Rasha na ci gaba da yin luguden wuta a kan Ukraine, yayin da ƙasar ke cika shekara huɗu tun bayan ƙaddamar da mamaya kan Ukraine.
Jami'an Ukraine sun ce mutane biyar, ciki har da yaro guda sun ji rauni kuma an lalata gidaje da dama a hare-haren jirage marasa matuƙa, musamman a birnin Zaporizhzhia.
An tsara gudanar da tarukan tunawa da ranar mamayar a wurare da dama, kamar Bucha, inda dakarun Rasha suka kashe sojojin Ukraine da dama.
Ana sa ran shugabanni da 'yan siyasa daga faɗin Turai za su halarci Kyiv babban birnin Ukraine din don halartar tarukan.
Sabon harajin kashi 15 da Trump ya laftawa ƙasashen duniya ya fara aiki
Asalin hoton, Getty Images
Sabon harajin kashi 15 cikin 100 da shugaban Amurka, Donald Trump ya laftawa dukan ƙasashen duniya ya fara aiki.
Ya sanar da matakin ne, bayan hukuncin da Kotun ƙolin ƙasar ta yanke ranar Juma'a, inda ta ayyana haraje harajen da yake sanyawa a matsayin waɗanda suka saɓa wa doka.
A yanzu dai sabon harajin na kaso 15 da ya sanya ƙarƙashin wata dokar ta daban ya shafi hatta ƙawayen Amurka, ciki har da Birtaniya da Australia.
To amma duk da haka zai kasance wani sauƙi ga wasu ƙasashen kamar China da Brazil waɗanda ke takun sakar tattalin arziki da gwamnatin Trump.
Hukuncin da kotun ƙolin ta yanke ya janyo dakatar da yarjejeniyoyi da dama na cinikayyar ƙasa da ƙasa da aka amince da su ko kuma ake ƙoƙarin cimma matsaya kansu da Amurkar.
'ICPC ta ƙi ba da belin El-Rufai'
Asalin hoton, El-Rufai/X
Lauyoyin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun ce har yanzu ba su samu wata amsa daga Hukumar yaƘi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ba kan buƙatar belinsa da suka gabatar, duk da cewa wa’adin awanni 48 na tsare mutum ba tare da tuhuma ba ya cika.
Mai taimaka wa El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan a shafinsa na X cewa
Sanawar ta ce "lauyoyin sun bayyana cewa har yanzu ba a nuna musu wata takardar umarnin kotu da ta ba da izinin ci gaba da tsare shi ba.
A cewarsu in ji sanarwar, wannan na zuwa ne bayan an miƙa shi daga hannun hukumar EFCC zuwa ICPC a daren 18 ga Fabrairu, bayan ya kai kansa ofishin EFCC da safiyar 16 ga watan domin amsa gayyatar da suka yi masa..
A makon nan ne kuma ake sa ran kotu za ta saurari wasu ƙararraki biyu da suka shafi lamarin.
Ɗaya daga cikinsu ita ce karar take hakkinsa na dan Adam da ya shigar kan Gwamnatin Tarayya da hukumomin bincike ciki har da hukumar ICPC, wadda za a saurara a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja ranar 25 ga Fabrairu.
A cikin ƙarar, yana neman kotu ta umarci a sake shi bisa beli, yana mai cewa tsare shi da aka yi ba tare da cika sharuɗɗan doka ba ya saɓa haƙƙoƙinsa a matsayin ɗanadam.
Ana kuma sa ran a rana guda za a gurfanar da shi kan tuhume-tuhumen da DSS ta riga ta shigar.
Lauyoyinsa sun jaddada cewa rashin amsa buƙatar belin da kuma rashin nuna takardar umarnin tsarewa na daga cikin abubuwan da suke ƙalubalanta a shari’a, yayin da suke jiran matakin kotu kan buƙatunsu.
Me zai bambanta zaɓen Najeriya mai zuwa da waɗanda suka gabata?
Ƴan Najeriya na sa ran ganin sauye-sauye a hanyoyin gudanar da zaɓukan ƙasar a zaɓen 2027 da ke tafe nan da shekara guda.
Ana sa ran ganin sauye-sauyen ne bayan fara aiki da sabuwar dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyaran fuska.
A makon da ya gabata ne shugaban ƙasar da ya sanya hannun kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026, in da aka samar da manyan gyare-gyare, wadanda za su shafi tsarin gudanar da zaɓukan ƙasar.
Sauye-sauyen na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafen ƴan ƙasar, kan wasu dokokin zaɓen ƙasar da suke ganin ba su dace da yanayin ƙasar ba.
An dai kai ruwa rana a majalisar dokokin ƙasar kafin amincewa da sabbin dokokin, lamarin da ya kai ƙungiyoyin fararen hula shirya zanga-zangar matsin lamba ga majalisar dokokin ƙasar domin amincewa da sakamakon.
An ɓullo da sauye-sauyen masu yawa a tsarin zaɓen ƙasar, kama daga kan fitar da ƴan takara zuwa yakin neman zaɓe da ma tattara sakamako.
Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin akwai sauye-sauye da za a gani a tsarin zabukan kasar masu zuwa.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.
Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.