Wane taimako Rasha da China za su bai wa Iran idan ta fara yaƙi da Amurka?

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images)
- Marubuci, سعید جعفری
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, روزنامهنگار
- Lokacin karatu: Minti 6
A duk lokacin da Iran da Amurka suka nunawa juna yatsa, babbar tambaya ita ce:
Wane mataki China da Rasha za su ɗauka idan musayar yawu ta rikiɗe zuwa yaƙi?
Shin Iran za ta iya dogara da ƙasashen biyu masu ƙarfi ko kuwa ƙawancen da ke tsakanin Iran da waɗannan ƙasashe biyu taron dangi?
Amsar waɗannan tambayoyi ta dogara ga irin dangantakar da ke tsakanin Iran da Moscow da kuma Beijing.
Masana dangantakar ƙasashe sun bayyana ƙawance a matsayin ƙulla yarjejeniyar tsaro yayin da aka kai wa ɓangare guda hari.
Babu irin wannan yarjejeniya tsakanin Tehran da waɗannan ƙasashe masu ƙarfi.
Wata yarjejeniya da aka ƙulla tsakanin Tehran da Moscow a watan Janairun shekara ta 2024 duk da ta ƙunshi batun tsaro da haɗin kai a ciki amma babu batun kai taimakon sojoji yayin da aka kai wa wani ɓangare hari.
Hamidreza Azizi, masanin alaƙar ƙasashe ya shaida wa Sashen Farsi na BBC cewa ƙawancen soji shi ne ƙololuwar dangantaka tsakanin ƙasashe, sannan babu wannan a tsakanin Iran da China da kuma Rasha.
''Yayi imanin cewa ko a lokacin yaƙi zai yi wuya Moscow da Beijing su kaiwa Iran wata muhimmiyar gudummawa. Za su iya bayar da gudunmawarsu amma a matakin diflomasiyya.

Asalin hoton, AFP via Getty Images)
Nahiya: Me ya sa taimakon zai yi wahala?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani abun la'akari shi ne yanki ko nahiya abubuwan dubawa ne; Chaina da Rasha na da kyakkyawar alaƙa a Gabas ta Tsakiya.
Beijing babbar abokiyar hulɗar tattalin arziƙi ce ga Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Isra'ila.
Moscow na hulɗa kai tsaye da Tehran da Tel Aviv da kuma wasu ƙasashen Larabawa.
Shiga yaƙi kai tsaye tare da Iran zai iya zama ƙalubale cikin wannan haɗaka.
Dukkan ƙasashen masu ƙarfi na gasa da Amurka. Rasha na yaƙi da Ukraine don haka sojojinta da siyasarta a takure suke.
Ita ma Chaina ta mayar da hankali wajen gasa da Amurka musamman a gabashin yankin Asiya da kuma batun Taiwan.
Don haka buɗe babin sabon rikici a Gabas ta Tsakiya ko da kai tsaye ne ba zai hafar musu da ɗa mai ido ba.
Yulia Roknifard farfesa a jami'ar Taylor da ke Malaysia ta shaidawa BBC cewa ''Rasha da China za su iya kallon wannan sabon lamari a matsayin damar da zasu yi amfani da ita wajen goyon bayan abokin hulɗar da ya fi muhimmanci a tsakaninsu, Iran memba ce a ƙungiyar BRICS kuma memba a ƙungiyar Shanghai Cooperation Organization don haka Moscow da Beijing ba za su zuba ido a lalata ɗaya daga cikin membobinsu ba."

Asalin hoton, AFP via Getty Images)
Yaƙin ''kwanaki 12'' da iyakokinsa
Misali guda da za a iya bayarwa zai bada hoton matsayin Chaina da Rasha lokacin da Jamhuriyar Musulunci ta fuskanci barazana daga waje.
A sake duba kwanaki goma 12 na yaƙin Iran da Isra'ila a lokacin tsakanin Moscow da Beijing ba wanda ya taimakawa Jamhuriyar Musulunci sai a matakin siyasa. Babu wani taimakon soji daga ƙasashen biyu.
Kodayake ita ma Iran ta dage cewar ba ta nemi taimakon ƙasashen biyu ba.
Bayan yaƙin kakakin Dakarun Juyin Juya Halin Iran IRGC ya sanar cikin watan Nuwamban shekara ta 2025 cewar:
''Babu wata yarjejeniyar da aka ƙulla da waɗannan ƙasashe biyu a matakin sojoji sannan babu buƙatar neman taimako."
Hamidreza Azizi ya yi imani tasirin ƙasashen biyu membobi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya abun dubawa ne a rikicin.
Kafafen Yaɗa Labarai da suka haɗa da CNN da mujallar Financial Times sun fidda rahoto a shekarar da ta gabata inda suke ce ganau daga Hukumar Tattara Bayanan Ƙasashen Yamma sun bayyana yadda Chaina ta aika da man da jiragen yaƙi zasu yi amfani da shi Iran.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Chaina ta mayar da martani inda ta ce bata da masaniya game da wannan labari sannan ta yi watsi da abinda ta kira ''zargi maras tushe," ta kuma ƙara da cewar sinadarin sodium perchlorate ba shi da wata ƙa'ida a Chaina kuma fidda shi ba laifi ba ne a ƙasar.
Mista Azizi ya yi imanin idan rikicin ya yi tsanani akwai yiwuwar a samu taƙaitaccen samun bayanan sirri ko taimakon na'urori ba tare da Chaina da Rasha sun shiga yaƙi kai tsaye da Amurka ba.
Yulia Roknifard ta yi imanin Rasha da Chaina ba sa buƙatar sanar da taimakon da suke baiwa Iran a fili kamar yadda Iran ta ɓoye irin taimakon da ta baiwa Rasha a farkon yaƙi da Ukraine.

Asalin hoton, Iranian Army Office/AFP via Getty Images)
Fargabar sauyin gwamnati?
Wasu masu sharhi na ganin sauyin gwamnati a Iran zai sauya tunanin Moscow da Beijing.
Iran dai memba ce a Ƙungiyar BRICS da Shanghai Cooperation Organization don haka tana da muhimmanci a tsakiyar Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya.
Daga wannan mahanga za a fahimci rusa siyasar Tehran zai haifarwa Moscow da Beijing komabaya a yunƙurinsu na ƙarawa kansu ƙarfi.
Yulia Roknifard ta ce rusa gwamnatin Musulunci da samar da sabuwar gwamnati mai goyon bayan Amurka barazana ce ga Rasha da Chaina
Sai dai masu sanya ido na ganin koda an kafa sabuwar gwamnati, ba zasu bayar da taimakon soji ba amma zasu iya taimakawa tattalin arziƙi da bayanan sirri da kuma makamai.
Amma shigar su yaƙi kai tsaye zai yi wahala.
Tattalin arziƙi: Abin da Iran ta fi buƙata
Ƙarfin tattalin arziƙi zai iya sa gwamnati ta jure a Tehran ya yin da karyewar tattalin arziƙi zai haifar da tarzoma.
A wannan gaɓa ne kuma Chaina zata taka muhimmiyar rawa kodaye abubuwan da suka faru a shekarun baya bayan nan sun sa Beijing na taka tsan tsan.
Sabbin rahotannin sun bayyana yadda Beijing ta rage siyan man Iran a watannin baya bayan nan.
Ƙididdiga daga kamfanonin mai ta nuna a baya Chaina na sayen mai daga Iran da ya kai ganga miliyan 1.4 kowacce rana a shekarar da ta gabataa, amma a yanzu ta na sayen ganganr mai kusan 800,000 zuwa 900,000 kowacce rana a makonnin baya bayan nan.
Komabayan ya biyo bayan takunkumin da Amurka ta sanyawa harkar fito. Lamarin da zai iya hana Iran samun isassun kuɗaɗen shiga idan rikicin ya yi tsanani.
A baya bayan nan Rasha ma ta nuna haɗin kan da ta ke baiwa Iran na wucin gadi ne. Daga cibiyar makamashi ta Bushehr da isar da na'urorin kare kai daga farmaki, an ga yadda Rasha ta ke jinkirtawa tare da sanya siyasa a al'amarin.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
'Akwai taimako amma ban da lokacin yaƙi'
Gabaɗaya akwai yiwuwar idan rikici ya rincaɓe ko kuma taƙaitaccen rikici ya ɓarke tsakanin Iran da Amurka, China da Rasha zasu bi tsari ɗaya: Adawar diflomasiyya da Washington da yunƙurin kwantar da rikicin da kuma wataƙila bayar da hadin kai a bayanan sirri da Tehran.
Amma shiga yaƙin kai tsaye zai yi wahala idan aka yi la'akari da abinda ya faru a baya.
Yulia Roknifard ta ƙara da cewa : "A yanzu babban burin Chaina da Rasha shi ne aikawa da saƙonnin da zasu dakatar da Amurka jibge dakaru a yankin."
Hamidreza Azizi ya ce idan yaƙi ya ɓarke, kar a yi tsammanin Chaina ko Rasha zasu taimakwa Iran da sojoji.
A taƙaice abinda ke tsakanin Tehran da Moscow da kuma Beijin ya fi ƙarfin haɗin kan tsaro, wani haɗin kai ne da aka ƙirƙira sakamakon matsin lambar ƙasashen ƴamma










