Me harin Lakurawa kan ayayin jagoran rundunar soji ke nufi ga tsaron ƙasar?

HQ Nigerian Army

Asalin hoton, HQ Nigerian Army

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairu ne ayarin sojojin da suke raka babban hafsan rundunar sojin ƙasan Najeriya ta 8 suka gwabza faɗa domin tsira daga harin ƙwanton ɓauna da Lakurawa ta kitsa musu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar Latfanal kanal Olaniyu Osoba ya fitar, ya ce ƴan Lakurawa sun ɗana tarkon ne domin neman ayarin sojojin su faɗa, amma jami'ansu suka samu nasarar fatattakar su.

Sai dai duk da wannan nasarar da sojojin suka samu, masu bibiyar harkokin tsaro da sharhi, irin su Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon security and consulting, suna ganin barazana ce babba.

Ya ce akwai tashin hankali idan ya kasance ƴanbindiga sun samu ƙarfin gwiwar tunkarar hafsan soji da ayarinsa da niyyar cimmasa, maimakon neman hanyar tserewa idan sun hango shi, ko kuma suka ji yana kan hanya.

Yadda aka yi gumurzun

A sanarwar da rundunar sojin ƙasan Najeriya ta fitar, ta ce lamarin ya auku ne a kusa da Tsaunin Mayama da ke cikin jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.

"Babban hafsan runduna ta 8 ta sojin ƙasan Najeriya, Manjo Janar Bemgha Koughna ya faɗa wani mummunan tarkon da maharan Lakurawa suka ɗana a Tsaunin Mayama da ke jihar Kebbi a lokacin da ayarin babban sojan ke hanyar zuwa ziyartar sojojinsa," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ayarin sojojin suna cikin tafiya suka ji an buɗe musu wuta na kan mai uwa da wabi.

"Amma sai hafsan da sojojinsa suka nuna bajinta, inda suka yi musayar wuta da maharan har suka samu nasarar fatattakar su, tare da kashe mahara biyar a nan take, inda suka samu nasarar ficewa daga tarkon," in ji kakakin rundunar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ayarin sojojin sun samu nasarar fatattakar maharan, sannan suka lalata manufarsu, "wanda ƴar manuniya ce ga sauran ƴanbindigar da ke addabar yankin baki ɗaya."

Osoba ya ce bayan samun nasarar fatattakar maharan, sojojin sun kutsa domin neman maharan tare da samun ƙwato makamai da sauran kayayyakin tattara bayanan sirri.

Daga cikin makaman da sanarwar ta ce sun ƙato akwai bindiga ƙirar OJC da bindiga ƙirar PKT da bindiga ƙirar AK-47 da sunduƙan harsasan AK-47 guda huɗu da kuɗi kimanin naira 840,000 da wayoyin salula da babura guda biyar.

"Yanzu haka akwai sojoji a yankin suna ci gaba da sintiri domin hana maharan sakat, ballanta su samu natsuwar sake ƙaddamar da harin irin wannan," a cewar sanarwar.

...

Asalin hoton, X/NigerianArmy

'Babbar barazana ce ga tsaro'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dokta Kabiru Adamu, Shugaban kamfanin Beacon Security and consulting, wanda ke nazarin al'amuran tsaro a Najeriya da yankin Sahel, ya ce hafsa irin GOC ba daidai yake da ɗaiɗaikun mutane ba.

"Babbar barazana ce ga tsaron Najeriya a ce hafsa babba irin GOC, da irin sojojin da yake tafiya da su da irin makaman da yake tafiya da su na kariya a ce an kai masa hari," in ji shi.

Ya ce GOC babban hafsa, "wanda a matakin aikin soja ya kai ƙololuwa, sannan yana tafiya ne tare da rakiyar dakaru da manyan kayan aiki, amma duk da haka, ƴanbindiga su iya kai masa hari, gaskiya abu ne na tayar da hankali."

Ya ce irin wannan harin zai sa waswasi a zuciyar sauran ƴan ƙasa da suke neman kariya daga sojoji.

Masanin tsaron ya ce wani babban abin tashin hankali shi ne lura da inda aka kai harin ba cikin ƙungurmin daji ba ne.

"Wurin bai da yanayi na daji, wuri ne da ake iya hangowa daga nesa. Bayanan da suka fito sun nuna cewa sun dasa bama-bamai ne a ƙasa, wataƙila da nufin da zarar ayarin sun faɗa cikin tarkon, bama-baman su tashi, sai su fito su far musu da harbe-harbe, duk da ba su samu nasara ba," in ji Kabiru Adamu.

Shugaban kamfanin na Beacon ya ce da a ce akwai hanyoyin tattara bayanan sirri, "da za a hango ko gano lokacin da ake dasa bama-baman, sannan da za a iya bibiya a kama wanda ya dasa bama-baman."

Ya ce akwai tayar da hankali, "sannan kuma ya nuna raunin ɓangaren tsaron Najeriya. Ya kamata a ce ana iya tattara bayanan sirri ne, sannan ana iya hango abubuwa daga nesa."

Birgediya Janar Musa Uba

Uba Musa

Asalin hoton, Amaq/X

A watan Nuwamban shekarar 2025 ne mayaƙan Iswap suka kai harin ƙwanton ɓauna kan ayarin sojojin Najeriya, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Musa Uba.

Lamarin ya tayar da ƙura, inda ake ganin an watsa wa gwamnatin Najeriya ƙasa a ido ne a ce mahara za su iya kama babban soja irin shi.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce mutuwar janar ɗin "ta kaɗa" shi.

A harin wanda mayaƙan Iswap suka kai a ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamban, sun yi wa Musa Uba ƙanton ɓaune, amma sojoji suka ce ya tsira, kafin daga bisani labari ya fito cewa mayaƙan sun tafi da shi.