Yadda ƴan adawar Najeriya ke shirin zaɓukan fidda gwani

Jagororin adawa a Najeriya

Asalin hoton, FB/Multiple

Lokacin karatu: Minti 2

Alamu na nuna cewa jam'iyyun adawa a Najeriya za su bi hanyar cimma maslaha ne tsakanin ƴan takararsu gabanin babban zaɓen ƙasar na 2017.

A watan Faburairu ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026, da aka yi wa gyaran fuska.

Shugaban na Najeriya ya sanya hannu kan dokar ne bayan hargitsin da aka samu a zaurukan majalisar tarayyar ƙasar da ma zanga-zangar da ƙungiyoyin fararen hula suka yi game da gyaran da aka yi wa dokar.

Daga cikin manyan gyare-gyaren da aka yi wa dokokin zaɓen akwai wanda ya shafi hanyoyin da jam'iyyu ke bi wajen zaɓen mutanen da za su tsaya musu takara a kujeru daban-daban, wato zabukan fitar da gwani.

A baya jam'iyyun siyasa kan yi amfani da wasu wakilai na musamman da ake kira 'deliget' a turance, waɗanda ake zaɓa a matakai daban-daban, tun daga matakin akwati da mazaɓa har zuwa matakin ƙasa.

Dalaget sun yi kaurin suna a baya, musamman lokacin zabukan fitar da gwani.

Amma a bisa sabuwar dokar zaɓen Najeriya ta 2026, hanyoyin biyu da dokar ta amince da su domin zaɓukan fitar da gwani a cikin gidan jam'iyyun siyasa kuma su ne masalaha da kuma ƴar tinƙe ko ƙato-bayan-ƙato.

Jam'iyyun ADC ta ce tana Kallon wannan tsari na maslaha tsakanin ƴan takara domin fitar da wanda ya dace a matsayin hanyar rage yawan kudin da ake kashewa wajen fitar da ƴan takara, gashi kuma mai sauƙin aiwatarwa domin haka ta fi karkata gare shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Faisal Kabir na daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar kuma ya shaidawa BBC cewa ƙofarsu a buɗe take kuma ba za su bayar da wata kafa ta kawo cikas ga ƙoƙarin ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC ba, ta duk wata hanya da doka ta tanada.

Ya ce ''komai zai iya faruwa(game da hanyar fitar da ƴan takara a ADC), babban abin da muka sa a gaba shi ne yadda za mu kawar da gwamnatin Bola Tinubu, muna ci gaba da tattaunawa domin samar da ɗan takara guda ɗaya wanda zai ƙalubalanci jam'iyyar APC.''

Ita ma jam'iyyar PDP na da irin wannan ra'ayi, kamar yadda mai magana da yawun jam'iyyar Farida Umar, ta tabbatar.

Ta ce PDP tana ƙoƙarin samar da ɗan takara mai nagarta da zai kai ta ga nasara a babban zaɓen na 2027, kuma zaɓin amfani da tsari irin na maslaha na gaba-gaba a cikin zaɓin da take da su.

A cikin wani bayani da sakataren watsa labaran jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnsoin ya fitar, ya ce jam'iyyar ta ce tana ci gaba da tattaunawa domin samar da haɗin kai tsakanin masu muradin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashinta.

Masana lamurran siyasar ƙasar dai na ganin wannan matakin jam'iyyun na neman tabbatar da sun hada kansu, da ma na 'ya'yansu, koda kuwa ta cimma maslaha ne domin tsayar da dan takara, na zama tamkar wani darasi ne suka koya daga babban zaben da ya gabata na shekarar 2023.