Me ya sa ake fara shekara da sunan gunkin Janairu?

Asalin hoton, Getty Images
A bisa al'ada, duk shekara a lokaci irin wannan mutanen duniya suna murnar shiga sabuwar shekara.
A irin wannan lokaci, jama'a a ɓangarori da dama na duniya na bukukuwan sabuwar shekara ta hanyar wasa da tartsatsin wuta da kaɗe-kaɗe da kuma rungumar juna don nuna farin ciki.
Kafin mu shiga batun bukukuwa da raye-raye, ko ka taɓa tunanin mene ne ya sa aka ayyana watan Janairu a matsayin watan farkon shekara?
Dalilin ya samo asali ne lokacin bukukuwan maguzawan Rum.
Sarki Julius Ceaser ne ya ƙaddamar da kalendar sama da shekaru 2,000 da suka gabata.
Tabbas ba zamu manta da Fafaroma Gregory XIII ba.
Gumaka da tatsuniyoyi
Watan Janairu na da muhimmanci ga Romawa na da, domin shi suka keɓe wa suna Janus (watau Janairu kenan a latin).
A cikin tsoffin labaransu, Janus wani gunki ne mai fuska biyu wanda ke nufin farko da ƙarshe da sauyawar lokuta.
''An fi dangantaka shi da abin da ya wuce da wanda zai faru'', in ji farfesa Diana Spencer, ta jami'ar Birmingham da ke Burtaniya.

Asalin hoton, Getty Images
Watan kuma yana zuwa daidai lokacin da wuni ke tsawo a Turai da yanayin sanyin hunturu.
"A wurin al'ummar Romawa, ''yana ɗauke da ma'anoni da dama'', in ji Farfesa Spencer, "saboda bayan waɗannan gajerun kwanaki za a zo lokacin da duniya za ta yi duhu ga sanyi kuma ganyen shuke-shuke zai bushe."
"Lokaci ne na hutawa da waiwayen abubuwan da suka gabata," in ji Misis Spencer.
Yayin da daular Rum ta ƙara karfi sai ta baza kalandar a masarautu da dama.
Kiristanci
Bayan rushewar Daular Rum, sai addinin Kirista ya kafu daga nan sai ɗaya ga watan Janairu ta zama al'adar maguzanci.
Ƙasashen mabiya addinin Kirista da dama sun nemi mayar da ranar bukukuwan sabuwar shekara ya koma 25 ga watan Maris, ranar da suka yi imanin Mala'ika Jibril ya bayyana ga Nana Maryamu (A.S).
''Duk da cewar lokacin Kirsimeti shi ne lokacin da aka haifi Annabi Isa, muhimmin lokaci shi ne yayin da aka shaida wa Nana Maryamu cewa za ta haihu'', kamar yadda Misis spencer ta shaida wa BBC.
"Shi ne lokacin da labarin addinin Kirista ya fara, don haka daga nan ya cancanta a fara lissafin sabuwar shekara'', a cewar ta.
A cikin ƙarni na 16 Fafaroma Gregory XIII ya gabatar da kalendar Gregorian, inda aka sake ayyana ɗaya ga watan Janairu a matsayin wani ɓangare na farkon shekara a ƙasashen mabiya ɗarikar Katolika.

Asalin hoton, Getty Images
To amma Birtaniya wadda ta yi wa Fafaroman tawaye ta hanyar bin tafarkin waɗanda suka bijire, ta ci gaba da bikin sabuwar shekara a ranar 25 ga watan Maris har zuwa shekara ta 1752.
A shekarar ne aka gabatar da wata doka a zauren majalisar Birtaniya wadda ta mayar da ƙasar tsarin da sauran ƙasashen Turai ke bi.
A yau ƙasashe da dama a duniya na bin kalendar Gregorian, shi ne kuma dalilin da yasa ake kunna tartsatsin wuta kowacce ranar 1 ga watann Janairu.










