Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kisan gagarumin mai safarar kwaya ke neman jefa Mexico cikin tashin hankali
- Marubuci, Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Approved by Andrew Webb, Global Journalism
1700 23.2.26
Kisan da jami'an tsaro suka yi wa Nemesio Oseguera Cervantes a ranar 22 ga watan Faburairu ba ƙaramar nasara bace ga gangamin yaƙi da ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi da ƙasar ke yi.
Amma ta yaya hakan zai shafi gaggan masu safarar ƙwayoyi da ya kafa, da suka zamo wata gagarumar harka?
Wane ne 'El Mencho'
Mutumin da aka sani da "El Mencho" wani jagoran ƙungiyar Jalisco New Generation Cartel (CJNG) ne, wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙayoyi da ta zamo wadda aka fi tsoro a Mexico cikin shekaru goma da suka gabata.
A ƙarƙashin jagorancin shi, CJNG ta taka gagarumar rawa a harkar safarar miyagun ƙwayoyi a duniya baki ɗaya, tun daga 2011.
Daga baya ƙungiyar ta faɗaɗa harkokin ta, inda ta haɗa da safarar mutane da haƙar zinari ta bayan fage da dai sauran su.
Me zai faru da ƙungiyar safarar ƙwayoyi ta CJNG?
Ƙwararrun da BBC ta zanta da su sun yi gargaɗin cewa yadda ƙungiyar ta shahara abu ne mai wuya kisan ''El Mencho'' ta tarwatsa ta.
"Mutuwar El Mencho tana da tasiri sosai," in ji farfesa Annette Idler, wata ƙwararra a kan tsaron duniya da ke jami'ar Oxford.
Ta ƙara da cewa "Shi ne jigo a cikin ƙungiyar CJNG, wadda ta zama ƙungiyar masu aikata laifi da aka fi tsoro a Mexico kuma ta yaɗu zuwa sassan duniya.
"Amma bana zaton mutuwar shi za ta zama barazana ga ƙungiyar ko kuma safarar miyagun ƙwayoyin. Za a ci gaba da safara yadda aka saba."
Tarihi ya nuna yadda irin waɗannan ƙungiyoyi ke yin tujiya da naci sosai bayan mutuwar jagororin su.
Babbar ƙungiyar da ke hamayya da CJNG, Sinaloa Cartel, ta tsallake yanayi da dama da aka kama shugabanta, Joaquin Guzman Loera, da aka fi sani da El Chapo. Kamen baya-bayan nan da aka yi mashi shi ne na 2016.
Farfesa Idler ta ƙara da cewa ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyi sun riga sun shiga dukkan harkokin kasuwanci da na yau da kullum a Mexico.
"Su na samar da guraben ayyukan yi ga jama'ar ƙarƙara.
Do cartels expect to lose their leaders?
Jennifer Scotland, wata ƙwararriya kan harkar da ta shafi ƙungiyoyi masu aikata laifuka a cibiyar Royal United Services Institute (RUSI), ta birnin London ta ce dama can ƙungiyoyi irin wannan suna zama cikin shirin ko ta kwana, da tunanin ana iya kamawa ko kashe shugabannin su.
"'An shafe shekaru gwamnatin Mexico na neman El Mencho', don haka babu mamaki ian aka ce ƙungiyar CJNG ta riga ta tsara wanda zai gaje shi.''
Daga jin labarin kisan "El Mencho", sai magoya bayan shi suka bazama kan tituna a Guadalajara, birni na uku mafi girma a Mexico. Sun riƙa ƙone-ƙone da afkawa jami'an tsaro.
Zanga-zangar da kai hari ya faɗaɗa zuwa jihohi 20, ciki harda Birnin Mexico.
Wannan na tabbatar da tsoron da ake yi cewa mutuwar Cervantes za ta iya ruruta wutar matsala rashin tsaro a Mexico.
CJNG ta yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare kan hukumomi da jami'an tsaro da kuma faɗa da ƙungiyoyi masu hamayya da ita.
Ɓarnar da CJNG ke yi a sassan Mexico dai wani abu ne da ake yi kallon na ramuwar gayya kisan shugaban nata.
Akwai kuma wata dambarwar da ake ganin itama za ta tunzura rikicin, wato batun da ya shafi zaben sabon shugaban ƙungiyar.
Wace barazana sauran ƙungiyoyin safarar ƙwaya ke yi wa jami'an tsaron Mexico?
Akwai kuma fargabar kan yadda hukumomi a Mexico za su iya shawo kai idan faɗa ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyi biyu masu gaba da juna.
Farfesa Idler ta ce yana da kyau a sake nazari da ɓullo da sabon tsari na hukunta masu laifi da kuma ƙoƙarin kawo ƙarshen aikata kaifuka a Mexico.