Abin da ya sa aka binne Sardauna a Kaduna maimakon Sokoto

Sardauna

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan cika shekara 60 da juyin mulkin soji na farko a Najeriya, wanda ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin jamhuriya ta farko, wasu na ci gaba da tattaunawa kan tabon da matsalar ta haifar.

Juyin mulkin ne ya yi sanadiyar mutuwar fitattun ƴansiyasa irin su Firaministan Najeriya na wancan lokaci Abubakar Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da takwaransa na Yamma Ladoke Akintola da sauransu.

A yunƙurin juyin mulkin, wanda aka yi a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, wasu hafoshin sojin Najeriya ne suka yi yunƙurin juyin mulki, wanda shi ne na farko da aka fara samu bayan samun ƴancin kai.

Baya ga manyan 'yan siyasa, juyin mulkin ya kuma rutsa da manyan jami'an sojin Najeriya.

Wani abu da yake ci gaba da ɗaukar hankali shi ne yadda aka binne marigayi Sardauna Sokokot a Kaduna, maimakon jiharsa ta Sokoto, kamar yadda aka binne sauran waɗanda aka kashe jihohinsu na asali.

Wasiyyar binne Sardauna

Sardauna

Asalin hoton, Getty Images

Game da abin da ya faru, Dr. Shuaibu Aliyu, masanin tarihi, kuma shugaban gidan adana tarihi na Arewa House da ke Kaduna, ya ce asali shi ma Sardauna a Sokoto yake so a binne shi.

Masanin tarihin ya ce da kan shi Sardauna ya je Sokoto, inda ya nuna wa makusantansa cewa yana so a binne shi a kusa da kakanninsa.

A game da yadda aka binne marigayin, Dr Shuaibu ya ce tun kafin rasuwarsa dama ya yi wasiyyar yadda yake so a binne shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Mafi yawan ƴan gidan sarkin musulmi, yawanci tun daga zamanin Sarki Muhammad Bello a Wurno aka binne su. Shi ma Sardauna sai ya yi wasiyya cewa idan ya rasu a binne shi a kusa da kakanninsa."

Masanin tarihin ya ce an binne Muhammadu Bello a Wurno ne, amma shi Usman Ɗanfodio a Sokoto aka binne shi.

"Muhammad Bello ne ya kafa Sokoto, sai ya mayar da Ɗanfodio can daga Sifawa, amma sai shi ya koma Wurno daga baya. Shi ya sa yawanci sarakunan da suka zo bayan Muhammad Bello a Wurno aka binne su," in ji shi.

Sai dai ya ce akwai Sultan Attahiru, "shi ne Sultan na ƙarshe kuma na 12 a jerin Sarakunan Musulunci tun daga mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodio, kafin turawan mulkin mallaka su ƙwace iko da daular. Shi a Gombe ya rasu."

Ya ƙara da cewa akwai Sarki Tambari da aka cire, aka mayar da shi Wukari, "shi ma a can ya rasu, aka binne shi a can."

"A ɓangaren Sardaunan Sokoto, a daren ranar 15 ga watan aka kashe shi, da aka wayi gari, sai sarkin musulmi na wancan lokacin ya buƙaci a mayar da gawar Sokoto, amma sai ya kasance babu dama saboda an saka dokar ta-ɓaci."

Ya ce a lokacin masu juyin mulkin sun saka dokar hana shiga da fita a Kaduna, don haka babu damar ɗaukar gawar.

"Wannan ya sa dole babu yadda za a yi da gawar face a binne ta a Kaduna. Shi ne marigayi Sheikh Abubakar Gumi ya jagoranci masa wanka da sallah, sannan aka binne shi a gidan sarkin musulmi da ke Kaduna," in ji Dr Shuaibu.

Game da yadda aka yi sauran iyalan Sardauna, masanin tarihin ya ce dama masu juyin mulkin ba su ƙona gidan baki ɗaya ba.

"Asali dama gaban gidan ne ɓangaren Sardauna, akwai wasu sassa a baya. To sauran iyalansa da suke can ɓangaren ba a ƙona musu ɓangarensu ba. Daga baya an kwashe su, an mayar da su Sokoto inda suka ci gaba da rayuwa har suka rasu," in ji shi.

Tarihin Ahmadu Bello Sardauna

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Muhammad Bello, wanda na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa daular Sokoto, kuma ɗa ne ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo.

Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.

Kafin daga bisani Sultan ya naɗa shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka naɗa shi Sardaunan Sokoto, sannan ya halarci ƙasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zaɓe shi mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya ƙasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.

Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaɓen da aka gudanar bayan samun ƴancin kai.

Bayan kammala zaɓe, ya zaɓi ya ci gaba da kasancewa Firimiya na arewa, inda ya zaɓi Abubakar Tafawa Ɓalewa ya zamo Firaministan Najeriya.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji ƴan ƙabilar Ibo suka jagoranta.