Yadda aka kashe Kacalla Alti, ɗanbindigan da ke ‘dasa bama-bamai‘ a Zamfara

Asalin hoton, Others
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga 45 da suka kai hari wani ƙauye a jihar Katsina da ke arewacin ƙasar.
Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Katsina, Hon. Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa cikin ƴanbindigar da aka kashe har da wasu manyan kwamadandojin ƴanbindiga biyu da suka addabi wasu yankunan jihohin Katsina da Zamfara, wato Kacalla Alti da Kacalla Damale waɗanda dukkansu yan'uwan juna ne.
Lamarin ya faru ne ranar Juma'a da maraice kamar yadda hukumomin jihar suka tabbatar.
Rahotonni sun ce tun da farko ƴanbindigar waɗanda suka taso daga jihar Zamfara mai makwabtaka, sun kai hari ƙauyen Alhazawa na ƙaramar hukumar Danmusa a ranar Alhamis domin satar shanu.
To sai dai mazauna garin sun nuna turjiya inda suka kashe huɗu daga cikin maharan.
Kwana daya bayan hakan ne kuma ƴanbindiga suka sake taruwa da nufin ɗaukar fansa kan mazauna ƙauyen, inda suka ci karo da sojoji a kan hanyar tasu, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakani.
Bayanai na cewa an kashe sojojin ƙasar uku a lokacin gumurzun.
Wane ne Kacalla Alti?

Asalin hoton, others
Ana yi wa Kacalla Alti kallon mataimaki ga ƙasurgumin ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna a jihohin Katsina da Zamfara, wato Ado Aliero.
Mannir Sani Fura Girke, ya ce, kacalla Alti ɗan'uwa ne ga Ado Aliero.
''Mahaifinsa ƙani ne ga mahaifin Ado Aliero, don haka za ka iya ce masa ƙanin Ado Aliero,'' in ji shi.
Ya kuma ce shi Kacallah Alti ƙani ga kacalla Isuhu Yalo, wanda shi ma shahararen ɗan bindiga ne da sojojin Najeriya suka kashe a shekarar da ta gabata.
''Shi ne ma ya gaji dabar yayan nasa wato Isuhu Yalo da ke cikin dajin Munhaye, inda ya riƙa ƙaddamar da hare-hare musamman a yammacin ƙaramar hukumar Tsafe a Zamfara,'' in ji shi.
Ƙawancensa da Boko Haram

Asalin hoton, Others
Mannir Fura Girke ya ce daga baya-bayan nan Kacalla Alti ya kulla ƙawance da mayakan Boko Haram, inda har ya riƙa gayyato su zuwa yankunan da yake kai hare-hare.
A cewar ɗan jaridar mai binciken ayyukan yan fashin daji, a baya-bayan nan ma ya gayyato ƴan Boko haram inda suka riƙa dasa nakiyoyi a kan hanyar Tsafe zuwa Funtuwa.
''Za ka iya cewa ma kacalla Alti ya rikiɗe daga ɗan fashin daji zuwa ɗan Boko Haram'', kamar yadda Fura Girke ya bayyana.
Wuraren da Kacalla Alti ya fi kai hare-hare
Fura Girke ya ce yankunan da kacallah Alti ya fi kai hare-hare sun hada da Danmusa da Faskari da Kankara a jihar Katsina.
''Sai kuma ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara da garuruwan da ke yammacin ƙaramar hukumar'', in ji shi.
Ɗanjaridar ya kuma ƙara da cewa Kacalla Alti ya kuma yi ƙaurin suna wajen tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtuwa.
Me ya sa ƴanbindiga ke kai wa Katsina hari duk da sulhu?

Asalin hoton, others
Hon. Nasiru Mu'azu ya ce galibi yanbindigar da ke kai hare-hare ba yan jihar ba ne.
''Galibi sukan fito ne daga jihohin Zamfara da Kaduna, mu kam a jihar Katsina ba za ka ce babu ba, amma gaskiya an samu raguwar su sosai tun bayan sulhun da aka yi'', in ji shi.
Shi ma Mannir Sani Fura Girke, ɗan jarida mai bincike kan ayyukan yan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya ya ce yanbindigar da ke jihar Katsina ne aka yi sulhu da su a jihar Katsina.
''Su kuma waɗannan daga jihar Zamfara suke fita su shiga jihar Katsina su kaddamar da hare-harensu su kuma koma'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Wace nasara kashe Alti zai kawo?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mannir Fura Girke ya ce kisan Kacalla Alti ba ƙaramar nasara ba ce a yaƙin da sojojin Najeriya ke yi da yanbindigar daji.
''Saboda a yanzu za a iya cewa ɓarnar da yake yi kusan babu wani ɗanbindiga da ke irin ta a wannan yanki na tsakanin Tsafe da faskari da Kankara da Danmusa,'' in ji shi.
Mai binciken harkokin yanfashin dajin ya kuma ce shigarsa Boko Haram ba ƙaramar illa zai haifar wa yankin ba.
''Saboda shigarsa Boko Haram har ta ba shi damar dasa nakiyoyi a kan titunan yankin da yake ƙaddamar da hare-hare'', in ji Fura Girke.
Don haka ne mai bincike kan ayyukan yanfashin dajin ke ganin kisansa zai kawo zaman lafiya a yankunan Tsafe da Danmusa da Kankara da kuma yankin Faskari.
A kwanakin baya-bayan nan ‘yan bindiga sun fito da wani salo da dasa ababen fashewa kan hanyoyi a jihar Zamfara.
A baya-bayan nan matafiya kan hanyar Funtua zuwa Gusau sun shiga cikin farbaba bayan nakiya ta tashi da wata motar tirela, sai dai babu wanda ya rasa ransa a sanadiyyar hakan, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Masana sun rika nuna fargaba kan wannan salo da ‘yan bindigar suka bullo da shi, wanda akasari an fi ganin hakan ne tattare da mayakan Boko Haram wadanda suka dade suna addabar yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma yankin tafkin Chadi.











