Tura sojojin Amurka Najeriya: Me hakan ke nufi ga tsaron ƙasar?

Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 7

Cibiyar sojin Amurka a Afirka wato Africom ta tabbatar da aika wasu sojoji zuwa Najeriya domin taimakon ƙasar a yaƙin da take yi da matsalolin tsaro, inda ta ce sun tura wasu sojoji "ƙalilan".

Shugaban sojojin na Amurka a nahiyar, Janar Dagvin Anderson ne ya tabbatar da tura sojojin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Hafsan sojan na Amurka ya ce tura sojojin na cikin yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka ƙulla, inda aka amince akwai buƙatar haɗaka domin magance matsalar da Najeriya ke fuskanta.

"Wannan ya sa an samu ƙarin haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu, ciki har da tura wasu sojojin Amurka ƙalilan domin taya sojojin Najeriya aiki," in ji Anderson.

Sai dai bai yi cikakken bayani kan adadin sojojin ba, yaushe suka isa Najeriya da kuma haƙiƙanin aikin da za su yi a ƙasar.

Wannan kuma ɗoriya ne kan kan hare-haren da Amurka ta ƙaddamar a wasu maɓoyar Lakurawa a jihar Sokoto a ranar Kirsimetin shekarar 2025.

A wata tattaunawa da BBC, ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa ya tabbatar da cewa Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da Amurka domin kawo ƙarshen rashin tsaro a ƙasar.

Amma wata majiyar tsaro daga Amurka ta shaida wa Reuters cewa sojojin na Amurka za su taimaka wa dakarun Najeriya ne wajen tattara bayanan sirri.

Janar ɗin ya ce Amurka ta tura sojojin ne da amincewar Najeriya, inda ya ƙara da cewa ƙasashen biyu sun amince da matakin.

Amurka dai na ci gaba da matsa wa Najeriya lamba kan yaƙi da ta'addanci, musamman tun bayan da Trump ya zargi ƙasar da rashin kataɓus wajen daƙile abin da ya kira muzgunawa da kuma kisan da ake yi wa Kiristoci a arewacin Najeriya.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta daɗe tana musanta zargin kisan kiristoci a ƙasar, inda ta nanata cewa kashe-kashen da ake yi a ƙasar yana shafar dukkan addinai da ƙabilun ƙasar.

Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka ƙasar

Ministan tsaron Najeriya Christopher Musa

Asalin hoton, FB/Gen CG Musa

Bayanan hoto, Ministan tsaron Najeriya Christopher Musa

A tattaunawarsa da BBC, Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar da zuwan sojojin na Amurka.

Ya ce sojojin na Amurka za su taimaka wa sojojin Najeriya wajen tattara bayanan sirri da horo.

Ya ce sojojin Amurka za su "kasance tawaga ce ta horaswa ce ga dakarunmu domin aiki".

Sai dai Musa bai yi cikakken bayani ba kan yadda haɗakar za ta kasance da kuma yadda za su yi aiki tare da Amurkar ba.

Najeriya ta ƙara haɗin gwiwa da Amurka ne a daidai lokacin da take fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, ciki har da hare-haren ƴanbindiga da sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa da sauran su.

Harin Amurka a Najeriya

A ranar 25 ga watan Disamba ne Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta ƙaddamar da abin da ya kira da wani mummunan hari kan mayaƙan da ya ce ƴan IS ne a arewa maso yammacin Najeriya.

Cibiyar sojin Amurka a Afirka daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto, sannan daga baya aka tsinci ɓurɓushin bam a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya.

Trump ya ce "a ƙarƙashin shugabancina, ƙasarmu ba za ta bar masu tsattsauran ra'ayin Musulunci suna gawurta ba."

Ma'aikatar tsaron Amurka ta wallafa wani gajeren bidiyo da ke nuna wani harin makami mai linzami da aka harbo daga wani jirgin ruwan soji.

Tun bayan harin ne kuma, gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙara ƙarfafa alaƙar tsaro da Amurka.

Me ya sa Trump ke nuna damuwa kan rashin tsaro a Najeriya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A shekarar da ta gabata ce ɗan majalisar dokokin ƙasar Amurka, Sanata ted Cruz ya zargi gwamnatin Najeriya da bari ana yi wa Kiristoci "kisan kiyashi".

Sanata Ted Cruz dai ya gabatar da ƙudirin ne a gaban majalisar dattawan Amurka a watan Satumban bara, inda ya yi zarge-zargen tare da kira da gwamnatin ƙasarsa ta ɗauki mataki.

A ranar Talata ta 8 ga watan Oktoban ne kuma Ted Cruz ɗin ya wallafa a shafinsa na X cewa ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi a Najeriyar sun kashe Kiristoci 50,000 daga shekarar 2009 kawo lokacin a faɗin ƙasar, sannan sun lalata makarantun mabiya addinin Kiristan 2,000 da coci 18,000.

Shi ne sai Ted Cruz ya nemi majalisar dokokin Amurkar ta ƙaƙaba wa jami'an gwamnatin Najeriya waɗanda ya zarga da "kawar da kai da ma wani lokacin taimakon masu ɓarnar, takunkumai.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen na Sanata Ted Cruz, inda ta ce ƙungiyoyin da suke yin hare-haren suna harar ƴan Najeriya ba tare da bambanci ba, sannan ta kuma amince da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar amma ta ce ana samun ci gaba.

Daga baya Trump ya saka baki kan lamarin, inda ya ce ko dai Najeriya ta ɗauki mataki, ko kuma ya ɗauki mataki da kansa.

Ana cikin tattauna barazanar ta Trump ne, sai kwatsam shugaban na Amurka ya sanar da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar.

Matakan da Najeriya ta ɗauka

Bayan kai-komon da aka yi ne gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan rashin tsaro a ƙasar tare da bayar da umarnin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki.

Lamarin ya biyo bayan sace ɗalibai da dama da ƙaddamar da wasu hare-hare da ƴanbindiga suka yi a ƙasar.

Hari mafi muni da ya faru shi ne wanda ƴanbindiga suka kai ranar 21 ga watan Nuwamba inda suka sace ɗalibai da malamai kimanin 300 a makarantar St Mary's Catholic School da ke jihar Neja.

Lamarin ya auku ne bayan wasu ƴanbindigar sun yi garkuwa da ƴanmata 25 daga makarantar gwamnati ta mata da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yamma.

Haka kuma an ci gaba da samun rahoton kai hare-hare, ciki har da wasu mutum 36 a jihar Neja a ranar 26 ga watan Nuwamba da wasu a Sokoto da kuma wanda aka yi a jihar Kogi a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Yawancin waɗanda aka sace dai an kuɓutar da su zuwa yanzu, inda tuni suka koma cikin iyalansu.

Amma dai duk da haka Najeriya ta tura tawaga ta musamman a ƙarƙashin mai ba shugaba ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu zuwa Amurka domin fayyace yadda lamarin yake.

Daga baya ma Amurka ta tura wakilanta zuwa Najeriya, domin jin bahasi, inda aka ƙarshe ƙasashen biyu suka amince za su yi aiki a tare, sannan suka kafa kwamitin haɗaka da ya ƙunshi mambobi daga ƙasashen biyu.

Me haken ke nufi?

A game da abin da tura sojojin Amurka zuwa Najeriya, mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Abdullahi Bakoji Adamu ya ce za a iya samun taimakon, amma ba zai magance matsalar baki ɗaya ba.

Ya ce, "tabbas a wata fuska za mu iya zuwan sojojin zai iya kawo ci gaba, amma ba maganin matsalar ba baki ɗaya ba."

Ya ce za su iya taimakon Najeriya wajen tattara bayanan sirri da samun horon zamani, saboda a cewarsa Amurka tana da horewa wajen amfani da fasaha kamar jirage marasa matuƙa wajen bin sahun ƴan ta'adda zuwa cikin daji.

"Sannan za su taimaka wajen inganta haɗin gwiwa musamman a tsakanin ƙasashen yankin Sahel," in ji shi.

Sai dai ya ce ƙalubale babba, "domin baƙin sojoji ba su san ƙasar sosai ba, kuma ba su san yanayin al'ummar ƙasar ba. Sannan kuma ita matsalar tsaron Najeriya ta wuce maganar bindiga, ta shafi al'adu da ƙabilanci da talauci da siyasa."

Ya ce idan aka yi la'akari da yanayin rikice-rikicen Najeriya, dogaro da sojojin waje bai iya barin baya da ƙura.

"Sannan zai iya jawo wa Najeriya raini a idon ƙasashen duniya, da ma ƴanbindigar, domin za su iya lafawa, amma da zarar sojojin wajen sun tafi, su koma gidan jiya," in ji masanin tsaron.

Bakoji Adamu ya ce babban abin da zai fi tasiri wajen magance matsalolin tsaron Najeriya shi ne inganta aikin sojan ƙasar, inda ya ce akwai buƙatar a inganta musu kayan aiki da inganta jin daɗinsu da kuma hukunta waɗanda suka aikata laifi.

"Sannan uwa-uba dole a koma tushe, matuƙar ana so a magance matsalar, dole a magance talauci da jahilci, sannan a tabbatar da adalci a dukkan ɓangarorin."

A game da tsaron iyaka, masanin tsaron ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin Sahel, musamman wajen haɗin gwiwa da raba bayanan sirri.

A nasa ɓangare, Group Captain Sadik Shehu mai ritaya, wanda mai bincike ne kan lamuran tsaro a Najeriya, ya ce bai kamata Najeriya ta amince da irin wannan matakin ba, ba tare da sanar da al'ummar ƙasar ba.

Haka kuma ya kamata ya yi ƴan Najeriya su samu labarin zuwan sojojin na Amurka daga gwamnatin ƙasarsu, "amma a riƙa samun labari daga Amurka cewa sojojinta sun shiga, ai dole mutane su yi tunanin tursawa aka yi ko ba haka ba ne."

Ya ce akwai tasirin da sojojin za su iya yi, saboda "maganar gaskiya sojojinmu sun yi ƙaranci, wanda kuma sojojin Amurka idan har da gaske suke yi za su taimaka. Ka ga sojojin Amurka suna da na'urar tauraron ɗan'adam za su iya hango ƴanbindiga ko sauran ɓatagari a lungu da saƙo."

Ya ce ko a baya lokacin da ake tsaka da yaƙi da Boko Haram, Amurka ta taimaka wa Najeriya da irin wannan fasahar, amma daga baya ta dakata bayan an samu wani kuskure.