Da gaske ne gwamnatin Najeriya ta biya Boko Haram kuɗi don sakin ɗaliban Neja?

Asalin hoton, Boko Haram
Gwamnatin Najeriya ta yi martani kan zargin da wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar waje ta yi cewa ƙasar ta biya Boko Haram ''maƙudan kuɗi'' a matsayin fansa tare da sakin wasu kwadamandojin ƙungiyar da ake tsare da su kafin sakin ɗaliban da ƙungiyar ta sace a jihar Neja.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP, wanda BBC ba ta tabbatar da gaskiyarsa ba ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta biya kuɗaɗe masu yawa ga Boko Haram kafin ƙungiyar ta saki ɗaliban makarantar St Mary's Catholic Church da ke ƙauyen Papiri fiye da 260 da ke jihar Neja.
Sai dai cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labaran ƙasar ya fitar a ranar talata ya ce zargin ba shi da tushe balle makama.
''Gwamnati na jaddada cewa waɗannan zarge-zarge tsantar ƙarairayi ne marasa tushe, kuma an ƙirƙire su ne domin karya gwiwar ƙwarewar dakarunmu da ƙoƙari da sadaukarwar da suke yi ba dare ba rana'', a cewar sanarwar.
Kamfanin dillancin labaran na AFP ya kafa hujja da wasu majiyoyi, waɗanda ya ce suna da masaniya kan batun biyan kuɗin.
Amma gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta lamunci a riƙa amfani da wasu majiyoyi da ba a ambata ba wajen neman zubar wa gwamnati da dokokin ƙasar ƙima ba.
"Don haka domin kare kowace irin shakka, ba a biya kuɗin fansa ba, sannan babu wasu kwamandojin ƴanbindiga da aka saki'', kamar yadda ministan ya yi ƙarin haske.
Ministan ya ce rahotonnin sun saɓa wa musantawar - da ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin Tsaro da hukumar tsaron Farin kaya ta DSS - suka sha yi kan batun biyan kuɗin fansa.
A ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka kai hari makarantar kwana ta St Mary Catholic Church da ke garin Papiri na jihar Neja, lokacin da ɗaliban da ke tsaka da barci.
Ƴanbindigar sun sace ɗalibai da malamai fiye da 260 a lokacin harin, wanda ya ɗauki hankula a ciki da wajen Najeriya.
Sai dai cikin watan Disamba aka sako ɗaliban, a rukuni-rukuni, inda aka saki rukunin ƙarshe da ya ƙunshi ɗalibai 130, ranar 22 ga watan Disamban 2025.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana musguna wa Kiristoci a Najeriya.
Zargin da gwamnatin Najeriya ta musanta.
A ina aka samo rahoton biyan kuɗin fansar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahoton ya fito ne daga Kamfanin dillancin labarai na AFP, wanda ya ce bincikensa ya gano cewa gwamnatin Najeriya ta biya makudan daloli a matsayin kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban makarantar St. Mary da aka sace a jihar Neja.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin labarin ba.
AFP ya ambato wasu majiyoyin sirri har guda huɗu masu alaƙa da yadda aka cimma yarjejeniyar , waɗanda suka yi iƙirarin cewa gwamnatin ƙasar ta biya ''maƙudan'' kuɗi a matsayin fansa kafin sakin ɗaliban na Papiri.
Rahoton ya kuma yi zargin cewa an saki wasu manyan kwamandojin Boko Haram biyu a cikin ɓangaren yarjejeniyar, duk kuwa da haramcin biyan kuɗin fansa ga yanbindiga ƙarƙashin dokokin Najeriya.
A cewar AFP, an ɗauki kuɗin a jirgi mai saukar ungulu zuwa yankin Gwoza - na jihar Borno - mai fama da ayyukan ƙungiyar Boko Haram - a kusa da kan iyakar Kamaru, domin miƙa su ga kwamandan Boko Haram.
AFP ya ce wasu majiyoyi uku ne suka shaida masa cewa an miƙa kuɗin zuwa ga wani kwamandan Boko Haram a yankin mai suna Ali Ngulde.
''Sakamakon matsalar sadarwar da aka samu a yankin, an ruwaito cewa sai da kwamandan ya tsallaka cikin Kamaru mai makwabtaka domin tabbatar da karɓar kuɗin kafin sakin rukunin farko na ɗalibai kusan 100'', a cewar AFP.
Yayin da hare-haren Boko Haram suka fi yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, tun 2009, AFP ya ruwaito cewa tsagin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin wani mutum mai suna Sadiku ne ya sace ɗaliban na Neja.
A baya ma an alaƙanta Sadiƙu da hannu a manyan hare-hare ciki har da harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.
Kawo yanzu dai ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro, Mallam, Nuhu Ribadu - wanda rahoton ya ce shi ne ya jagoranci yarjejeniyar - bai ce komai ba game da lamarin, sai dai a baya ofishinsa ya sha musanta biyan kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban.











