Shin Mojtaba Khamenei zai fuskanci ƙalubale wajen jagorancin Iran?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, لیز دوست
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, خبرنگار ارشد بینالمللی
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaba wanda bai taɓa riƙe madafun iko ba ne ya fara jan ragamar jagorancin addinin Musulunci a ƙasar Iran, lamarin da ya zo a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale mafi girma a ƙani biyar.
Sauye-sauye ba shiri ba tsammani ne suka sa Mojtaba Khamenei mai shekara 56 ya zama sabon jagoran ƙasar bayan an kashe mahaifinsa, Ali Khamenei a farkon ɓarkewar yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran.
Shi ne jagoran addinin ƙasar na uku tun bayan kafa Jamhuriyar Musulunci ta ƙasar bayan juyin-juya-halin 1979.
Tuni magoya bayansa suka shiga titunan ƙasar suna murna da taya murna ga sabon jagoran addinin ƙasar, suna ta kabbara suna "Allahu Akbar."
Haka kuma jami'an tsaron ƙasar sun yi mubaya'a ga sabon jagoran, inda suka ɗauki alwashin kare darajar ƙasar da "jininsu."
Sai dai a wani ɓangaren daban, an ga wasu masu zanga-zanga waɗanda suka taɓa yin zanga-zanga a baya suna kiran mahaifinsa da "mai kama-karya" suna kiran "mutuwa ga Mojtaba."
Ga waɗanda suke cigaba da jimamin mutuwar dubban mutanen da aka kashe a lokacin zanga-zanga, naɗa Mojtaba tamkar ƙara fama musu ciwo ne, domin sun san za a ɗaura ne daga inda aka tsaya a baya.
Sai dai ba su yanke tsammani ba cewa za a zo lokacin da mulkin Khamenei zai kawo ƙarshe.
Mojtaba Khamenei ya kasance yana aiki ne a bayan fage a gwamnatin mahaifinsa. Amma yana da masaniya a kan duk wani mataki da aka ɗauka, da yadda ake gudanar da mulkin ƙasar.
Haka kuma yana da alaƙa ta kusa da dakarun juyin-juya-halin ƙasar, kasancewar ya yi aikin soja yana matashi.
Dakarun, waɗanda aka kafa a shekarar 1979, suna aiki ne domin kare jamhuriyar ta Musulunci, kuma yanzu tana da hannu a tsaro da tattalin arzikin ƙasar. Wannan ya sa kwamandojinta suke da matuƙar ƙarfin faɗa a ji a muhimman abubuwan da suka shafi ƙasar.
An ce kwamandojin rundunar sun fi Mojtaba ya gaji mahaifinsa a muƙamin jagoran addinin ƙasar.
Wannan yaƙi ba na siyasa ba ne kawai, yaƙi ne zai iya rikiɗewa zuwa ramakon gayya.
A hare-haren Isra'ila a gidan jagoran addinin, an kashe mahaifin Mojtaba da mahaifiyarsa Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh da matarsa Zahra Haddad-Adel.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An kuma ruwaito cewa ya ji rauni a harin, duk da cewa ba a samu cikakken bayani ba, kuma har yanzu ba a gan shi a zahiri ba.
A daidai lokacin da ake cigaba da maganar naɗa sabon jagoran addinin ne Mr Trump ya bayyana cewa ba zai amince da ɗan marigayin ya karɓi matsayin ba.
Yanzu kuma ya ce Mojtaba Khamenei "ba zai yi ƙarko ba." Haka kuma Isra'ila na haƙonsa, inda ministan tsaron Isra'ila ya kira shi da "wanda suke nema."
Don haka akwai yiwuwar Mojtaba zai kasance yana aiki ne a bayan fage na wani ɗan lokaci.
Ba a taɓa ganinsa yana jawabi ba a taro, kuma ba a cika ganinsa a taro ba, ballantana ma ya riƙe muƙamin gwamnati.
Rahotanni sun ce marigayi Khamenei da kansa ya taɓa cire shi a cikin waɗanda za su iya maye gurbinsa domin ba ya son salon mulkin sarauta ta gado, irin wanda suka kifar a juyin-juya-halin 1979.
Yadda Mojtaba ya ɗare karagar jagorancin ya ƙara nuna cewa masu yunƙurin kawo sauyi suna ƙara fuskantar ƙalubalen koma-baya a mulkin ƙasar.
A siyasance, Khamenei na kusa da manyan masu ƙarfin faɗa a ji ƙasar guda biyu, waɗanda kuma suke da alaƙa da dakarun juyin-juya-hali, wato Ali Larijani da Mohammad Baqer Qalibaf.
A wata tattaunawa jaridar New York Times, Abdolreza Davari ya bayyana Mojtaba Khamenei a matsayin "mai son ci gaba," sannan ya ce yana tunanin Mojtaba zai ɗauki matakan "rage ƙarfin ikon masu tsattsauran ra'ayi."
Ya ce Mojtaba ne zai zama tamkar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman.












