Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce makomar ‘dalaget’ bayan sauya dokar zaɓen Najeriya?
A makon da ya gabata ne, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026, da aka yi wa gyaran fuska.
Shugaban ya sa hannu kan dokar – wadda ta ƙunshi ƙa'idojin yin zaɓukan tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomin yankin birnin tarayya.
A lokacin sanya hannu kan dokar, Tinubu ya ce "babu batun siyasa a cikin wannan gyare-gyare, abu ne na tsari, ƙoƙari ne na cike giɓi da ƙarfafa tsari da kuma samar da tsaftatacciyar hanya ga masu tsarawa da kuma masu yin zaɓuka."
Shugaban na Najeriya ya sanya hannu kan dokar ne bayan hargitsin da aka samu a zaurukan majalisar tarayyar ƙasar da ma zanga-zangar da ƙungiyoyin fararen hula suka yi game da gyaran da aka yi wa dokar.
Ɗaya daga cikin manyan gyare-gyaren da aka yi wa dokokin zaɓen shi ne hanyoyin da jam'iyyu ke bi wajen zaɓen mutanen da za su tsaya musu takara a kujeru daban-daban, wato zabukan fitar da gwani.
'A yanzu babu dalaget'
A baya jam'iyyun siyasa kan yi amfani da wasu wakilai na musamman da ake kira 'deliget' a turance, waɗanda ake zaɓa a matakai daban-daban, tun daga matakin akwati da mazaɓa har zuwa matakin ƙasa.
Dalaget sun yi kaurin suna a baya, musamman lokacin zabukan fitar da gwani.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce a gyaran fuskar da aka yi wa dokar zaɓen ta 2026 an rusa wannan tsari na dalaget.
Malamin jami'ar na da ra’ayin cewa tsarin “deliget na daga cikin abubuwan da suka gurɓata tsarin fitar da ƴantakara da ma zaɓen Najeriya baki ɗaya”.
''Saboda su deliget ɗin nan, idan suka je zaɓen fitar da gwani ciniki suke yi, sukan karɓi kuɗin kowane ɗan takara, kuma idan ba su zaɓe shi ba ba za su mayar masa da kuɗinsa ba'', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ce yana daga cikin dalilan da suka sanya a sabuwar dokar zaɓen ta 2026 aka soke tsarin na dalaget.
''A yanzu sabuwar dokar ta tanadi hanyoyi guda biyu na gudanar da zaɓukan fitar da gwani na ƴantakara'', in ji shi.
Hanyoyin biyu da dokar ta amince da su don zaɓukan fitar da gwani su ne masalaha da kuma ƴar tinƙe ko ƙato-bayan-ƙato.
Me ake nufi da masalaha?
Masalaha shi ne masu sha'awar tsayawa takarar gujera ɗaya a jam'iyyar ɗaya su zauna tsakaninsu su yi sasanci domin janye wa mutum guda, kamar yadda malamin jami'ar ya bayyana.
A wannan zama ƴantakarar da shugabannin jam'iyyu za su zauna tare da ƙulla alƙawura domin cimma masalaha.
A baya ma wasu jam'iyyun kan yi amfani da wannan hanyar, domin fitar da ƴantakara.
Sabuwar dokar zaɓen ta yi tanadin cewa idan wannan hanya ba ta kai ga nasara ba, to sai a je hanya ta biyu, wato ƴanttinke ko ƙato-bayan-ƙato.
Me ake nufi da ƴar tinƙe?
Farfesa Kamilu Fagge ya ce abin da wannan ke nufi shi ne ƴan jam'iyya masu rajista za su fita domin zaɓen mutumin da suke so ya tsaya wa jam'iyyar takara.
''Kuma akan gudanar da wannan zaɓe a matakai daban-daban, kama daga mazaɓu zuwa ƙaramar hukuma da jihar da kuma matakin tarayya'', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ce shi ma wannan tsari akwai guda biyu da ake bi wajen yin sa.
''Na farko shi ne ƴan jam'iyya su bi layi a bayan ɗantakarar da suke so, sai a ƙirga yawansu, domin gane wanda ya yi nasara, ko kuma a yi a asirce, wato a kawo akwati a ajiye sai a bai wa ƴan jam'iyya damar jefa ƙuri'a, in an kammala sai a ƙirga'', in ji Farfesa Fagge.
A ina za a yi zaɓukan?
A baya akan gudanar da zaɓukan fitar da gwanaye a manyan tarukan jam'iyyun.
Don haka a yanzu ma a manyan tarukan za a fitar da gwanayen kamar yadda Farfesa Kamilu Fagge ya bayyana.
''Shi ma mataki-mataki ne, kama daga matakin mazaɓa zuwa ƙaramar hukuma da kuma jiha'', in ji shi.
Sai dai masanin siyasar ya ce a matakin zaɓen wanda zai yi wa jam'iyyar takarar gwamna ko shugaban ƙasa, za a gudanar da zaɓukan ne a wurare daban-daban a ƙananan hukumomi da jihohi amma duka a rana guda.
''Idan za a yi na gwamnoni saboda yawan ƴan jam'iyyar za a gudanar da zaɓukan ne a kowace ƙaramar hukumar, haka ma na shugaban ƙasa za a yi a kowace jiha'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan an kammala sai a tattara sakamakon a aika shi jiha ko tarayya a haɗa shi wuri guda domin fitar da wanda ya yi nasara.
'Shi ma tsarin na da nasa matsaloli'
Manufar yi wa dokar gyara dai shi ne magance matsalolin da ake yawan samu a zaɓukan fitar da gwanaye, lamarin a wasu lokutan ke ƙarewa a kotuna, ko ma su janyo wa jam'iyyar asarar kujerar da ta riga ta ci a babban zaɓe.
Alal misali a shekarar 2019, jam'iyyar APC ta rasa kujerar gwamna da kujerun majalisar dattawa da na wakilai a jihar Zamfara bayan sun riga sun ci zaɓe, sakamakon matsaloli masu alaƙa da zaɓukan fitar da gwani.
To sai dai Farfesa Kamilu Fagge ya ce shi ma wannan tsari yana ƙunshe da nasa matalolin.
''A wasu lokutan ƴan takara kan karɓi katunan jam'iyyar daga hannun ƴan jam'iyyar ta hanyar ba su kuɗi, sai kuma ya kira wasu da ma ba ƴan jam'iyyar ba ya ba su kuɗi da waɗannan katuna domin su zaɓe shi''.
Sannan ya ce ƴan takara sukan tayar da fitina a lokacin da ake ƙirga mutanen da suka goya musu baya a zaɓukan.
''Idan alal misali ɗan takara na farko yana da magoya baya 200 da aka ƙirga masa aka kuma rubuta, to idan ya hango abokin hamayyarsa na da fiye da nasa, idan aka fara ƙirgen kamar an kirga 100 ko 50 sai ya sa magoya bayansa su tayar da fitina, har ta kai ga dakatar da ƙirgen, to idan aka tafi sai a ce mai 200 ne ya yi nasara, tun an kammala ƙirga masa'', in ji shi.