Ta yaya Donald Trump zai cika 'burinsa' na mallakar Greenland?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Bernd Debusmann Jr
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, at the White House
- Marubuci, Nick Beake & Kayla Epstein
- Lokacin karatu: Minti 6
Donald Trump na son mallakar yankin Greenland - kuma fadar White House ta tabbatar da cewa duka zaɓi da ake da su suna ƙasa na mallakar yankin, ciki har da amfani da ƙarfin soji.
Matakin soji ya kasance wani zaɓi da ake tunanin ɗauka, tun da kamar mambar ƙungiyar Nato ne za ta kai wa ƴar uwarta hari, kuma wannan mataki zai iya janyo ruɗani a cikin ƙawancen, duk da cewa ba mai yiwuwa ba ne.
Trump ya sha nanata cewa Greenland na da muhimmanci ga tsaron Amurka, inda ya yi iƙirari ba tare da hujja ba cewa wurin "na ɗauke da jiragen ruwan Rasha da na China baki ɗaya".
Mun yi duba kan irin matakai da Trump ke tunanin ɗauka don ganin ya mallaki yankin.
Matakin soji
Ƙwararru kan harkar tsaro sun ce idan aka ɗauki matakin soji don mallakar Greenland za a yi shi ne cikin sauki, amma abin da zai biyo bayan yana da girma.
Yawan al'ummar yankin bai fi mutum 58,000 ba, inda kashi ɗaya bisa uku ke zaune a Nuuk, babban birnin yankin, yayin da sauran da yawa ke rayuwa a yammacin yankin.
Greenland ba shi da sojoji na kashin kansa inda Denmark ke da alhakin bai wa yankin tsaro, sai dai sojojinta na sama da kuma na ruwa ba su da isassun kayan aiki.
Jami'ai na musamman ne daga Denmark ke sintiri a faɗin wurare na yankin, inda suka dogara ga karnuka.
Denmark ta ƙara yawan kuɗin da take kashewa a fannin tsaro a bara a yankin Arctic da kuma arewacin Atlantika, ciki har da tsibirin na Greenland.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kasancewar yankin na da faɗi, mai al'umma kaɗan da kuma rashin sojoji zai yi wa Amurka kyau wajen mallaka - Amurkar ta girke jami'an soji kusan 100 a arewa maso yammacin yankin.
Ta daɗe tana burin mallakar Greenland.
Bayan sojojin Nazi na Jamus sun mamaye yankin da ake kira Jutland a Denmark a lokacin yaƙin duniya na biyu, sai Amurka ta shiga Greenland, inda ta kafa sansanin soji da gidajen rediyo a tsibirin.
Bayan yaƙin, dakarun Amurka ba su fice daga yankin ba. Har yanzu Amurka na aiki a sansanin jiragen sama jannati na Pituffik Space Base, wanda a baya ake kira Thule Air Base.
Wani ƙwararre kan tsaro a Denmark, Hans Tito Hansen, ya zayyana yadda matakin soji da Amurka za ta iya ɗauka zai wakana.
A cewar Hansen, wasu sojojin saman Amurka na shiyya ta 11 su za su iya jagorantar yin aikin saboda ƙwarewarsu, tare da taimakon sauran sojojin ruwa da kuma na sama.
Wani sojan wucin-gadi na Birtaniya Justin Crump, wanda ke jagorantar ɓangaren tattara bayanan sirri, ya goyi bayan abin da Hansen ya faɗa.
"Amurka na da ƙarfi a ɓangaren sojin ruwa kuma tana da ikon samar da sojoji da yawa," in ji shi.
Trump ya ƙara da cewa wannan mataki zai kasance ba sani ba sabo, sai dai ba zai samu turjiya mai yawa ba.
Sai dai a can Amurka, tsoffin jami'an tsaro da dama da kuma ƙwararru kan tsaro sun ce da wuya a ɗauki matakin soji, ganin cewa zai yi tasiri kan ƙawancen Amurka da Turai.
"Hakan zai saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa," in ji Mick Mulroy, tsohon mataimakin sakataren tsaro. Ba barazana ba ce ga Amurka kaɗai, har ma ga ƙawayenta."
Idan fadar White House ta fara shirin ɗaukar matakin soji, Mulroy ya ce hakan zai fuskanci turjiya wajen ƴan majalisa waɗanda za su yi amfani da dokar iko kan yaƙi, wadda ta taƙaita ikon shugaban ƙasa shiga yaƙi ba tare da amincewarsu ba, don hana hakan.
"Ba na tunanin akwai ɗan majalisar da zai amince a wargaza ƙawancen Nato," in ji shi.
Sayen Greenland
Amurka na da ɗimbin arziki, sai dai an tabbatar wa ƙasar cewa yankin Greenland ba na sayarwa ba ne.
Kafar yaɗa labarai ta CBS - wadda BBC ke ƙawance da ita Amurka - ta ruwaito cewa sakataren harkokin cikin gidan Amurka Marco Rubio ya faɗa wa ƴan majalisar ƙasar cewa zaɓin gwamnatin Trump shi ne a sayar mata da yankin.
Amma ko da ana son sayar da Greenland, cinikin zai kasance mai sarkakiya.
Dole ne sai majalisa ta amince da kuɗin da za a sayi yankin, sannan mallakarsa ta hanyar yarjejeniya ba zai yiwu ba har sai kashi biyu bisa uku na majalisar dattawa ya goyi baya - wanda ƙwararru suka ce zai yi wuya a samu.
Za a buƙaci ita ma Tarayyar Turai ta saka hannu kan yarjejeniyar.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da Trump zai yi ƙoƙarin cimma yarjejeniya ba tare da shigar da ƴan Greenland ko majalisa ba, ƙwararru na cewa hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Farfesa Monica Hakimi, ƙwararriya kan dokokin ƙasa da ƙasa a Jami’ar Columbia, ta ce "Mutum zai yi tunanin yanayin da za a ce Denmark, Amurka da kuma Greenland sun amince a mayar da yankin zuwa wani ɓangare.
"Amma don ganin ya daidaita da dokokin ƙasa da ƙasa, dole ne sai yarjejeniyar ta shigar da ƴan Greenland a ciki domin amincewarsu," in ji ta.
Ba a dai san hakikanin nawa za a kashe ba wajen sayen yankin. Wannan zai ƙara dagula wa Trump harkoki, wanda ya yi kamfe lokacin yaƙin neman zaɓe cewa komai za a yi to "Amurka ce a farko".
Shirin kashe biliyoyi ko kuma tiriliyoyin daloli na harajin ƴan Amurka wajen sayen tsibirin na Greenland, zai iya janyo ruɗani.
Sai dai sojan Birtaniya Crump na ganin cewa gaza sayen yankin, zai ƙara ingiza Trump ɗaukar matakin soji - musamman ma ga gwamnatin da ke ganin ta samu nasarar kai samame har da garkuwa da shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro.
"Zai iya cewa, kawai za mu ɗauki matakin soji, in ji Crump kan abin da shugaban Amurkar zai iya yi.
Sakataren harkokin cikin gida na Amurka Marco Rubio ya ce Trump "ba shi ne shugaban Amurka na farko da ya nuna sha'awar mallakar Greenland ba".
Ya kwatanta shugabanni irin Harry Truman, wanda ya yi tayin biyan Denmark dala miliyan 100 na zinare don sayen yankin a shekara ta 1946.
Kamfe don neman goyon bayan al'ummar Geenland
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa ƴan Greenland da dama na son samun ƴanci daga Denmark.
Sai dai kuri'un sun nuna cewa mutanen ba sa son zama wani ɓangare na Amurka.
Duk da haka, Amurka za ta yi ƙoƙarin neman goyon bayan ƴan tsibirin ta hanyar samar musu da kuɗaɗe ko kuma alfanu na tattalin arziki a nan gaba.
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa hukumomin leƙen asirin ƙasar tuni suka fara sa ido kan gwagwarmayar neman ƴancin Greenland, inda suke ƙoƙarin gano jagororin da za su mara wa burinsu.
Imran Bayouni, tsohon mai ba da shawara kan tsare-tsare a sashen tsaro na Amurka, ya faɗa wa BBC cewa "kaddamar da kamfe" shi ne abin da zai fi maimakon matakin soji.
Ya ce kamfe ɗin zai taimakawa yankin a ƙoƙarinta na samun ƴanci.
"Bayan Greenland ta ayyana ƴanci, gwamnatin Amurka za ta iya ƙulla alaƙa da yankin," in ji shi. "Kuɗin da za a kashe wajen ɗaukar matakin soji yana da yawa."
Wannan haɗaka ba a matsayin kyauta yake ba.
Alal misali, Amurka ta ƙulla irin wannan yarjejeniya da ƙasashen yankin Pacific na Palau da Micronesia da kuma Marshall - dukka waɗannan ƙasashe suna bai Amurka damar samun hakkoki na tsaro.
Yayin da al'ummar waɗannan ƙasashe ke samun damarmaki na aiki da kuma rayuwa a Amurka.
Sai dai hakan ba zai gamsar da Trump ba, inda yake da ƙarfin ikon aika dakaru da dama son ransa zuwa Greenland karkashin yarjeniyoyi da aka amince da su.
A yanzu, babu wata jam'iyyar siyasa da ke kamfe don zama wani bangare na Amurka a tsibirin.
"Akwai yiwuwar cewa Greenland ya sake zama mamban ƙungiyar Tarayyar Turai," in ji sojan Birtaniyar.
"Kuma, gwamnatin Amurka mai ci na da sauran shekara uku kan mulki, yayin da za a iya cewa al'ummar Greenland kuma na da shekaru 1,000."











