Real Madrid da Barca na fafatawa kan Rodri, Arsenal da Chelsea sun ja daga kan Alvarez

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City za ta fuskanci kalubale wajen ci gaba da riƙe ɗan wasan tsakiya na Spain Rodri a wannan bazarar, inda Real Madrid da Barcelona ke son ɗan wasan mai shekaru 29. (Bild)

Fatan Liverpool na siyan mai tsaron baya na Roma Zeki Celik ya ƙaru bayan da wakilinsa ya yi watsi da yuwuwar komawar ɗan wasan na Turkiyya mai shekaru 29 Juventus. (Mirror)

Arsenal da Chelsea suna matsa wa Barcelona lamba a ƙoƙarinsu na neman ɗan wasan gaba na Atletico Madrid Julian Alvarez mai shekaru 26. (Teamtalk)

Juventus na sa ran daukar mai tsaron ragar Tottenham mai shekaru 29, Guglielmo Vicario, na Italiya a wannan bazarar, amma za ta fuskanci gogayya daga Inter Milan. (Gazzetta dello Sport)

Newcastle za ta sayar da ɗan wasan gaba na Jamus Nick Woltemade ne kawai a wannan bazarar idan ɗan wasan mai shekaru 24 ya buƙaci barin ƙungiyar. (Football Insider)

Arsenal tana gaban Manchester City da Newcastle wajen neman ɗan wasan baya na Sporting mai shekaru 21 Ivan Fresneda. (Fichajes)

Zuwan Fresneda zai iya sa ɗan wasan baya na Ingila mai shekaru 28 Ben White ya bar Arsenal. (Teamtalk)

Manchester United da Arsenal su ne waɗanda ake sa ran za su sayi ɗan wasan baya na Jamus mai shekaru 22 na Eintracht Frankfurt Nathaniel Brown a wannan bazarar. (Caughtoffside)

Chelsea za ta iya ba wa ɗan wasan baya na Ingila mai shekaru 26 Trevoh Chalobah damar komawa Aston Villa a wannan bazarar idan Blues din za ta iya siyan wanda zai maye gurbinsa. (Football Insider)