Mayaƙan Kurɗawa: Dabar da mata zalla ke jagoranta a asirce

Asalin hoton, Valentina Sinis
- Marubuci, Kawoon Khamoosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Erbil, Iraq
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai, a Iran ana ci gaba da raɗe-raɗin cewa ƙungiyoyin Kurɗawan Iran masu ɗauke da makamai da ke zaune a Iraƙi za su tsallaka ƙasar domin shiga yaƙin da Jamhuriyar Musulunci.
A matsayin martani, Iran ta ƙaddamar da hare-hare masu yawa kan ƙungiyoyin Kurɗawan, ciki har da na makami mai linzami wanda ya kashe wani mayaƙin kungiyar ɗaya.
Sai dai a wani jawabi da ya yi ranar Asabar, Shugaba Trump ya ce ba ya son Kurɗawan su shiga cikin yaƙin.
BBC ta samu damar ziyartar ɗaya daga cikin waɗannan ƙungiyoyi na Kurɗawa - wadda duka bataliyar mata ne.
BBC ta ɗauki kwanaki ana tattaunawa kafin samun damar shiga sansanin nasu da kuma hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da suke gudanar da aikinsu a arewacin Iraƙi.
Suna gudanar da sadarwa a asirce yayin da suke zaune a wuraren da babu titunan ko lantarki a yankin Kurdistan mai ƙwarya-ƙwaryar ƴancin kai.
Mace mai ɗaukar hoto guda ɗaya kawai aka bari ta shiga yanki, wadda ta yi kwana 10 tare da Kurɗawan.
A cikin gomman shekarun baya-bayan nan da dama cikin mayaƙan ƴantawayen Kurdawa daga Iran sun koma kan tsaunuka a kan iyakar ƙasar da Iraƙi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Suna ɓoye wa jami'an leƙen asirin Iran, da kuma ƴan Shi'a a Iraƙi da sojojin Turkiyya.
A baya-bayan nan manyan ƙungiyoyin Kurɗawan a arewacin Kraƙi sun ƙulla ƙawance da juna, inda aka riƙa samun bayanan cewa Shugaba Trumo ya tattauna da shugabanninsu, inda ya buƙaci su shiga yaƙin Iran.
Cikin wata hira ta waya da kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar 5 ga watan Maris, Mista Trump ya ce ya goyi bayan hare-haren da Kurɗawan ke kai wa Iran, yana mai cewa ''Ina tunanin abin a yaba ne idan suka yi hakan.''
To amma a ranar Asabar Shugaba Trump ya faɗa wa ƴanjarida cewa ba ya buƙatar Kurɗawa su shiga yaƙin Iran ta ƙasa.
''Ba ma son yaƙin ya sake dagyulewa fiye da yadda yake a yanzu,'' in ji shi.
Ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin da suka shirya wa yaƙin mai suna PJAK, ta ce sun jima suna shirin wannan yanayi, ranar da za su shiga Iran.
"Zan yi faɗa don ƙwato wa iyali da Kurɗawa yanzi da aka jima ana atuye musu,'' a cewar Aryen mai shekara 21.
Ta kasance mamba a sashen rundunar tsaron mata na ƙungiyar PJAK.
A matsayinta na Bakurdiwa, Aryen ta ce ta kwashe dimbin rayuwarta cikin zalunci da nuna mata wariya a Iran, don haka ta rasa zaɓi illa ɗaukar makamai.
Shekara biyu da suka wuce ne ta shiga ƙungiyar PJAK.
Sansanonn sirri na soji

Asalin hoton, Valentina Sinis
Hanyoyin ƙarƙashin ƙasa sun kasance dandazin tudun mun-tsira na abinci da kudi da kuma harsasai.
Galibi ƙungiyar PJAK na ɓoye sirrin mayaƙanta, amma akwai mayaƙanta mata kusan 60 da ke samun horo a wannan sansani kafin fara yaƙin Amurka da Isra'ila da kuma Iran.
Mayaƙan kan samu horon soji, musamman samun ƙwarewar aikin da dabarun iya harbi kamar ƙwarewar iya harbi daga nesa da jirage masara matuƙa.
Sukan kuma je gwajin lafiya, idan ana shirin tura su fagen daga, yayin da zaman ɗarɗar ke ƙaruwa akan iyakar ƙasashen biyu, bayan ɓarkewar yaƙin Amurka da Iran.
"Mun jima nuna jiran wannan yaƙi," a cewar gelawej ewrin mai shekara 40.
A lokacin da take shekara 20, Ewrin ta fice daga garinta a birnin Urmia na Iran, inda ta shiga ƙungiyar PJAK a matsayin soja, har ta kai matakin kakakin ƙungiyar.
Yayin da take magana daga maɓoyarta, Ewrin ta ce ta shafe rabin rayuwarta a kan tsaunuka, kuma ba ta sake ganin danginta ba tun bayan ficewa daga gida.
Ta ce duk da cewa Khamenei ya mutu ne a hare-haren baya-bayan nan, amma jerin zanga-zangar da mata suka yi a farkon 2022 ya fito da raunin gwamnatinsa.

Asalin hoton, Valentina Sinis
Zaɓi ɗaya kacal
Zanga-zangar, wadda ta faro sakamakon mutuwar Mahsa Amini a hannun jami'an tsaro, ta kasance abin da ya burge wasu mayaƙan PJAK.
Kafin shiga PJAK, Begen mai shekara 18 ta shiga zanga-zangar inda ta ƙi ɗauka ɗankwali a makaranta a matsayin nuna rashin ɗa'a ga gwamnati.
"Ba mu da zaɓi da yawa," a cewar Bigen yayin da take yi wa ɗaya daga cikin takwarorinta mayaƙa kitso.
"Ko dai mu fuskanci musgunawa a cikin gidaje da hanu mu damrmaki, ko kuma mu kare kanmu ta hanyar yin tawaye.''
An sha zargin mayakan tawayen Kurɗawa da ɗaukar yara ƙananan a matsayin mayaƙa, kuma Begin na karatun sakandire alokacin da ta shiga ƙungiyar shekara uku da suka gabata.
Mafi yawan mayaƙan da muka zanta da su, sun ce turje wa gwamnati ne kawai hanyar ɓullewa.
"Ina faɗa ne domin kwato makomar yaran Kurɗawa masu tasowa," a cewarDelal, likitar haƙori, da ta shiga yaƙin sar-ka-noƙe lokacin tana shekara 23.
"Ga al'ummar Kurdawa... shekaru 200 da suka gabata sun kasance shejarun azabtarwa da zalunci gare su," in ji ta.
An kafa ƙungiyar PJAK a 2004, wadda ke da alaƙa da jam'iyyar PKK, ƙungiyar ƴan'aware a Turkiyya, wadda ta ajiye makamai a shekarar da ta gabata bayan shekara 40 na rikici da gwamnatin Turkiyya.
PJAK ta ce ta martaba matakin, amma Kurdawan Iran za su ci gaba da riƙe makamai don hyaƙar Jamhuriyar Musulunci
Duka Ƙasashen Turkiyya da Iran na kallon ƙungiyar amatsayin ta ata'addanci.
Fargabar yaƙin basasa

Asalin hoton, Valentina Sinis
Mayaƙan Kurɗawan na sani da girman barazanar da ke gabansu, musamman yiwuwar samun arangama da dakarun Iran masu manyan makamai.
"Ba ma fatan shiga yaƙin basasa'', kamar yadda Ewrin ta shaida wa BBC.
"Za mu yi duk mai yiwuwa don jagorantar yaƙin ruguza gwamnatin Iran, domin sama wa yara masu tasowa makoma,'' in ji ta .
Kurɗawa ne kashi 10 cikin 100 na al'ummar Iran miliyan 90, kuma a cikin gomman shekaru suna ganin gwamnatin ƙasar na nuna musu wariya da cutar da su.
Tehran ta jima tana kai hare-hare kan ƙungiyoyin mayaƙan Kurdawa a yankin Kurdistan na Iraƙi.
BBC ta tattauna da shugabannin sabon ƙawancen inda ta tambaye su kan kiran da Shugaba Trump ya yi musu, amma sun ƙi cewa komai, sannan suka musanta iƙirarin da ke cewa dakarunsu sun tsallaka kan iyakar Iran domin shiga yaƙin.
Wane mataki za su ɗauka?

Asalin hoton, Valentina Sinis
Sauran ƙungiyoyin Kurɗawa na ƴan'adawa a Iran sun ce suna nazarin halin da ake ciki yayin da suke auna matakan da su zu iya ɗauka.
Mustafa Hijri, shugaban jam'iyyar KDPI, ya ce burinsu shi ne " su mulki yankin Kurdistan na Iran idan aka samu sauyin gwamnati" sannan ya kira magoya bayansa su kauce wa yin kalaman da za su kawo matsala wa fannin tsaro.
To amma wasu mayaƙan Kurɗawan na bayyana shakku kan ko za su iya dogara da goyon bayan Amurka a kowane yaƙi.
Wata majiya mai alaƙa da mahaƙan Kurɗawa na Iran ta shaida wa BBC cewa ƙungiyoyin mayaƙan ba su shigar da mayaƙansu cikin Iran ba, har sai sun tabbatar da samun goyon bayana Amurka.
Ya yi imanin cewa sojojin Iran na da ƙarfin gaske, kuma mayaƙan Kurɗawa ka iya fuskatar ''murƙushewa'' idan suka ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa cikin Iran.
Ga matan mayaƙan Kurɗawa ''ƴancin'' da suke nema zai jima bai zo musu ba.
A yanzu Delal ta bar sansanin samun horo, inda aka turata kusa da kan iyaka.
Idan Kurɗawa za su shiga yaƙi da gwamnatin Iran, babu tabbas kan lokacin da faɗan zai ɗauka, da ma abin da hyaƙin zai haifar.
Ƙarin rahoto daga Valentina Sinis
Ba a bayyana sunayen Mayaƙan mata na gaskiya ba, an yi amfani da inkiya ne wajen bayyana sunayen nasu.











