Zargin kashe Kiristoci: Matakai 6 da ake son Trump ya ɗauka a kan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar wakilan Amurka ta kammala tare da miƙa rahoton binciken da ta yi kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana jan hankali tare da haifar da zazzafar muhawara.
Ɗanmajalisar wakilan Amurka, Riley M. Moore ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, wadda ya bayyana da rahoton da za su miƙa ga Shugaban Amurka Donald Trump.
More ya ce rahoton ya ƙunshi cikakken bayanin kan abin da ka bankaɗo da kuma wasu matakan da suke so a ɗauka domin "kawo ƙarshen muzgunawa Kiristoci a Najeriya."
Sauran ƴan majalisar da suka taya Moore aikin sun haɗa da wasu ƴan kwamitin majalisar kan kasafin kuɗi da na harkokin ƙasashen waje, inda suka je tare zuwa fadar gwamnatin Amurka domin miƙa rahoton a hukumance.
Sun yi wannan aikin ne bayan an kafa kwamitin bincike a majalisa, biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke buƙatar sa ido da Trump ya yi a ranar 31 ga watan Oktoban 2025.
Tun a lokacin ne Trump ya buƙaci Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Amurka Tom Cole da su jagoranci wani kwamiti na musamman domin gano gaskiyar zargin muzgunawa Kiristoci da sauran matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya ce, "wannan rahoton ya biyo bayan nazari da bincike na watanni, ciki har da zuwa da ƴanmajalisar Amurka ta yi Najeriya domin bincike da tattaunawa da masana da jagororin addini da ma tattaunawa da ƴan gudun hijira da kuma manyan jami'an gwamnatin Najeriya," in ji shi a sanarwar.
Matakan da za a ɗauka
A sanarwar da Moore ya fitar bayan miƙa rahoton binciken, ya ce sun ba gwamnatin Amurka wasu muhimman shawarwari na matakan da suke so a ɗauka domin magance matsalar.
Daga cikin shawarwarin da suke ƙunshe a cikin rahoton akwai:
- Shiga yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya domin kare garuruwan Kiristoci da ke fuskantar muzgunawa da fatattakar mayaƙa masu iƙirarin jihadi.
- Dakatar da wasu tallafi ga Najeriya har sai an ga matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wajen hana muzgunawa Kiristoci
- Sanya takunkumi da hana biza ga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da suke da hannu a tauye ƴancin gudanar da addini.
- Taimakon gwamnatin Najeriya domin daƙile ayyukan Fulani masu riƙe da makami.
- Neman soke shari'a Musulunci da kisa kan ɓatanci a Najeriya
- Aiki tare da ƙasashen waje irin su Faransa da Hungary da Birtaniya domin samun nasara.
'Wahalar da Kiristocin Najeriya ke fuskanta'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A sanarwar, ɗanmajalisa Riley M. Moore ya ƙara da godiya ga Trump bisa ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da yake sa ido, inda ya ce Kiristocin ƙasar sun daɗe suna fuskantar barazana.
"Bayan tattaunawar da muka yi a fadar gwamnatin Amurka, ina so zan ƙara jaddada godiya ga Shugaba Trump bisa ayyana Najeriya da ya yi a matsayin ƙasar da yake sa ido a kanta. Hakan ya ƙara nuna yadda gwamnatinsa ke damuwa da halin da ƴanuwanmu Kiristoci suke ciki."
Ya ce wannan ne zai taimaka wajen kare Kiristocin Najeriya daga muzgunawa da ma taimakon ƙasar wajen yaƙi da matsalolin tsaro.
"Tun bayan da Trump ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da yake sa ido da kuma ba ni aikin gudanar da bincike ne fara bincike, inda na yi aiki tuƙuru wajen tattara bayanan da muka miƙa wa Trump ɗin," in ji shi.
Ya ce yana ƙara godiya ga sauran waɗanda suka taya shi aikin, ciki har da shugaban kwamitin kasafin kuɗi a majalisar wakilan Amurka Tom Cole da mataimakinsa Mario Diaz-Balart, da shugaban kwamitin harkokin ƙasashen waje, Brian Mast da ɗanmajalisa Chris Smith, "bisa gudunmuwarsu wajen samun nasarar wannan aikin."
Ya ƙara da cewa da shi da wasu ƴanmajalisar ƴan jam'iyyar mabambanta sun ziyarci Najeriya, "inda muka gane wa idonmu halin ƙuncin da Kiristoci ke fuskanta, da rashin ƙoƙarin gwamnatin ƙasar wajen magance matsalar," in ji shi.
Ya ce sun gana da mutane da dama, daga ɓangarori da dama, "inda muka samu nasarar tattara bayanai masu muhimmanci kan muzgunawar da Kiristoci ke fuskanta, sannan mun zayyana hanyoyin da za a bi samun nasara."
Ya ce idan aka ɗabbbaƙa matakan da suka bayar da shawarwari a ɗauka, za a samu nasarar daƙile ayyukan mahara masu iƙirarin jihadi, "sannan mun tsara hanyoyin da za mu yi aiki tare da gwamnatin Najeriya domin samar da tsaro ga dukkan ƴan Najeriya."
"Ƴanuwanmu Kiristoci sun daɗe suna shan wahala a Najeriya, amma suka yi gum. Amma yanzu duniya na kallo, kuma ina kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi amfani da wannan damar wajen faɗaɗa haɗaka da gwamnatin Amurka," in ji shi.
Ya ce hakan ne zai taimaka wajen samun nasara, "domin dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen magance matsalolin tsaro da kawo ƙarshen muzgunawa Kiristoci," in ji shi a sanarwar











