Yadda kisan gagarumin mai safarar kwaya ke neman jefa Mexico cikin tashin hankali

Wani jami'in tsao daga ofishin masu gabatar da ƙara riƙe da bindiga a ranar 22 ga watan Faburairun 2026.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Fernando Duarte
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 4

Approved by Andrew Webb, Global Journalism

1700 23.2.26

Kisan da jami'an tsaro suka yi wa Nemesio Oseguera Cervantes a ranar 22 ga watan Faburairu ba ƙaramar nasara bace ga gangamin yaƙi da ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi da ƙasar ke yi.

Amma ta yaya hakan zai shafi gaggan masu safarar ƙwayoyi da ya kafa, da suka zamo wata gagarumar harka?

Wane ne 'El Mencho'

Wani hoton 'El Muncho' da aka wallafa mai ɗauke da saƙon ana neman shi ruwa a jallo kuma za a biya ladar dala miliyan 15 ga duk mai bayanin wajen da za a iya kama shi.

Asalin hoton, Reuters

Mutumin da aka sani da "El Mencho" wani jagoran ƙungiyar Jalisco New Generation Cartel (CJNG) ne, wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙayoyi da ta zamo wadda aka fi tsoro a Mexico cikin shekaru goma da suka gabata.

A ƙarƙashin jagorancin shi, CJNG ta taka gagarumar rawa a harkar safarar miyagun ƙwayoyi a duniya baki ɗaya, tun daga 2011.

Daga baya ƙungiyar ta faɗaɗa harkokin ta, inda ta haɗa da safarar mutane da haƙar zinari ta bayan fage da dai sauran su.

Jerin gwanon jami'an tsaron birnin Mexico suna sintiri.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Jami'an tsaron birnin Mexico suna sintiri jim kaɗan bayan dakaru na musamman sun kashe 'El Mencho'

Me zai faru da ƙungiyar safarar ƙwayoyi ta CJNG?

Ƙwararrun da BBC ta zanta da su sun yi gargaɗin cewa yadda ƙungiyar ta shahara abu ne mai wuya kisan ''El Mencho'' ta tarwatsa ta.

"Mutuwar El Mencho tana da tasiri sosai," in ji farfesa Annette Idler, wata ƙwararra a kan tsaron duniya da ke jami'ar Oxford.

Ta ƙara da cewa "Shi ne jigo a cikin ƙungiyar CJNG, wadda ta zama ƙungiyar masu aikata laifi da aka fi tsoro a Mexico kuma ta yaɗu zuwa sassan duniya.

"Amma bana zaton mutuwar shi za ta zama barazana ga ƙungiyar ko kuma safarar miyagun ƙwayoyin. Za a ci gaba da safara yadda aka saba."

Taswirar da ke nuna bayani kan Fentanyl da aka kwace a kan iyakar Amurka ta mahadar ta da yankin a 2021.
Bayanan hoto, Bayani kan Fentanyl da aka kwace

Tarihi ya nuna yadda irin waɗannan ƙungiyoyi ke yin tujiya da naci sosai bayan mutuwar jagororin su.

Babbar ƙungiyar da ke hamayya da CJNG, Sinaloa Cartel, ta tsallake yanayi da dama da aka kama shugabanta, Joaquin Guzman Loera, da aka fi sani da El Chapo. Kamen baya-bayan nan da aka yi mashi shi ne na 2016.

Farfesa Idler ta ƙara da cewa ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyi sun riga sun shiga dukkan harkokin kasuwanci da na yau da kullum a Mexico.

"Su na samar da guraben ayyukan yi ga jama'ar ƙarƙara.

Wata babbar mota da aka ƙona a kusa da garin Acatlan de Juarez,

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Wata babbar mota da aka ƙona a kusa da garin Acatlan de Juarez, na jihar Jalisco bayan kashe 'El Mencho'

Do cartels expect to lose their leaders?

Jennifer Scotland, wata ƙwararriya kan harkar da ta shafi ƙungiyoyi masu aikata laifuka a cibiyar Royal United Services Institute (RUSI), ta birnin London ta ce dama can ƙungiyoyi irin wannan suna zama cikin shirin ko ta kwana, da tunanin ana iya kamawa ko kashe shugabannin su.

"'An shafe shekaru gwamnatin Mexico na neman El Mencho', don haka babu mamaki ian aka ce ƙungiyar CJNG ta riga ta tsara wanda zai gaje shi.''

Jami'an tsaron Mexico na National Guard su shida a wajen da aka kashe Cervantes.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Jami'an tsaron Mexico na National Guard sun kewaye wajen da aka kashe Cervantes.

Daga jin labarin kisan "El Mencho", sai magoya bayan shi suka bazama kan tituna a Guadalajara, birni na uku mafi girma a Mexico. Sun riƙa ƙone-ƙone da afkawa jami'an tsaro.

Zanga-zangar da kai hari ya faɗaɗa zuwa jihohi 20, ciki harda Birnin Mexico.

Taswirar kasar Mexico da ke nuna jihar Jalisco da Guadalajara da kuma Puerto
Bayanan hoto, Taswirar kasar Mexico da ke nuna jihar Jalisco da Guadalajara da kuma Puerto

Wannan na tabbatar da tsoron da ake yi cewa mutuwar Cervantes za ta iya ruruta wutar matsala rashin tsaro a Mexico.

CJNG ta yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare kan hukumomi da jami'an tsaro da kuma faɗa da ƙungiyoyi masu hamayya da ita.

Jami'an kashe gobara na Guadalajara na ƙoƙarin kashe wutar da ta kama.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Guadalajara an bankawa motoci wuta bayan kisan 'El Muncho'

Ɓarnar da CJNG ke yi a sassan Mexico dai wani abu ne da ake yi kallon na ramuwar gayya kisan shugaban nata.

Akwai kuma wata dambarwar da ake ganin itama za ta tunzura rikicin, wato batun da ya shafi zaben sabon shugaban ƙungiyar.

Shugaban ƙungiyar Sinaloa Cartel, Joaquin 'El Chapo' Guzman

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban ƙungiyar Sinaloa Cartel, Joaquin 'El Chapo' Guzman kenan lokacin da aka kai shi babban filin jirgin sama na birnin Mexico a 2014

Wace barazana sauran ƙungiyoyin safarar ƙwaya ke yi wa jami'an tsaron Mexico?

Akwai kuma fargabar kan yadda hukumomi a Mexico za su iya shawo kai idan faɗa ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyi biyu masu gaba da juna.

Farfesa Idler ta ce yana da kyau a sake nazari da ɓullo da sabon tsari na hukunta masu laifi da kuma ƙoƙarin kawo ƙarshen aikata kaifuka a Mexico.