Yadda mayaƙan 'Boko Haram suka kwashe wuni biyu suna ta'asa' a Gwoza

Boko Haram

Asalin hoton, Boko Haram

Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar wa BBC harin da ake zargin cewa mayaƙan Boko Haram ne suka kai a garin Ngoshe da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno, Nahum Daso Kenneth ne ya tabbatar da haka a ranar Juma'a, inda ya ce harin ya auku ne a daren ranar Laraba, amma bai tabbatar da adadin waɗanda aka kashe ko sace a harin.

"Lallai an kai hari, amma dai jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar maharan," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa jami'an tsaro na cigaba da ƙoƙarin ceto waɗanda ba a gani ba.

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya ne suka ruwaito cewa an sace sama da mata da ƙananan yara 100 a harin, sannan kuma an ruwaito cewa maharan sun kashe jami'an sojin na Najeriya.

Jihar Borno ce cibiyar ayyukan mayaƙan Boko Haram da Iswap, ƙungiyoyin da suka sahfe sama da shekara 10 suna ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a arewa maso gabashin Najeriya da kuma fadin yankin tafkin Chadi.

Duk da cewa a shekarun baya gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cin galaba a kan ƙungiyar, amma a baya-bayan nan ƙungiyar na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare babu ƙaƙƙautawa kan jami'an tsaro da kuma fararen hula.

Wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar Hadin Kai Laftanar Kamar Sani Uba ya fitar, ta ce rundunar ta yi nasara daƙile harin ƙungiyoyin masu dauke da makamai a garuruwan Gajiram da Gajigana da kuma Mayanti cikin kwana biyu kacan, wato tsakanin 28 ga watan Fabarairu zuwa 1 ga watan Maris.

Abin da ya faru

Umaru Yakubu Kirawa, wani ɗan jarida ne a jihar ta Borno, ya shaida wa BBC cewa mazauna garin sun tabbatar da cewa an kashe mutane da dama, sannan an yi garkuwa da mutane masu yawan gaske.

Ya ce mazauna garin sun shaida masa, "a lokacin ma suna azumi ne. Wasu sun yi buɗe-baki, wasu ma ba su yi ba a lokacin da maharan suka kai musu hari."

Ngoshe gari ne da Musulmi suka fi yawa, sannan an kai harin ne a cikin dare a daidai lokacin da mutane suke buɗe-baki.

Kirawa ya ce garin ƙauye ne, kuma rikicin Boko Haram ya taɓa tursasa mazauna garin su yi gudun hijira, "amma wannan ne hari na farko tun bayan da suka koma garinsu."

'Sun kwashe wuni biyu a Ngoshe'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A zantawarsa a BBC, Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya ce sai da maharan suka yi kusan kwana biyu a garin.

''Ƴan Boko Haram ne ko Iswap suka kai harin. Sun afka wa sojoji sun kore su, sannan suka ƙona makamai suka kwashi wasu, sannan suka cigaba da zama a garin har na kusan kwana biyu," a cewar Sanata Ndume.

Ndume ya ce sai a ranar Alhamis ne sojoji suka koma, suka fatattaki maharan suka sake ƙwace garin.

A game da irin asarar rayuka da aka yi, sanatan ya ce ba su iya ƙididdige adadin waɗanda aka sace, da waɗanda aka kashe ba.

"Amma dai bayanan da muke samu babu daɗin ji. Gawarwaki ne ta ko'ina, kuma har yanzu (safiyar Juma'a) ba a samu nasarar kwaso gawarwaki ba. Don haka ba za mu iya tantance yawan waɗanda suka kashe ba, da kuma adadin waɗanda suka sace a harin," in ji shi.

Sanata Ndume ya kuma tabbatar da cewa akwai sojojin da aka kashe a harin, inda ya ce, "mun ga hotunan sojojin da aka kashe da kuma fararen hula."

Ya ce akwai mutanen gari da dama da suke tsere zuwa garin Pulka, inda suke zaman gudun hijira.

"Dama can garin Pulka suka koma suna gudun hijira a lokacn da rikicin Boko Haram ya yi ƙamari. Gwamna ya bayar da umarni a kai musu kayan agajin gaggawa. Akwai wani sansanin a garin da aka tsugunar da waɗanda suka dawo daga Kamaru."

A cikin bayanin da ya yi wa BBC, Ndume ya ce har yanzu ba a samu damar shiga domin kwaso gawarwakin waɗanda aka halaka ba.

Ndume ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ƙara ƙaimi wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.

"Tun daga shekarar 2009 da muke fama da matsalar Boko Haram zuwa yanzu ai yaƙin sari ka noƙe suke mana. Shi ya sa muka ce a bar komai a fuskanci yaƙin har sai an gama. Idan ba gamawa aka yi, da an ɗan yi shiru, sai su koma. Gayya suke yi su kai hari, sai kuma su sake wata gayyar su kai harin a wani wajen daban," in ji shi.

Sanatan ya ƙara da cewa sojojin ma suna buƙatar ƙarin kayan aiki da ƙarfafa gwiwa, "domin ba zai yiwu ka kai mutum yaƙi ba, sannan a ce ba a biya masa haƙoƙoƙinsa da kyau ba."