Trump ya yi barazanar sake kai hare-hare a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta iya sake kaddamar da hare-hare a Najeriya idan har a cewarsa aka ci gaba da kisan Kiristoci.
Mista Trump ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Jaridar New York Times da aka wallafa a ranar Alhamis.
Gwamnatin Najeriya ta sha musanta ikirarin danganta kashe-kashen ƙasar da kisan Kiristoci kawai.
A cikin hirar da aka yi da Donald Trump, ya ce ya so ya kai hari ɗaya amma a cewarsa idan aka ci gaba da kisan kiristoci, Amurka za ta sake ƙaddamar da wasu hare-hare a Najeriya.
Ya kuma ce harin ranar Kirsimeti da Amurka ta kai a Najeriya na hadin guiwa ne da hukumomin ƙasar.
Sannan da aka yi masa batun da mai ba shi shawara kan harakokin Afrika kan tsokacinsa cewa ƴanta'adda sun fi kisan musulmi fiye da kiristoci a Najeriya, sai trump ya amsa cewa ya yarda ana kisan musulmi a hare-haren na Najeriya amma a cewarsa an fi kisan kiritoci.
A karshen watan Oktoba ne Trump ya fara gargadin cewa kiristoci na fuskantar barazana tare da yi gargadin zai kai wa Najeriya hari kan abin da ya kira gamnati ta gaza wajen kare kiristoci, zargin da gwamnatin Najeriya ta musunta, tana mai cewa rikicin kasar ya shafi dukkanin bangarorin addini na ƙasar ba tare da fifita wani addini ba.
Harin farko da Amurka ta kai Najeriya
A ranar 25 ga watan Disamba ne Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta ƙaddamar da abin da ya kira da wani mummunan hari kan mayaƙan da ya ce ƴan IS ne a arewa maso yammacin Najeriya.
Cibiyar sojin Amurka a Afirka daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto, sannan daga baya aka tsinci ɓurɓushin bam a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya.
Trump ya ce "a ƙarƙashin shugabancina, ƙasarmu ba za ta bar masu tsattsauran ra'ayin Musulunci sun gawurta ba."
Ma'aikatar tsaron Amurka ta wallafa wani gajeren bidiyo da ke nuna wani harin makami mai linzami da aka harbo daga wani jirgin ruwan soji.
Tun bayan harin ne kuma, gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙara ƙarfafa alaƙar tsaro da Amurka.
Ta ya zargin kisan Kiristoci a Najeriya ya faro?
Tun da farko, ɗan majalisar dokokin ƙasar Amurka, Sanata ted Cruz ne ya zargi gwamnatin Najeriya da bari ana yi wa Kiristoci "kisan kiyashi".
Sanata Ted Cruz dai ya gabatar da ƙudirin ne a gaban majalisar dattawan Amurka a watan Satumba, inda ya yi zarge-zargen.
A ranar Talata ta 8 ga watan Oktoban ne kuma Ted Cruz ɗin ya wallafa a shafinsa na X cewa ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi a Najeriyar sun kashe Kiristoci 50,000 daga shekarar 2009 kawo yanzu a faɗin ƙasar, sannan sun lalata makarantun mabiya addinin Kiristan 2,000 da coci 18,000.
Shi ne sai Ted Cruz ya nemi majalisar dokokin Amurkar ta ƙaƙaba wa jami'an gwamnatin Najeriya waɗanda ya zarga da "kawar da kai da ma wani lokacin taimakon masu ɓarnar, takunkumai.
Wane martani gwamnatin Najeriya ta mayar?
Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen na Sanata Ted Cruz, inda ta ce ƙungiyoyn da suke yin hare-haren suna harar ƴan Najeriya ba tare da banbanci ba, sannan ta kuma amince da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar amma ta ce ana samun ci gaba.
Gwamnatin ta kuma musanta zargin cewa ba sa yin komai wajen hana kisan Kiristocin.
Ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙari wajen ƙoƙarin fattakar ƙungiyoyin ƴanta'adda a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyin ƴanƙasar, kuma ana ganin sakamakon hakan.
Daga baya Trump ya saka baki kan lamarin, inda ya ce ko dai Najeriya ta ɗauki mataki, ko kuma ya ɗauki mataki da kansa.
Ana cikin tattauna barazanar ta Trump ne, sai kwatsam shugaban na Amurka ya sanar da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar.











