Me ya sa Elon Musk ke son gina birni a duniyar wata?

A wani rubutu a shafin X, Elon Musk ya yi bayanin abin da ya sa ya canja inda yake son gina gari SpaceX daga duniyar Mars zuwa duniyar wata

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A wani rubutu a shafin X, Elon Musk ya yi bayanin abin da ya sa ya canja inda yake son gina gari daga duniyar Mars zuwa duniyar wata
    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wani gagarumin birni ne da Elon Musk ya ƙuduri aniyar ginawa, kuma yake da burin kammalawa nan da shekara 10.

Shugaban kamfanin na X da Tesla da SpaceX, wanda kuma shi ne wanda ya fi kowa arziki a duniya ya bayyana a wani rubutu da ya yi a X, wanda sama da mutum miliyan 40 suka karanta cewa SpaceX ya canja tsari daga gina birnin a duniyar Mars zuwa duniyar wata.

Amma me ya sa ya canja shawara? kuma me ya kamata mu sani kan birnin da yake son ginawa?

Duniyar wata maimakon ta Mars

Har yanzu babu wani cikakken bayani kan yadda ginin zai kasance, kawai har yanzu wani buri ne da Musk yake da shi da ya fara bayyanawa a kafar X.

Ya bayyana burinsa na assasa wani gari da mutane za su iya zama su yi rayuwa a cikinsa.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Musk ya ce zai cika burinsa "a ƙasa da shekara 10, maimakon duniyar Mars da zai ci shekara 20."

Ya ƙara da cewa za a iya zuwa duniyar Mars ne "a duk lokacin da duniyoyi suka yi daidai, wanda kan faru bayan wata 26 (kimanin tafiyar wata shida)."

Sai dai ya ce a ɗaya ɓangaren, "za mu iya zuwa duniyar wata duk bayan kwana 10."

Babban burin kamfanin na SpaceX shi ne assasa birni a duniyar Mars, sannan "za a iya farawa nan da shekara biyar zuwa bakwai," in ji shi. "Amma babban burin shi ne ƙara inganta hanyoyin samar da cigaba, kuma duniyar wata ta fi (alamun haka)."

Masu bibiyar Musk tuni suka fara ƙirƙirar yadda birnin zai kasance a duniyar, inda wasu suke amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta kamfanin Musk, Grok wajen tsara yadda suke tunanin duniyar za ta kasance.

Burin na Musk ya ƙara samun tagomashi ne bayan ya yi daidai da wani bincike da mujallar Wall Street Journal ta wallafa a farkon wannan watan, inda a ciki aka ce kamfanin zai fi mayar da hankali kan zuwa duniyar wata, sannan daga bisani ya koma shirin zuwa duniyar Mars.

Wannan wani babban canji ne daga daɗaɗɗen burin kamfanin SpaceX na zuwa duniyar Mars, inda ko a bara, ya nanata burinsa na zuwa duniyar Mars zuwa ƙarshen shekarar 2026.

Yadda za a cika burin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Sungwoo Lim, babban masanin harkokin sama jannati a Jami'ar Surrey da ke Birtaniya ya bayyana burin gina birnin a duniyar wata a matsayin "gagarumin abu," amma ba "zuƙi ta malle ba."

"Za a yi amfani da ƙasar da ke cikin wata domin samar da iskar da ake buƙata domin numfashi da ruwa da kayan gina. Don haka a taƙaice za a iya aiwatarwa," in ji shi a tattaunawarsa da BBC.

Ƙalubalen kuma shi ko za a iya amfani da waɗannan a yanayin cikin duniyar ta wata mai yanayin tsananin zafi da ƙura da rashin isasshen makamaki.

Ya ce hukumomin gwamnati da suke da burin zuwa duniyar wata suna bi a hankali ne saboda da kuɗin gwamnati suke amfani, ga kuma siyasa da ke hana wasu abubuwan tafiya da sauri, amma SpaceX, in ji shi, "yana aiki ta hanyoyi daban."

"Idan sabuwar rokar da suke haɗawa ta yi aiki yadda ake so, za ta iya fara kai kayan aiki zuwa wata kuma a farashi mai rahusa cikin sauri, wanda zai sa abubuwan ya yi sauri."

Shi ma Dr Ugur Guven, darakta a cibiyar nazarin sararin samaniya da makamashi a Jami'ar GD Goenka da ke India ya ce duniyar wata ta fi sauƙin mu'amala ga mutane.

"Idan an samu matsala, cikin sauƙi za a iya tura wasu su kai ɗauki cikin gaggawa," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa daga duniyar da mutane suke ciki ta Earth zuwa wata "na kai kwana biyu zuwa uku."

Sai dai duk da haka, Dr Lim ya ce gina birnin a duniyar wata, "aiki ne ja aka ɗauko."

"Noma abinci ba tare da kai sinadaran da ƙasa ke buƙata domin duniyar Earth da kuma samar da yanayi da za a iya amfani da abubuwa da sake amfani da su na cikin abubuwan da suke da wahala. Amma duk da cewa aiki ne ja, za a iya aiwatar a hankali a hankali."

Shi ma Clive Neal, farfesan tsare gine-gine da da kimiyyar duniya a Jami'ar Notre Dame da ke Indiana a Amurka ya ce, "sai mun yi nazari tare da tabbatar da duk abin da ake buƙata kafin za mu tabbatar da yiwuwar abin da ake so," in ji shi.

Dr Lim ya ce ya yi amannar cewa akwai ɗan ƙarmin waje da ke duniyar wata da zai iya samar da iskar da ake buƙata domin numfashi, wanda kuma zai iya samar da ruwa nan da shekara 10.

Rububin tafiya duniyar wata

First full moon of 2026

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Amurka da China na rige-rigen tura mutane zuwa duniyar wata

Musk ya yi wannan bayanin ne a daidai lokacin da Amurka da China ke rige-rigen sake tura mutane zuwa duniyar wata. Tun Apollo 17 da hukumar ta aika duniyar wata a shekarar 1972, ba a sake samun nasarar zuwa.

A kwanakin baya ne kamfanin SpaceX ya sanar da mallakar ƙirƙirarriyar basira mai suna xAI, wadda darajar kamfanin da kadarorinsa irin su rokoki da tauraron ɗan'adam ta kai dala tiriliyan 1, sannan ƙirƙirarriyar basirar ta kai dala biliyan 250.

Haka kuma sanarwar za ta iya taimakon burinsa na assasa cibiyoyin tattara bayanai da alƙaluma a duniyar wata, kamar yadda Michelle Fleury na BBC ya bayyana a New York.

A watan jiya ne Musk ya sanar da shirye-shiryensa na kafa miliyoyin cibiyoyin tattara alƙaluma da bayanai a sararin samaniya.

Amma masana sun ce akwai saurin aiki a gaba, inda suka yi nuni da rashin isasshiyar iskar sanyaya kayan aiki, wanda kume dole sai da su ƙirƙirarriyar basirar za ta yi aiki da kyau.