Yadda ƴanbindiga suka sace ɗalibai a Jihar Neja

makarantar

Asalin hoton, BBC Via Zahradden

Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin jihar Neja da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya ta tabbatar da aukuwar hari kan wata makarantar kwana tare da sace ɗalibai da ba a kammala sanin adadinsu ba.

Cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alh. Abubakar Usman ya fitar, ya ce an kai harin ne kan makarantar kwana ta Cocin St. Mary da ke garin Papiri a yankin ƙaramar hukumar Agwara.

Rahotonni daga yankin sun ce ƴanbindiga ɗauke da makamai sun kai harin ranar Alhamis da tsakar dare, lokacin da ɗaliban ke tsaka da barci.

Harin na zuwa ne kwana biyar da sace ɗaliban makarantar sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi tare da sace ɗalibai fiye da 20.

Har ya zuwa yanzu dai ba a gano su ba, kuma tuni shugaban ƙasar ya umarci ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Mohammed Bello Matawalle ya koma jihar domin sanya idanu kan ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban.

Duka wannan na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakan soji kan Najeriya saboda abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.

Sai dai bayanin da hukumomi suka fitar ƙusnhe da sunayen ɗaliban da aka sace a jihar ta Kebbi, ya nuna cewa dukkaninsu Musulmai ne.

Gwamnatin Najeriya ta dage kan cewa matsalar tsaro a ƙasar na shafar dukkanin al'ummar ƙasar ba tare da la'akari da addini ba.

'Mun samu bayanan sirri'

Gwamnatin jihar ta ce dama tuni ta samu bayanan sirri game da barazanar tsaro a yankin - da ke yankin arewacin jihar, lamarin da ya sa gwamnatin ta ɗauki matakin rufe duka makarantun kwanan da ke yankin tare da dakatar da ayyukan gine-gine.

''Amma abin kaico sai hukumomin makarantar St. Mary suka yi gaban kansu suka sake buɗe makarantar ba tare da sanar da gwamnati ko neman sahalewa ba, inda suka jefa rayukan ɗalibai da malaman makarantar cikin hatsari'', in ji shi.

Gwamnatin ta ce tuni ta ƙaddamar da bincike da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban tare da maido da su cikin kwanciyar hankali.

''Gwamnatin jihar Neja na tuntuɓar jami'an tsaro kan matakan da ake ɗauka na kuɓutar da ɗaliban'', in ji Sanarwar.

Yadda aka sace ɗaliban

Allon makarantar

Asalin hoton, BBC Via Zahradden

Cikin wata sanarwa da cocin ta fitar ta ce maharan sun ƙaddamar da harin ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 3:00 na dare a cikin makarantar.

''Ƴanbindiga sun auka makarantar furamare da sakandiren kwana ta St. Mary da ke garin Papiri, tare da sace wasu ɗalibai da malamai tare da harbe maigadin makarantar'', in ji sanarwar.

Cocin ta ce lamarin ya haifar da tashin hankali da ruɗani a cikin hotuna.

Haka kuma cocin ta ce ta yi matuƙar damuwa da harin, tare da yin Allah wadai da shi da kuma kiran al'umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.

'A kan babura maharan suka zo'

Wasu babura kafe a ƙofar shiga makarantar

Asalin hoton, BBC Via Zahradden

Sarkin Papiri, inda lamarin ya faru, Ibrahim Alhaji Ibrahim ya shaida wa BBC ce maharan sun je garin ne a kan babura inda suka karkasu a cikin garin kafin su sace ɗaliban.

''Wasu sun tsaya a bakin kasuwa, wasu kuma suka isa makarantar, inda suka harbe maigadin makarantar, wanda yanzu haka ke kwance a asibiti'',in ji shi.

Ya ƙara da cewa al'ummar garin na cikin tashin hankali da ɗimauta, tun bayan aukuwar harin.

'An tura jami'an tsaro yankin'

Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami'ai yankin domin kuɓutar da ɗaliban.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar ya ce an aika jami'an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru domin kuɓutar da su.

Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba.

Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al'umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban.