Yadda aka gano asibitocin da ke yaɗa wa yara cutar HIV - Binciken BBC

- Marubuci, Ghazal Abbasi, Seamus Mirodan and Mohammad Zubair Khan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye
- Aiko rahoto daga, Punjab, Pakistan
- Lokacin karatu: Minti 9
Gargaɗi: Wannan labarin na ƙunshe da bayanan da za su iya tayar da hankalin mai karatu
Mohammed Amin ya rasu yana da shekara takwas, jim kadan bayan gwaji ya nuna cewa yana ɗauke da cutar HIV mai karya garkuwar jiki.
Ya riƙa yin zazzaɓi mai zafi da muni inda a wani lokaci yakan so ya kwanta a cikin ruwan sama, yana cikin ''tsananin uƙuba tamkar wanda aka jefa a kaskon suya," in ji mahaifiyarsa, Sughra.
Kwanaki kaɗan bayan ɗan'uwanta ya kamu da cutar, ita ma Asma an gano cewa tana ɗauke da cutar ta HIV.
Iyalansu sun yi amannar cewa sun samu cutar ne bayan an yi amfani da allurar da aka yi wa wasu amfani da ita, sa'ilin da suka je duba lafiya a wata asibitin gwamnati da ke garin Taunsa, a lardin Punjab na ƙasar Pakistan.
Su na daga cikin yara 331 da sashen binciken ƙwaƙwaf na Africa Eye ta gano cewa suna ɗauke da cutar HIV a birnin tsakanin watan Nuwamban 2024 zuwa Oktoban 2025.
Tun bayan da wani likita a wata asibiti mai zaman kanta ya alaƙanta asibitin mai suna THQ Taunsa da yawaitar kamuwa da cutar a ƙarshen shekarar 2024, gwamnatin yankin ta sha alwashin yin bincike, sannna aka dakatar da babban likitan asibitin a watan Maris na 2025.
Sai dai wani bincike na BBC Eye ya gano cewa an ci gaba da yi wa fiye da mutum ɗaya amfani da allura ɗaya har tsawon watanni bayan batun ya tashi.
A lokacin da muka kwashe tsawon sa'o'i 32 muna ɗaukar bidiyo a asibitin THQ Taunsa ta hanyar yin ɓadda-bami, mun gano yadda ake amfani da sirinjin allura ɗaya wa yara da dama har sau 10, wanda akwai yiwuwar hakan ya gurɓata maganin allurar.
A lokuta hudu kuma mun ga yadda aka yi amfani da ruwan magani daga kwalba ɗaya aka yi wa yara daban-daban allura.
Ba mu da masaniya kan ko wani daga cikin yaran na ɗauke da cutar HIV, to amma irin hakan na da haɗarin yaɗa cutar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ko da ma sun canza allurar, amma suka yi amfani da sirinji ɗaya, sirinjin na ɗauke da ƙwayar cutar, saboda haka nan za a iya yada cutar ta sabuwar allurar," in ji Dr Altaf Ahmed, babban masanin ƙananan halittu kuma ɗaya daga cikin manyan ƙwararru kan cutuka masu yaɗuwa a Pakistan, bayan kallon bidiyon.
Duk da bayanin da aka manna a bango cewar ana amfani bin dokokin da suka dace wajen yin allura - mun ɗauki bidiyon ma'aikatan asibitin, ciki har da likita - suna yi wa yara allura ba tare da amfani da safar hannu ta kariya ba har sau 66, kuma wani masani ya bayyana mana cewa abin da muka gani shi ne irin ,matsalar da ake fama da ita a bangaren yin allura a fadin ƙasar Pakistan.
Mun kuma ga yadda wata malamar jinya ke tsoma hannu cikin kwandon sharar asibiti ba tare da safar hannu ba. "Tana karya duk wata doka ƙa'idar yin allura," in ji Ahmed.
Amma a lokacin da muka nuna wa sabon shugaban asibitin Dr Qasim Buzdar, bidiyon da muka ɗauka, ya ki amincewa bidiyon na gaskiya ne.
Ya yi iƙirarin cewar yana iya yiwuwa an ɗauki bidiyon ne kafin ya kama aiki ko kuma "ƙila an haɗa bidiyon ne", sannan ya dage kai da fata cewa asibitin na da aminci ga yara.

Dr Gul Qaisrani, likita a wani asibiti mai zaman kanshi a yankin, shi ne na farko da ya fara gane cewa an samu ɓarkewar cutar HIV a yankin a ƙarshe-ƙarshen 2024, inda ya gano cewa akwai yara da yawa waɗanda aka kai su asbintin da yake aiki suna ɗauke da cutar HIV.
Kusan dukkanin yara 65 zuwa 70 da ya gano cewa suna ɗauke da HIV sun taɓa zuwa neman lafiya a asibitin THQ Taunsa, in ji shi.
Ya tuno cewa akwai wata mata da ta faɗa masa cewa an yi wa ƙaramar yarinyata allura da sirinji ɗaya da wata yarinya daga cikin danginsu mai ɗauke da HIV, sannan an yi amfani da sirinjin ga wasu yaran da yawa.
Qaisrani ya ce wani mahaifi ya taɓa faɗa masa cewa ya ƙalubalanci yadda ake amfani da sirinji ɗaya ga yara da yawa a asibitin na THQ Taunsa, sai dai malaman jinya ba su kula shi ba.
Sashen BBC Eye ya haɗa alƙaluma daga shirin tantance masu cutar HIV na lardin Punjab, da asibitoci masu zaman kansu da kuma wasu alƙaluma da da suka fito daga ƴansanda waɗanda suka bayyana yara 331 da aka yi wa gwaji aka gano suna ɗauke da cutar HIV a garin Taunsa tsakanin Nuwamban 2024 zuwa Oktoban 2025.
Daga cikin yara 97 na yaran da aka gane suna ɗauke da cutar HIV, waɗanda kuma aka yi wa iyayensu gwaji, iyaye huɗ ne kacal aka samu suna ɗauke da cutar.
Wannan ya nuna cewa ƙalilan ne cikin waɗannan yara suka samu cutar daga iyayensu a lokacin haihuwa.
Mahaifiyar Mohammed Amin da Asma, wato Sughra, ba ta ɗauke da cutar – mijinta kuma ya rasu shekara biyu da suka gabata sanadiyyar haɗarin mota.
Sakamakon binciken da hukumomin lardin suka yi ya nuna cewa "sirinjin da ya guraɓata da cuta" na daga cikin hanyar da fiye da rabin yara 331 suka kamu da cutar, ciki har da Asma – sauran kuma ba a bayyana hanyar da suka samu cutar ba.
Gwamnatin lardin Punjab ta shiga lamarin a watan Maris ɗin 2025, lokacin da ta ce yawan yaran da suka kamu sun kai 106. An salami shugaban likitocin asibitin THQ Taunsa Dr Tayyab Farooq Chandio, amma BBC Eye ya gano cewa ya ci gaba da aiki na tsawon wata uku a wani asibitin ƙauye.

Ya bayyana wa BBC Eye cewa ya ɗauki mataki ''nan take'' bayan da aka sanar da shi game da yawan kamuwa da cutar HIV a asibitin THQ Taunsa, amma y ace ba asibitin ne sanadiyyar yaɗuwar cutar ba.
An maye gurbin Chandio da Buzdar, wanda ya shaida wa BBC cewa ya mayar da hankali sosai kan batun HIV bayan karɓar aiki a watan Maris ɗin 2025 kuma kuma "bay a lamuntar" Rashin ɗaukar matakan kariya.
"Mun gudanar da shirye-shiryen bayar da horo ga malaman lafiya da ma'aikata a kan yadda za a daƙile yaɗuwa da kuma kawar da cutar HIV.
Akwai kuma wani sashenmu mai muhimmanci kan kare kamuwa da cuta. An yi wa jami'an sashen horo a ɓangaren," in ji shi.
Sai dai binciken BBC Eye ya gano ana gudanar da ayyukan babu kariya a watanni takwas bayan haka.

Bidiyon da muka ɗauka a watan Nuwamba da Disamban 2025, wanda aka ɗauka a tsawon makonni ya nuna yadda ake barin kwalbar magani a buɗe tare da sirinjin allura waɗanda aka yi amfani da su a kan teburi, a maimakon a ajiye su a wurin da cut aba za ta iya shiga ba.
Yawancin yaran da muka ga ana kula da su a asibitin THQ Taunsa ana yi musu allura ne ta hanyar allurer da akan saƙala a cikin jijiya – wanda hakan ke ƙara haɗarin kamuwa da cuta. Ta hanyar tura magani kai-tsaye zuwa cikin jijiya, hakan zai bai wa ƙwayoyin cuta damar zille wa garkuwar jiki.
Mun kuma ɗauki bidiyon wata malamar jinya wadda ta ɗauko wani sirinji daga ƙasar teburi wanda yake ɗauke da sauran maganin da aka yi wa wani yaron na daban. A maimakon ta jefa shi cikin kwandon shara sai ta miƙa wa abokiyar aikinta, wanda ahakn ke nufin za a yi amfani da shi ga wani yaron na daban.
Lokacin da muka nun awa Buzdar bidiyon da muka ɗauka sai ya dage kai da fata cewa an ɗauki bidiyon ne kafin yak ama aiki ko kuma kawai an shirya bidiyon ne.

Lokacin da aka tambaye shi me zai faɗa wa iyayen yaran da ke zaune a yankin waɗanda za su kalli bidiyon, sai y ace "zan faɗa musu cewa su zo neman lafiya a asibitin THQ Taunsa."
A wata sanarwa, gwamnatin yankin ta ce "babu wata cikakkiyar shaida ta ƙararru" da ta "tabbatar cewa THQ Taunsa ne asibitin da ya zama silar" ɓarkewar cutar.
Sanarwar ta ƙara da cewa akwai wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin asusun kula da yar ana Unicef da hukumar lafiya ta duniya da kuma sashen sashen kula da lafiya na yankin ya nuna cewa "rashin dokokin kula da asibitoci masu zaman kansu" da "amfani da jinin da ba a tantance ba" na daga cikin sila.
Sai dai wani rahoton Shirin na shekarar 2025 wanda BBC ta gani game da ɓarkewar cutar, ya gano matsaloli da dama irin waɗanda BBC ta gano a binciken da ta yi a asibitin THQ Taunsa.
"Akwai damuwa, musamman a ɓangaren kula da lafiyar yara," in ji rahoton – yana cikin sassan da BBC ta ɗauko bidiyonsu.
"Babu wasu kayan da ake buƙata na kula da lafiyar yara kuma ana yin allura babu ɗaukar matakan kariya.
Ana sake amfani da kayan ƙarin ruwa, ba a sanya lamba a kan alluran da ake saƙala wa yara a jijiya sannan ana barin kayan ƙarin ruwa da aka gama amfani da su a kan tebura. Ba a bin dokokin tsaftace hannu – bahunan wanke hannu sun toshe sannan babu sinadaran tsaftace hannu.


A shekarar 2019, ɗaruruwan yara a garin Ratodero na lardin Sindh ne aka gano cewa suna ɗauke da HIV bayan yin gwaji, kuma mafi yawansu iyayensu ba su ɗauke da cutar.
Likitan yara a yankin, Dr Imran Arbani ya shaida wa BBC cewa ya gano cewa da dama daga cikinsu sun ziyarci wasu asibitocin kuma an yi musu allurai da dama, "saboda haka akwai yiwuwar an saka musu cutar ne a lokacin yi musu magani".
Ya zuwa 2021, yawan yaran yankin da ke fama da cutar HIV ya kai 1,500 - kuma har yanzu ana samun ƙaruwar yara masu kamuwa.
Yayin da muke ɗaukar bidiyo a asibitin Taunsa, an gano dandazon wasu da suka kamu da cutar a Karachi. A yankin garin SITE, yaran da aka yi wa magani a asibitin Kulsoom Bai Valika, daga baya an gano suna ɗauke da cutar HIV.
Mikasha, ƴar shekara biyu na cikin su.

Wani daga cikin iyalin yarinyar ya shaida wa BBC Eye cewa jami'an asibitin sun yi amfani da sirinji ɗaya wajen yi wa yara da dama allura: "sukan cika sirinjin da magani su yi wa yaro allura, sai su sake cika sirinjin su yi wa wani yaron na daban allura".
Shugaban likitocin asibitin Dr Mumtaz Shaikh ya faɗa a cikin tattaunawar da aka yi da shi cewa "ƙwararrun likitoci ba za su taɓa amfani da sirinji ɗaya wajen yi wa yara da dama allura ba, saboda haka ba mu da irin haka a asibitocin gwamnati".
Sai dai ministan lafiya na tarayya ya tabbatar cewa ɓarkewar cutar da aka samu tsakanin mutum 84 ta faru ne sanadiyyar yin amfani da sirinji ɗaya kan mutane daban-daban a asibitin.

Tsangwamar da ke tattare da cutar HIV na nufin cewa maƙwafta za su iya hana yaransu wasa da Asma, abin da zai sa ta zama cikin kaɗaici yayin da kuma take fama da rashin lafiya, kamar yadda iyalanta suka bayyana. Takan tambayi mahaifiyarta: "Mece ce matsalar da ke damu na?"
Tsaye a kusa da kabarin ɗan'uwanta da ya rasu, Asma ta ce tana kewar shi. "Yana wurin Allah a yanzu."
Ta bayyana wa BBC cewa tana yin karatu tuƙuru a makaranta.
Ta ce "idan na girma ina so na zama likita."









