Wane ne Auta, riƙaƙƙen ɗan bindiga da sojojin Najeriya suka kashe?

Kacalla Auta

Asalin hoton, Nigerian Army/X

Lokacin karatu: Minti 3

Bayanai na ƙara fitowa game da farmakin da sojojin Najeriya suka kai wanda ya yi sanadin halaka ƙasugumin ɗanbindiga, Sale Ado Madale da aka fi sani da Kacalla Auta a Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar sojin ƙasar, Manjo Janar Markus Kangaye ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce sojojin sun samu hallaka ƴan bindigan ne a wani samame na musamman da rundunaar Fasan Yamma ta yi kan gungun ƴan bindigar a yankin Ƙunchin Kalgo na ƙaramar hukumar tsafe ta jihar Zamfara.

Jami'an tsaron sun ce sun kai wani harin a Ɗanjibga, gidan mai mutum inda suka kashe mutum 10, sai kuma na Ƙunchin Kalgo inda a nan ma mutum shida aka kashe, cewar wani ɗanjarida mai bincike a yankin.

Ɗaya daga cikin manyan 'yanbindigan da aka kashe a farmakin shi ne Kachalla Auta, wanda aka daɗe ana nema ruwa a jallo saboda hannu da yake da shi a aikata munanan laifuka da tashe-tashen hankula a yankin.

Wane ne Kacalla Auta?

Wani ɗan jarida mai binciken ƙwaƙaf, Mannir Sani Fura-Girke ya yi wa BBC ƙarin bayani cewa riƙaƙƙen ɗanbindiga ne da dakarun Najeraya suka jima suna nema ruwa a jallo saboda ta'addancinsa.

''Fitaccen ɗanbindigar ne da ya yi fice wajen garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa, wanda ya addabi yankunan jihar Zamfara da wasu yankunan jihar Katsina'',in ji Fura Girke.

"Yana cikin masu kai hare-hare a wajajen Kaita, Ƙuncin Kalgo, Ɗanjibga da garuruwan da ke yammacin ƙaramar hukumar Tsafe", in ji ɗan jaridar mai bincike.

''Su ne suke addabar yankin Tsafe na jihar Zamfara da wasu yankunan ƙananan hukumomin Faskari da Bakari da Dandume da Kankara a jihar Katsina'',in ji shi.

Ya ƙara da cewa Kacalla Auta ɗa ne ga Kacalla Ado Aliero - ƙasurgumin ɗanbindigar nan da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar.

A cikin watan Maris ne jami'an tsaron Najeriya suka hallaka Ishuhu Yellow - wanda ƙani ne ga Aliero, a wani farmaki da jami'an tsaron haɗin gwiwa na ƴansanda da askarawan Zamfara da ƴan sa-kai da mafarauta

Munnir Fura-Girke ya ce ''tun bayane kashe Kacallah Isuhu, Auta ne ya maye gurbinsa a matsayin jagoran dabar tasa''.

'Sojoji sun sauya salon yaƙin da ƴanbindiga'

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Army/X

Mannir Fura-Girke ya kuma ce a yanzu jami'an tsaron ƙasar sun sauya salon yaƙi da ƴanbindigar.

''A yanzu jami'an tsaron sun fi mayar da hankali wajen fita farautar ƴanbindigar, maimakon su jira sai sun kawo hari da kore su'', in ji shi.

Ya ce a yanzu sojojin fita suke , su je har inda ɓarayin suke domin kai musu hari.

Dama dai masana harkokin tsaro sun jima suna kira ga sojojin ƙara su sauya salon yaƙi da ƴanbidigar ta hanyar kai musu hare-hare har maɓoyarsu, maimakon jira su kawo hari don mayar da martani.

Fura-Girke ya ce Idan sojojin suka ci gaba da amfani da wannan salo, da yiwuwar a samau nasara a yaƙin da suke yi da ƴanbindiga a ƙasar.