Me ya sa Najeriya ke cin bashi duk da janye tallafin man fetur?

Tinubu

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

Lokacin karatu: Minti 5

Har yanzu wasu ƴan Najeriya na mamaki kan dalilan da suka sanya gwamnatin ƙasar ta ci gaba da cin bashi daga waje da kuma cikin gida duk kuwa da janye tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

A yayin sanar da janye tallafin man fetur da ya yi a lokacin shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar, ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaba Bola Tinubu ya ce za a karkatar da kuɗaɗen don gudanar da wasu muhimman ayyuka.

Shugaba Tinubu ya koka cewa tallafin man fetur da gwamnati ke biya na janye ɗumbin dukiyar da ya kamata a yi amfani da ita wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa a ƙasar.

To sai dai tun bayan hawansa mulki shekara uku da suka gabata, Shugaba Tinubu ya ci manyan basuka aƙalla takwas.

Wani abu da ya riƙa dasa ayar tambayar cewa ina kuɗin tallafin da gwamnatin ta janye da ta ce zai ishe ta gudanar da wasu muhimman ayyukan?

Masu sukar ciyo bashin musamman na waje na nuni da haɗurran da suka ce na tattare da shi ga makoma da kuma al'ummar ƙasar.

To sai dai jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar ta kare batun, tana mai cewa karɓar basukan wata dabara ce ta samar da kuɗaɗen gudanar da wasu muhimman ayyukan.

Nawa ake bin Najeriya bashi?

Alkaluman ofishin kula da bashi na ƙasar sun nuna cewa zuwa watan Yunin shekarar 2025 da ya gabata abin da ake bin ƙasar matsayin bashi ya haura naira tiriliyan 152.

Kuma Dokta Murtala Abdullahi Ƙwara malami a tsangayar koyar da tattalin arziki ta jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce akwai yiwuwar bashin ya ƙaru, la'akari da giɓin da ke cikin kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar.

''Idan muka duba kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar cikin watan Disamban bara, za mu fahimci cewa akwai giɓin fiye da naira tiriliyan 23, wanda indai an karɓo su to bashin da ake bin ƙasar zai iya ƙaruwa'', in ji shi.

Malamin jami'ar ya kuma ce yawan cin bashi da ƙasar ke yi na daga cikin abubuwan da ke haifar da hauhawar farashin kaya a ƙasar.

Nawa Najeriya ta tara daga cire tallafi?

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

Bayanan hoto, Tinubu ya ce gwamnati za ta yi amfani da tallafin don yin wasu ayyuka
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Ahmed Adamu na Jami'ar Nile da ke Abuja ya ce hukumomin ƙasar ne kawai za su iya tantance adadin kuɗin da aka samu samakon cire tallafin man fetur, saboda ya danganta da yawan kuɗin shigar da ƙasar ta samu, da kuma darajar kuɗin ƙasar.

''Dama shi tallafin mai ana biyansa daga rarar kuɗaɗen mai da ake samu bayan sayar da mai, kuma yawansa ya dangata da tsadar mai a kasuwannin duniya, idan farashin mai ya tashi to za a samu da yawa, idan kuma ya faɗi to yana raguwa'', in ji shi.

Sai dai Dokta Murtala Ƙwara ya ce dama a baya gwamnatin kan ciyo bashi ne domin biyan tallafgin man, ba wai tana da shi ɗauka take yi ta biya ba.

''To don haka wannan bashin na biyan tallafin mai ya kamata a ce ya ragu cikin kuɗaɗen da kasar ke ciyo bashi a yanzu, tunda ta daina biyansa'', in ji shi.

Sai dai kuma watan Yunin 2025 Jaridar Punch ta ambato wani rahoto daga hukumar wayar da kai ta ƙasa NOA, na cewa gwamnatin ƙasar ta samu dala biliyan 84 sakamakon cire tallafin man fetur da ta yi a 2023.

A baya nawa gwamnati ke biyan tallafin?

Farfesa Ahmed Adamu ya ce a baya gwamnatin Najeriya kan biya tallafin mai la'akari da tsadar da man yake yi a kasuwannin duniya

''Abin da ke faruwa a lokacin shi ne idan farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya, to kuɗin da ake biya matsayin tallafin mai na ƙara yawa'', masanain tattalin arzikin man fetur.

A watan Janairun 2023, kamfanin dillancin labarai na Retuers ya ruwaito wasu alƙaluma daga babban kamfanin mai na ƙasar NNPC cewa a shekara 2022, ƙasar ta biya naira tiriliyan 4.39 a matsayin tallafin man fetur.

Farfesa Adamu ya ce idan darajar naira ta faɗi to abin da ake biya a matsayin tallafin mai a lokacin yana ƙara yawa.

Me ake yi da kuɗaɗen?

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

Farfesa Adamu ya ce kuɗaɗen rarar mai idan sun shigo kasafta su ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi.

''Ai tsayawa za a yi ana tara shi ko kallansa idan ya shigo ba, da zarar sun shigo kowane wata ake raba su'', kamar yadda ya bayyana.

Masanin tattalin arzikin ya kuma ce a yanzo kowa ya sani a ƙasar adadin kuɗaɗen da ake raba wa jihohi da ƙananan hukumomi ya ƙara fiye da a baya.

''Alal misala jihohin da a abaya ke samun naira biliyan biyar, yanzu suna samun biliyan 20, saboda ƙarin da aka samu sakamokin cire tallafin na man fetur'', in ji shi.

Sai dai Farfesa Adamu ya ce yanzu gwamnatin tarayya da jihohi ne ya kamata su fito suy bayyana wa duniya abin da suke yi da waɗanan kuɗaɗen da suke samu.

A nata ɓangare gwamnatin Tinubu ta ce ta samar da abubuwan more rayuwa da na rage raɗaɗi ga talakawa da abinci da tallafin taki ga manoma, daga wani ɓangare na kuɗin tallafin na man fetur.

Ko cire tallafi zai iya hana Najeriya cin bashi?

Dangane da ƙorafin da wasu ƴanƙasar ke cewa me ya sa gwamnatin ƙasar ta ci gaba da cin bashi duk da cire tallafin man fetur, Farfesa Adamu ya ce ba haka batun yake ba.

''Ai su dama kuɗin rarar mai idan an same su rabawa ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma ƙananan hukumomi'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa bashin kuwa da gwamnatin tarayya ke karɓowa tana amfani da shi wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda take cewa.

Sai dai ya ce ya kamata gwamnatin Najeriyar ta yi taka tsantsan wajen yawan bashin da take cin.