Kwamandojin sojin Najeriya uku da aka kashe cikin mako ɗaya

Asalin hoton, HQ Nigerian Army/Facebook
A Najeriya, ana ci gaba da tafka muhawara kan irin ɓarnar da mayaƙan Boko Haram da Iswap suka yi wa rundunar tsaron ƙasar na hallaka mata sojoji manya da ƙanana a wasu hare-hare da suka girgiza ta.
Tuni dai ISWAP ta ɗauki alhakin ƙaddamar da wasu hare-hare kan sansanonin sojin Najeriya a jihar Borno, inda a cikin cikin mako guda kacal ta kashe sojoji da dama bayan kashe fararen hula.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta hannun kamfanin dillancin labarai na Amaq mai alaƙa da mayaƙan na Iswap, ta ce a makon jiya ne ta ƙaddamar da hare-haren.
Sai dai duk da cewa wasu kafofin yaɗa labaran Najeriya sun bayar da rahoton wasu daga cikin hare-hare, alƙaluman sojojin da suka mutun ya sha bamban da iƙirarin ƙungiyar ta ISWAP.
Sai dai a wani salo da ba a saba gani ba ƙungiyar ta bayar da rahoton mutuwar mayaƙanta da dama a gumurzu da jami'an tsaro a lokacin hare-haren
Ƙungiyar ta yi iƙirarin kai hari sansanonin soji har guda huɗu a cikin dare ɗaya, lamarin da ta ce ya yi sanadin mutuwar sojoji.
Sai dai wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato sojojin ƙasar na cewa sun samu nasarar daƙile hare-haren mayaƙan na Iswap a wasu sansanonin da ke jihar ta Borno.
Ko a ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairu ayarin sojojin da suke raka babban hafsan rundunar sojin ƙasan Najeriya ta 8 sun gwabza faɗa domin tsira daga harin ƙwanton ɓauna da Lakurawa ta kitsa musu a jihar Kebbi da ke arewa maso yamma.
Hare-haren nan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin suke iƙirarin samun nasara a yaƙin da suke yi da matsalolin tsaro a faɗin Najeriya.
Kashe kwamandoji

Asalin hoton, HQ Nigerian Army/Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin mako ɗaya tal, rundunar sojin Najeriya ta rasa aƙalla kwamandojin sojin ƙasar guda uku a hare-hare manya da Iswap ta kai a wurare daban-daban a lokutua daban-daban, kamar yadda Jaridar Daily Trust a ƙasar ta ruwaito.
Sai dain rundunar sojin ba ta fito fili ta bayyana mutuwar kwamandojin nata ba, kodayake cikin wasu sanarwayi da ta fitar a baya-bayan nan ta amince da mutuwar dakarunta, cikin hare da wanda ta bayyana da ''jajirtaccen jagora''.
Rundunar tsaron Najeriyar ta yi asarar aƙalla kwamandoji masu yawa a cikin watanni ƙalilan, ciki har da Birgediya Uba Musa da rahotanni suka ce Iswap sun kashe a watan Nuwamban bara.
Daily Trusta ta ce kwamandojin guda uku da aka kashe a cikin mako ɗaya su ne: Manj U.I. Mairiga, wanda yake jagorantar sansanin Mayenti da Laftanal kanar Umar Faruq, kwamandan sansanin Birged 101 da ke Kukawa da Laftanal Kanal S.I Iliyasu wanda yake jagorantar sansanin Konduga.
Wani abu da yake ƙara ɗaga hankalin mutane shi ne yadda aka kai yawancin hare-haren har sansanin sojojin, ko kuma aka musu kwanton ɓauna.
Haka kuma a watannin baya ma an kashe kwamandojin soji a Damasak da Kukawa da Bama.
A ranar Litinin, 9 ga watan Maris ne mayaƙan Iswap suka kai hari a sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Bayanai sun nuna cewa a harin ne mayaƙan suka kashe kwamandan sansanin sojin, Laftanal kanal Umar Faruq tare da wasu sojoji da ba a ƙididdige ba.
A cewar Daily Trust maharan sun kutsa sansanin ne, suka buɗe wuta, inda suka tarwatsa sojojin, suka kuma kashe wasu, sannan suka cinna wa motocin sojoji wuta tare da kwashe makamai.
Kakakin rundunar musamman ta Operation Hadin Kai, Laftanal Kanal Sani Uba ya tabbatar da harin, inda ya ce an kashe wani gwarzon hafsa, amma bai bayyana sunansa ba.
Ko a watan jiya ma rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun yi yunƙurin kutsawa sansanin, amma sojoji suka tare su, tare da tarwatsa su.
A ranar 1 ga watan Maris ne mayaƙan Boko Haram suka kai hari a sansanin soji da ke Mayenti a ƙaramar hukumar Bama.
Harin ya auku ne makonni kaɗan bayan an kashe wasu sojoji a harin da aka kai a sansanin soji da ke Jakana a ƙaramar hukumar Kaga.
A ranar 6 ga watan Maris, kwamandan bataliya ta 222 a Konduga, Laftanal Kanal S.I Iliyasu ya rasu a wani harin mayaƙan Boko Haram, a cewar Jaridar ta Daily Trust.










