Bayanin da Melania Trump ta yi kan binciken Epstein ya dawo da hannun agogo baya
- Marubuci, Nada Tawfik
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, New York correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da Melania Trump ke tattaki zuwa teburin gabatar da bayani a White House a ranar Alhamis, daidai wajen da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar bayani kan Iran a makonnin da suka gabata, babu wata alama da ke nuna mutane sun ƙadu da ganin nata.
Akwai matsuwa da buƙatar jin abin da za ta faɗa, amma babu wanda ya yi hasashen abin da aka ji. Har mutanen da suke cikin gwamnatinsu ba su san maudu'in da za ta yi magana a kai ba, kamar yadda wasu jami'an suka bayyana.
Tsaye a gefenta hagu da dama da tutar Amurka, kalamanta na farko sun girgiza kowanne mutum da suka shiga kunnensa. "Ƙaryar da ake yi ake haɗa ni da watsattsen mara mutuncin nan Jeffrey Epstein ya kamata ta zo ƙarshe a yau."
Da waɗannan kalmomi, matsalar badaƙalar Epstein da ta jefa shugaban ƙasar cikin rikici a baya, ta ƙara dawowa sabuwa da abin da matarsa ta yi.
Cikin gaggawa gidan talabijin na Amurka suka katse shirin da suke yi kan Iran, suka koma haska abin da ke faruwa a White House.
Matar shugaban ƙasar ba ta fiye son tsoma baki cikin al'amuran saboda ba mai son hayaniya ba ce, a nutse take zaɓar bukukuwan da za ta je. Yana da matuƙar wuya ka ganta na wani sa-in-sa da manema labarai kamar mijinta.
Ta ce ba ta taɓa haɗa alaƙa da da Epstein ko Maxwell ba, kamar yadda ta riƙa karantawa daga rubutaccen bayin da ta zo da shi, kuma na Epstein ba ne ya haɗa ta da mijinta, kuma ita ba ta san komai ba cikin muggan laifukan da Jeffrey Epstein ya aikata ba.
Ta kuma ƙare bayanin nata da kira ga mjalisar ƙasar ta saurari waɗanda suka tsira daga hannun Epstein domin ƙara bankaɗo gaskiyar da har yanzu ba a sani ba.
Da a ce ta tsaya amsa tambayoyin 'yan jarida, da tambayar farko da za a mata za ta kasance ne, me yasa sai yanzu kika ji ya kamata ki fito ki yi bayani, kwatsama kamar daga sama? ta yi hakan ne domin nisanta kanta da waɗanda aka ce an yi lalata da su.
Ana ta raɗe-raɗin cewa wani kan-da-garki ne ta yi domin ana sa ran wasu sabbin bayanan da za su fito masu alaƙa da Epstein, sai ta fake da cewa tun tuni ta yi bayani duk mai son ji daga gareta ya tuntubi lauyanta.
'Yar jaridar nan Vicky Ward mai binciken kwakwaf, wadda ta yi ta kawo rahotanni kan Epstein na gwamman shekaru, ta ce yadda aka yi taron manema labaran a yaznu ya matuƙar haifar da ruɗani.
"Da a ce Melania Trump ta yi haka tun lokacin da aka fara batun Epstein shekara guda baya, ta yi kira a yi bincike da watakila tunanin da za mu yi ya sha banban da wanda muke yi yanzu."
Yadda ta yi bayanin bai yi ma'ana ba, kamar yadda Vicky ta ce. "Babu wasu abubuwa masu alaƙa da Melania Trump da yawa a cikin binciken Epstein, baya ga wani saƙon email ɗaya, wani email na abota ga Ghislaine Maxwell. Hakan ya rikita ni. Ba na tsammanin akwai wanda zai yarda cewa itama abin ya shafe ta.
Mijinta shugaba Trump ya ƙara yamutsa abin da cewa shi bai ma san za ta yi magana kan batun ba, duk da cewa kakakin matar tasa tun da fari ya ce Trump ya san za ta yi.

Asalin hoton, Reuters
Cikin gaggawa aka riƙa samun ce-ce-ku-ce kan sanarwar ta Melania.
Waɗanda suka tsira sun riƙa waya tsakaninsu, suna tattaunawa kan mafimtarsu da abin da yake faruwa, suka fara shirya yadda za su mayar da martani kan lamarin.
Sha uku daga cikinsu, tare da iyalan Roberts Giuffre, sun fitar da sanarwar cewa ƙara yi wa waɗanda suka tsira tambayoyin tamkar karkatar da idon mutane ne daga gare ki, rashin adalci ne hakan.
"Mai ɗakin shugaban Amurka Melania na neman kawar da idanun mutane daga kanta ta mayar da zargin kan waɗanda suka tsira daga Epstein, ta shiga rigar siyasa domin kare ikon da take da shi: da sashen shari'a da na tabbatar da doka waɗanda har ya zuwa yanzu ba su gama sakin bayanan Epstein duka ba.

Asalin hoton, US Department of Justice
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Phillips wadda ta tattauna da BBC Radio 4 ta ce kiran waɗanda suka tsira su bayar da labaransu abu ne mai kyau. Sai dai ta ƙalubalanci mai ɗakin shugaban ƙasar da ta tabbatar da ta aikata abinda ta fada.
"Abin da zan yi shi ne zan kira ta na tambaye ta, me za ki iya yi kan hakan? me za ki ki taimaka mana? Me za ki yi ki ciyar da wannan maganar gaba?
Shugaban kwamitin da yake lura da binciken kan Epstein, ya shaida wa Fox News a ranar Juma'a dama suna da shirin tattaunawa da wadanda suka tsallake rijiya da baya lokacin da za su kammala bincikensu na kwamiti.
"Na yarda da abin da matar shugaban ƙasa ta faɗa kuma na yi farin ciki da shi," James Corner na jam'iyyar Republican ya shaida. "Za mu saurare su".
Barry Levine, marubucin littafin the Spider: Tangled Web of Jeffrey Epstein and Ghislaine Maxwell, ya ce fitarwa Melania ta yi wannan maganar, nuna wa ta yi ba ta tare da mijinta.
Ya ce ko da yaushe Trump yana yi wa waɗanda lamarin ya rutsa da su kallon hadarin kaji.
Tammy Vigil marubuciyar Melania and Michelle, First Ladies in a New Era, ta shaida wa BBC cewa rashin bayyana sunan mijinta a bayanin da ta yi ya nuna wata gagarumar barakar da ake da ita a White House da kuma manufar da kowa ya sa a gaba.
"A zahiri tana so ta nuna matsayarta wadda a boye kuma ta sha banban da abin da ta bayyana.
Dan haka akwai muradinta na ƙashin kanta da take son sawa a gaba. Bayani ne na raɗin kanta don munga ta yi irinsa a baya.".
Jam'iyyar Democrats na ganin wannan abu a matsayin wata kyauta a siyasance.
Melania Trump yanzu haka ta sanya kanta dumu-dumu cikin labarin Epstein haka zalika ta dawo da hannun a gogo baya a bincike da ake ganin kamar an ɗauki gangara a cikinsa.
Shugaba Trump da ya yi mu'amala da Epstein a shekarun 1990 wanda kuma ya fito a bincike da ake yi a gurare da dama ya musanta yana da laifi, ya bayyana duk abubuwan da binciken Epstein ya bayyana a matsayin siyasa.
Amma a wannan karon ba zai iya zargin wadda ta dawo da hannun a gogo baya ba a wannan lamari, balle ya bayyana wata niyya da take bayan sanarwar da ta yi.













