

Yanzu haka Ahmad Jannati ne sakataren majalisar.

Majalisar ta shura tana da mambobi 12; manyan malamai guda shida waɗanda jagoran addinin ƙasar ke zaɓa, masana shari'a guda shida da kotu ke zaɓa, majalisa kuma ta tantance su, ta amince da su.

Majalisar ƙwararru

Tsohon hoton majalisar ƙwararru

Asalin hoton, MOHAMMADALI NAJIB/Middle East Images/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon hoton majalisar ƙwararru

Majalisar ƙwararru na da mambobi 88, waɗanda malamai ne masana addini, kuma su ne suke zaɓen jagoran addinin ƙasar da bibiyar ayyukansa.

Idan aka tabbatar da cewa jagoran addinin ba ya iya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, majalisar na da ikon sauke shi.

Yanzu haka Movahedi Kermani ne shugaban majalisar ta ƙwararrun ƙasar.

Tsohon hoton Ali Movahedi Kermani

Asalin hoton, MOHAMMADALI NAJIB/Middle East Images/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon hoton Ali Movahedi Kermani

Idan jagoran addinin ya rasu, ko ya zama ba ya iya sauke nauyinsa, majalisar na gudanar da zaɓe a cikin sirri domin naɗa sabo.

Ana gudanar da zaɓen majalisar ne duk bayan shekara takwas.

Majalisar shawara

Aikin wannan majalisar shi ne ba jagoran addinin ƙasar shawara, sannan ita ce ke da wuƙa da nama idan aka samu saɓani bayan majalisa ta yi doka.

Jagoran addinin ne ke zaɓen mambobin majalisar guda 45, waɗanda suka ƙunshi fitattun malaman addini da jagororin siyasa. Shugaban majalisar a yanzu shi ne Ayatollah Sadeq Larijani, wanda tsohon alƙalin alƙalai ne a ƙasar.

Kotu

Picha ya zamani ya Mkuu wa Mahakama nchini Iran, Gholam Hossein Mohseni Ejei.

Asalin hoton, Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images

Jagoran addinin ƙasar ne ke da ikon naɗa babban alƙalin ƙasar, kuma a ƙarƙashin ikonsa yake.

Kotunan ƙasar da alƙalai ne ke aikin tabbatar da ana amfani da dokokin shari'ar Musulunci a ƙasar.

A yanzu, babba alƙalin ƙasar shi ne Gholamhossein Mohseni Ejei.

Dakarun tsaro

.

Asalin hoton, tta KENARE / AFP) (Photo by ATTA KENARE/AFP via Getty Images

Dakarun tsaron ƙasar sun ƙunshi dakarun juyin juya-hali wato IRGC da kuma rundunar soji.

An kafa dakarun IRGC ne bayan juyin juya-halin da aka yi a ƙasar domin kare Jamhuriyar Musuluncin ƙasar.

Sai kuma akwai rundunar sojin ƙasa da ta sama da ta ruwa.

Dukkan manyan kwamandodjin dakarun juyin juya-halin da na sauran ɓangarorin tsaron suna ƙarƙashin jagoran addini ne.

Ministoci

Ministoci da sauran ma'aikata gidan gwamnati kuma suna ƙarƙashin ikon shugaban ƙasa ne, sai dai duk waɗada ya zaɓa, dole ne sai majalisa ta tantance su kafin su fara aiki.

Ministocin suna kasancewa ne a ƙarƙashin shugaban ƙasa, ko mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya wanda shi ne ke da alhakin kula da ayyukan ministoci.

Ƴan Hisba

.

Asalin hoton, ALI RAFIEI/Middle East Images/AFP via Getty Images

Jami'an Hisbah wani ɓangare ne na rundunar ƴan-sandan ƙasar ta Iran.

An kafa su ne a shekara ta 2005 domin tabbatar da mutane na sanya tufafi kamar yadda dokokin Musulunci suka tanada.

An yi ƙiyashin akwai jami'an Hisba kusan 7,000 da suka ƙunshi maza da mata , suna da ikon yi wa mai laifi gargaɗi ko cin tara ko kuma kamawa.

Dakarun juyin juya-hali

Dakarun juyin-juya-hali a Iran su ne ke aikin tabbatar da tsaro a cikin gida.

An kafa ta ne bayan juyin-juya-halin domin ta tabbatar da tsarin dokokin Musulunci a ƙasar.

A yanzu wannan runduna mai matuƙar tasiri ta ƙunshi harkokin soji da siyasa da kuma tattalin arziki a Iran, inda take da sama da jami'ai dubu 150, sannan ita ke kula da muhimman makaman ƙasar.

Haka kuma tana da reshenta na waje da ake kira Quds, wadda a cikin sirri take samar da kuɗaɗe da makamai da fasaha da kuma horas da abokanta a fadin Gabas ta Tsakiya.

Bugu da ƙari ita ke tafiyar da harkokin reshenta na sojin sa-kai wato Basij.