Yadda ƙasashen G7 ke ƙoƙarin kaucewa ƙarancin mai a duniya saboda yaƙin Iran

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
- Marubuci, Nick Edser
- Marubuci, Peter Hoskins
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporters
- Lokacin karatu: Minti 3
Ƙasashen ƙungiyar G7 mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya sun ce a shirye suke su ɗauki duk matakin da ya dace domin ganin ba a samu katsewa jigilar mai ba a duniya saboda yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, wanda ya janyo tashin farashin man.
Sai dai taron ƙungiyar ministocin kuɗi na ƙungiyar G7 da hukumar kula da makamashi ta ƙasa da ƙasa ya tashi ba tare da an cimma yarjejeniya game da yadda za a wadata duniya da man ba.
A ranar Litinin 9 ga watan Maris farashin gangar ɗanyen mai ya kai $120, bayan fargaba kan katsewar jigilar mai sabida yaƙin, amma farashin ya sauka cikin gaggawa bayan shugaba Trump ya bayar da fatan yaƙin zai ƙare nan ba da jimawa ba.
A yayin taron wanda ya gudana ta na'urar bidiyo an tattauna batun da ya shafi safarar mai a sassan duniya, bayan damuwar da aka nuna game da yadda aka samu koma-baya a fannin cikin kwanakin nan.
Shugaban hukumar kula da makamashi ta duniya Fatih Birol ya shaidawa taron cewa ''baya ga ƙalubalen da ke tattare ga safarar mai ta mashigar Mormuz, akwai kuma matakin da aka ɗauka na rage yawan man da ƙasashe ke samarwa wanda ya yi sanadiyyar fargaba a kasuwar duniya.
"Ƙasashen IEA sun dakatar da ganganr mai fiye da biliyan biyu da miliyan dubu ɗari biyu, baya ga wata ganga miliyan 600 da gwamnatoci suka ajiye don ko ta kwana.'' in ji Birol.
A yayin taron, ministan kudin Faransa, Roland Lescure ya ce "kawo yanzu ba mu cimma matsaya ko za a iya sakin man da aka ajiye domin buƙatar gaggawa ba.''
Idan aka fitar da man da aka ajiye domin gaggawa, matakin zai zamo irinsa na farko tun bayan wanda aka ɗauka a 2022 bayan Rasha ta ƙaddamar da kutse cikin Ukraine.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanarwar da ta fitar bayan taron, ƙungiyar G7 ta ce: "A shirye muke mu ɗauki dukkan matakan da suka wajaba domin wadata duniya da mai, ko da kuwa hakan zai kai ga taɓa ajiyar da aka yi domin shiryawa ɓacin rana.''
Katsewar da aka samu ta jigilar mai a gabas ta tsakiya ta janyo barazanar hauhawar farashin mai a sassan duniya lamarin da ya shafi masana'antu da kamfanoni, ya kuma tilastawa manyan bankunan duniya rage yawan kudin ruwa.
Aƙalla kashi biyar na man da ake amfani da shi a duniya na kaiwa ga ƙasashe ne ta mashigar Mormuz. Amma an dakatar da duk wata jigila ta mashigar tun bayan fara yaƙin, fiye da mako guda da ya gabata.
A ƙarshen makon da ya gabata haɗakar Amurka da Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran, kuma ta tarwatsa wurare da dama cki harda matatun mai.
Itama Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan ƙasashen yankin Gulf.
Saudiyya ta ce ta daƙile wasu hare-haren cikin dare da aka ƙaddamar kan matatun mai a ƙasarta.

Adnan Mazarei na cibiyar nazarin tattalin arzikin duniya ta Peterson Institute for International Economics ya ce dama an yi zaton samun tashin farashin na mai, saboda yadda wasu ƙasashen gabas ta tsakiya suka dakatar da aikin tace man, da kuma tasirin da yaƙin Amurka da Isra'ila ka Iran zai haifar a yankin.
Ya ce "A yanzu mutane sun fahimci cewa yaƙin ba zai ƙare cikin sauri ba, kuma alƙawurran da Amurka ta yi a kai suna ƙara zama abubuwan da ba za su tabbata ba.''
Do you have any views, comments or questions about this story?











