Ganawar shugaban Uganda da jagoran RSF cin fuska ne ga jama'armu - Gwamnatin Sudan

    • Marubuci, Wedaeli Chibelushi
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Sudan ta yi Allah-wadai da Uganda saboda ta tarbi shugaban ƙungiyar ƴan tawayen RSF, lamarin da ta kira tsantsan rashin damuwa da mutumcin ɗan Adam.

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan da rundunar sojin ƙasar sun ce Uganda ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa saboda tarbar da ta yi wa jagoran RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, mutumin da ake zargin mayaƙansa da aikata munanan laifukan yaƙi da keta haƙƙin ɗan Adam a tsawon lokacin da aka yi ana fama da yaƙin Basasa a ƙasar.

A ranar Juma'a shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ce ya gana da Dagalo a wani gidan shugaban ƙasa da ke birnin Entebbe.

Museveni, wanda ƙungiyar tarayyar Afirika ta naɗa domin tattauna hanyar sasanci tsakanin dakarun Sudan da mayaƙan RSF ya ce ya jaddada buƙatar ''samar da mafita ta hanyar difilomasiyya da kyakkyawan maslaha''.

Amma a wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar a ranar Lahadi 22 ga watan Faburairun 2026, gwamnatin ƙasar ta yi Allah-wadai da matakin Uganda na tarbar jagoran ƴan tawaye, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda ta kira ''kwamandan ƴan ta'adda.''

Sanarwar ta yi kakkausar suka kan ganawar shugaban Ugandan da Degalo, tana mai cewa mataki manuniya ce kan tsabagen rashin mutumta ɗan Adam, wanda ke bayyana yadda ba a damu da halin da jama'ar Sudan ke ciki ba.

Sudan ta ce tana sane da ƴancin Uganda na tarbar duk wanda ya ziyarce ta, amma kuma tarbar Dagalo ya saɓa dokar ƙasa da ƙasa. Har yanzu gwamnatin Uganda ba ta ce komi ba game da wannan zargi.

Amma a wata sanarwa da ya fitar, shugaba Museveni ya bayyana yadda ganawar tasu da Dagalo ta kasance, yana mai cewa ''Kama yadda aka saba, na jadadda buƙatar hawa teburin sasanci da warware matsala a cikin buƙatar wanzar da zaman lafiya domin ta haka ne kawai za a iya samar da zaman lafiya a Sudan da kuma yankin baki ɗaya.''

Shekaru kusan uku kenan Sudan na fama da yaƙin basasa, inda dakarunta ke fafatawa da mayaƙan RSF masu tawaye. Yaƙin ya yi sanadiyar kashe dubun dubatan mutane, kuma ya tilasatawa wasu fiye da miliyan 13 barin gidajensu, wani abu da ya janyo tsananin buƙatar ayyukan jin ƙai da yaduwar yunwa a ƙasar.

Daga RSF har dakarun Sudan, duk babu wanda ya tsira daga zargin da ake yi na aikata cin zarafi da keta haƙƙin ɗan Adam a yaƙin.

A farkon makon da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gano wasu shaidu masu tayar da hankali da ke nuni da irin ɓarnar da RSF ta tafka a birnin El Fasher, wani abu da ta ce ya yi kama da kisan kiyashi.

Tun da aka fara yaƙin gwamnatin Sudan take sukar duk wata ƙasa da ta tarbi shugabannin ƙungiyar RSF.

A shekarar da ta gabata, Sudan ta dakatar da shigar da kayan Kenya cikin ƙasar ta, bayan wani taro da RSF ta yi a Nairobi babban birnin Kenya.

Ita dai Kenya ta ce ta yi taron ne saboda ƙoƙarin kawi ƙarshen yaƙin.

Amma kawo yanzu babu wata alamar kawo ƙarshen rikicin, domin ko a ranar Asabar 21 ga watan Faburairun 2026, RSF ta sanar da ƙwace garin Al-Tina da ke arewacin Darfur, bayan shafe kanaki ana gabza yaƙi.

RSF ta wallaf wani bidiyo da ke nuna mayaƙan ta suna murnar nasarar ƙwace garin.

Go to BBCAfrica.com for more news from the African continent.

Follow us on Twitter @BBCAfrica, on Facebook at BBC Africa or on Instagram at bbcafrica