Yadda aka haifi jariri da mahaifar matar da ta mutu

Asalin hoton, PA Media
- Marubuci, Philippa Roxby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter
- Lokacin karatu: Minti 4
An haifi wani jariri, wanda ya zamo na farko a Birtaniya da aka haifa ta amfani da mahaifar da aka ciro daga matar da ta mutu aka dasa a jikin wata mai rai.
Uwar jinjirin, Grace Bell, wadda aka haifa ba tare da mahaifar da za ta iya ɗaukar ciki ba, ta ce jinjirin nata mai suna Hugo, wanda yanzu yake da sati 10 da haihuwa "ɗan baiwa ne."
Grace da abokin zaman ta Steve Powell da ke zaune a yankin Kent na Birtaniya, sun yaba da "tausayi da ƙaunar" da wadda ta bayar da gudunmawar mahaifar ta nuna, sannan kuma sun yaba wa likitocin da suka yi ɗawainiyar aikin dashen a asibitocin da ke birnin London da kuma Oxford.
Likitocin da suka gudanar da aikin sun ce wannan "lokaci ne mai matuƙar muhimmanci", wanda zai bai wa sauran mata masu fama da lalurar rashin mahaifa fatan samun waraka.
'Gagarumar kyauta'
An haifi Hugo ne kwanaki kaɗan gabanin bikin kirsimetin shekara ta 2025 a asibitin Queen Charlotte and Chelsea da ke yammacin birnin Landan.
Mahaifiyar Grace Bell ta kasance ba ta yin al'adar mata ta wata-wata, sai dai tana yin ƙwai a cikinta, kasancewar an haife ta ne da mahaifa wadda ba ta iya ɗaukar jariri.
Ana kiran wannan lalurar MRKH, wadda take shafar mutum ɗaya cikin 5,000 na mata a Birtaniya.
A lokacin da ta kai shekara 16 ne aka tabbatar mata cewa ba za ta iya haihuwa ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hanya ɗaya da ita, da mijinta za su iya bi domin samun haihuwa shi ne yin dashen mahaifa, ko kuma su bi tsarin dakon ciki.
Lokacin da aka fada mata cewa an samu wadda za ta ba ta gudumawar mahaifa, kuma aka tabbatar mata cewa za a iya yin aiki domin dasa mata mahaifar, ta yi murna sosai, sannan ta cika da mamaki.
Ta ce "A kullum nakan tuna matar da ta ba ni gudumawar mahaifar da iyalinta, kuma ina musu addua'ar samun kwanciyar hankali a rayuwa sanadiyyar wannan gagarumar kyauta da ta ba ni.
"Akwai wani ɓari na jikinta da zai rayu a jikina har abada."
An kwashe awa 10 ana tiyatar dasa wa Grace mahaifar a asibitin Churchill da ke Oxford a watan Yunin 2024, sannan daga baya aka yi musu dashen ɗan tayi a asibitin masu neman haihuwa na The Lister Fertility Clinic da ke London.
Lokacin da aka haifi Hugo, Grace ta ce: "wannan baiwa ce kawai.
"Na tuna lokacin da na buɗe ido da safe na ga ƴar ƙaramar fuskarsa, sai na ji abin kamar a mafarki.
"Abin ba a cewa komai."

Asalin hoton, Womb Transplant UK/PA Wire
Cire mahaifar da aka yi daga mamaciyar da ta bayar da gudumawa da kuma dasa ta a jikin Grace ya ɗauki tsawon awa 10, wanda aka yi a matsayin ɗaya daga cikin tiyatar gwaji.
An yi wa wasu matan uku irin wannan dashe, amma wannan ne karo na farko da aka haifi jariri bayan dashen.
A farkon shekara ta 2025 aka haifi jaririya ta farko daga matar da aka yi wa dashen mahaifa daga wata mace mai rai.
Mahaifiyar jaririyar ta samu gudumawara mahaifa ne daga ƴar'uwarta a watan Janairun 2023. Ƴar'uwar tata ta ba ta gudumarwar mahaifar ce bayan ita ta haifi yara biyu.
Yanzu haka ana sa ran yi wa mata biyar tiyatar dashen mahaifa, wadanda suka samu mahaifar daga ƴan'uwansu.
Labari mai daɗi ga matan da aka haifa babu mahaifa
Yara biyu da aka haifa bayan dashen mahaifa, Hugo da Amy, duk an haife su ne a asibiti ɗaya da ke birnin London.
Likitocin da suka yi ayyukan guda biyu duk sun dade suna shirya wa irin wannan lokaci.
Babban likitan mata Farfesa Richard Smith na gidauniyar Imperial College Healthcare NHS Trust, ne ya fara bincike kan yadda za a yi dashen mahaifa sama da shekara 25 da suka gabata, kuma yana nan a lokacin da aka haifi Hugo.
Ya ce "an haɗa mutane sosai" a wajen gudanar da aikin - tun daga lokacin dashen mahaifar zuwa hada ɗan tayi a waje da kuma dasa shi a cikin mahaifa.
Grace da abokin zaman ta sun nuna godiyarsu ga Farfesa Richard Smith, wanda kuma shi ne ya kafa ƙungiyar dashen mahaifa ta Birtaniya, inda suka sanya wa ɗan nasu laƙabin Ricahrd.
Ma'auratan za su iya samun ɗa na biyu idan suna so, amma bayan nan za a cire mahaifar.
Za a cire mahaifar ne domin Grace ta huta da shan magunguna, waɗanda idan ba a cire mahaifar ba dole ne ta ci gaba da shan maganin har ƙarshen rayuwarta domin hana garkuwar jiki yaƙar mahaifar da aka dasa mata.

Likitar dashe kuma wadda ta jagoranci tiyatar, Isabel Quiroga ta ce "ta yi farin ciki" da haihuwar Hugo, sannan ta bayyana lamarin da wata babbar nasara a harkar dashen gaɓa a Birtaniya.
Farfesa Smith ya ce haihuwar za ta bai wa yara mata da aka faɗa musu cewa ba su da mahaifa, fatan cewa za su iya ɗaukar ciki kuma su haifi yaransu da kansu.
Jaririn da aka haifa daga mahaifar da aka samu daga matar da ta mutu zai zamo ba ya da wata alaƙa da mai asalin mahaifar dangane da ƙwayoyin halitta.
An yi tiyatar dashen mahaifa sama da 100 a faɗin duniya, kuma an haifi yara sama da 70 bayan dashen.
Sai dai dashen mahaifa ba kamar dashen sauran gaɓoɓin jikin ɗan'adam ba ne kamar ƙoda ko zuciya - ana yi ne kawai idan an samu buƙatar neman yin hakan ta musamman daga iyalin wadanda za su bayar da gudumawar mahaifar ga ƴan'uwansu.
A Birtaniya, ana ɗaukar kowa a matsayin wanda ya amince ya bayar da gudumawar gaɓar jikinsa, sai dai idan mutum ya nuna cewa ba ya son yin hakan.
Iyalin matar da ta bai wa Grace gudumawar mahaifa, waɗanda ba su son a bayyana su, sun ce "suna matuƙar alfahari" da aikin alheri da ƴarsu ta yi.
An yi amfani da gaɓoɓinta wajen yin dashe ga mutane huɗu.










