Ko barazanar Amurka kan Najeriya ce ke ta'azzara rashin tsaro a ƙasar?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan rashin tsaro a ƙasar tare da bayar da umarnin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki bayan sace ɗalibai sama da 300 a wani kome na ayyukan ƴan bindiga a tsakiyar watan Nuwamba a fadin arewa maso yammacin ƙasar.
Hari mafi muni da ya faru shi ne wanda ƴan bindiga suka kai ranar 21 ga watan Nuwamba inda suka sace ɗalibai da malamai kimanin 300 a makarantar St Mary's Catholic School da ke jihar Neja.
Akwai mutane aƙalla 50 da suka kuɓuta, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sai dai har yanzu sauran na hannun ƴan fashin daji.
Hakan na zuwa ne kwana hudu bayan wasu ƴan bindigar sun yi garkuwa da ƴanmata 25 daga makarantar gwamnati ta mata da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi.
Ɗalibai biyu suka tsere daga hannun ƴan bindigar yayin da aka sako guda 23 a ranar 25 ga watan Nuwamba, inda gwamnati ta ce ta tattauna ne da ƴan bindigar.
A ranar 24 ga watan Nuwamba kuma jami'an tsaro sun ceto mutum 39 wadanda aka sace daga cocin Christ Apostolic a jihar Kwara, ranar 18 ga watan Nuwamba.
Sai dai an ci gaba da samun rahoton kai hare-hare, ciki har da wasu mutum 36 a jihar Neja a ranar 26 ga watan Nuwamba da wasu a Sokoto da kuma wanda aka yi a jihar Kogi a ranar 30 ga watan Nuwamba.
Waɗannan hare-hare na zuwa ne bayan zargin da Donald Trump ya yi na cewa Kiristoci na fuskantar muzgunawa a Najeriya, wani abu da ya sanya ya ayyana ƙasar a matsayin wadda "ake da damuwa a kanta" sanadiyyar take hakkin yin addini.
A ranar 1 ga watan Nuwamba, Trump ya yi gargadin cewa Amurka a shirye take ta ɗauki matakin soji kan Najeriya domin kare Kiristoci da ke cikin ƙasar.
Gwamnatin Najeriya ta ce wannan matsala na shafar Musulmai da Kiristocin ƙasar, inda ta sha musanta zarge-zargen.
Su wane ne ƴan bindigar da ke addabar Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matsalar da ta fara a wajen shekarar 2011, kuma ta ci gaba da ƙazancewa tun wajen 2014, ƴan bindiga sun watsu a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sokoto da Neja da kuma Kebbi, a arewa maso yammacin Najeriya.
Ƴan bindigar na gudanar da ayyukansu ne a dazukan da babu alamar gwamnati a yankin, inda suke satar shanu, da fashi da makami, da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da fyaɗe da yi wa al'umma fashin kaya da kuma kashe-kashe.
A wasu wuraren sukan ƙaƙaba wa mazauna haraji.
Abin da ke iza wutar ta'asar da suke tafkawa shi ne safarar ƙananan makamai a yankin, musamman daga yankin Sahel mai maƙwaftaka.
Maƙasudin ayyukan ƴan bindiga shi ne domin su azurta kansu, ba domin siyasa ko aƙida ba. Suna ayyukansu ne ba tare da wani tsayayyen shugabanci guda ɗaya ba, amma suna da wasu da suka yi ƙaurin suna a cikinsu.
Daga cikin irin wadannan jagororin daba da suka yi ƙaurin suna akwai Dogo Gide da Ado Aleru, wadanda ke gudanar da ayyukansu a yankin jihar Zamfara.
Akwai kuma Bello Turji, wanda hare-harensa suka karaɗe yankunan Zamfara da Sokoto.
Gwamnati ta ayyana ayyukan ƴan bindiga a matsayin na ta'addanci a watan Janairun 2022, wanda hakan ya sanya su sahu daya da mayaƙan Boko Haram da Iswap da ke yaki a arewa maso gabas, kusa da tafkin Chadi.
A shekarun baya-bayan nan an samu rahotannin ƴan bindiga suna hada kai da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ko kuma amfani da irin kalamansu.
Gwamnatin Najeriya na amfani ne da ƙarfin soji wajen yaƙi da gungun na ƴan bindiga, inda ta samar da sansanonin soji a yankin, tana ƙaddamar da farmaki ta ƙasa da sama, tana kama wasu daga cikinsu.
Ayyukan sojojin sun tarwatsa wasu daga cikin gungun ƴan bindigar, inda wasu suka watsu zuwa yamma, zuwa jihar Kwara, wasu kuma kudu zuwa jihar Kogi yayin da wasu suka yi wasu yankunan.
Gwamnatocin jihohi kan tallafa wa ayyukan sojoji, amma kuma wasu daga cikinsu sun yi sulhu da ƴan bindigar domin samun sauƙin matsalar wadda ta kashe dubban mutane da tarwatsa wasu dubban.
Shin kalaman Trump ne ke ta’azzara rashin tsaro a Najeriya?

Asalin hoton, EPA
Sake kazancewar garkuwa da mutane a arewacin Najeriya na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tura sojoji Najeriyar domin yaki da abin da ya kira kisan kiyashi kan Kiristoci, to amma akwai wahala a iya alakanta kalaman nasa kai tsaye da sace-sacen mutane da suka dawo na baya-bayan nan.
A baya, Najeriya ta fuskanci jerin sace-sacen al’umma, musamman daga farkon watan Disamban 2020.
A watan Yunin 2021 ‘yan bindiga sun kai hari kan Makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a jihar Kebbi, inda suka sace akalla dalibai 90 da malamai biyar.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa ya zuwa watan Yunin 2021 an sace akalla dalibai 1,000 bayan kazancewar matsalar hare-hare kan makarantu.
To sai dai kafafen yada labarai da manyan jami’an gwamnatin kasar sun alakanta sake dawowar wadannan hare-hare kan makarantu da kalaman Donald Trump na barazanar daukar matakin soji kan kasar.
A ranar 17 ga watan Nuwamba, Sakataren gwamnatin tarayyar kasar, George Akume ya ce kalaman shugaban na Amurka sun taimaka ta wani fannin wajen karuwar hare-haren yan bindiga.
“Kalaman da suka fito daga Amurka a baya-bayan nan sun karfafa wa kungiyoyin masu tayar da hankali gwiwa, wadanda ke son su yi amfani da zarge-zargen kasashen waje domin sake nuna kansu, ta hanyar kai hari a wurare masu sauki,” in ji shi.
Duk da cewa harin da aka kai kan coci a Kwara da sace dalibai a wata makaranta a jihar Neja abubuwa ne da za a iya alakantawa da addini, ‘yanbindiga kan farmaki taron mutane da makarantu kasancewar za su samu kudin fansa mai gwabi domin ci gaba da ayyukansu.
Kafafen yada labarai a cikin gida sun ce akan sace dalibai ne kasancewar iyaye za su biya kudin fansa cikin sauki, sannan kuma a baya coci-coci kan tattara kudi domin biyan kudin mutanensu da aka yi garkuwa da su.
Wadanne matakai gwamnati ta dauka?
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan matsalar tsaro a Najeriya a ranar 26 ga watan Nuwamba sannan ya bayar da umarnin daukar karin sojoji da jami’an ‘yansanda 20,000.
Ya ce za a janye jami’an tsaro da ke bayar da tsaro ga manyan mutane sannan a ba su horo domin tura su wuraren da ake fama da kalubalen tsaro.
Haka nan kuma Tinubu ya amince da kafa kwamitin tsaro na hadaka tsakanin Amurka da Najeriya.
Bugu da kari, jami’an Najeriya da na Amurka sun tattauna kan yadda za su habbaka hadin gwiwa a harkar tsaro da bunkasa zaman lafiya a yankin arewaci da tsakiyar kasar. A ranar 21 ga watan Nuwamba, Amurka ta yi tayin tallafawa wajen bincike kan sace-sacen daliban ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani, bayan samun bukatar hakan daga Najeriya.
A ranar 26 ga watan Nuwamba sanatocin Najeriya sun kada kuri’a domin bai wa fararen hula ‘yancin mallakar bindiga domin kare kai.
‘Yansanda sun daina bayar da lasisin amfani da kananan bindigogi a watan Agustan 2023 sanadiyyar yaduwar makamai barkatai ba bisa ka’ida ba.
Haka nan sanatocin sun kada kuri’ar ayyana garkuwa da mutane a matsayin aikin ta’addanci tare da yin gyara ga dokar ta’addanci domin zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin hakan.
Shugaban kasar ya kuma bayar da umarnin sake nazarin dokokin kafa ‘yansandan jihohi sannan ya bukaci kananan hukumomi su duba yiwuwar sake bude makarantun kwana da aka rufe.











