Wane ne Hamdan Dagolo, da ke iko da rabin ƙasar Sudan?

    • Marubuci, Alex de Waal
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa analyst
  • Lokacin karatu: Minti 9

Mohamed Hamdan Dagolo, wanda ake wa laƙabi da 'Hemedti' ya zamo wani mai ƙarfin tasiri a shugabancin Sudan, inda dakarun ko-ta-kwana na RSF da ke ƙarƙashin shugabancinsa a yanzu suke iko da rabin ƙasar.

RSF ta samu gagarumar nasara a baya-bayan nan bayan da ta ƙwace iko da birnin el-Fasher, wuri na ƙarshe da ya kasance ƙarƙashin ikon gwamnati a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.

Mutumin da masu adawa da shi ke shakkarsa, mabiya Hemedti na yaba masa kan dagiyarsa da karsashi, da ƙudurinsa na kawar da gwamnatin da yake jayayya da ita.

Hemedti bai taso a cikin iyali da suka shahara ba. Iyalinsa sun samo asali ne daga ƙabilar Mahariya wadanda aka sani da kiwon dabbobi, daga yankin Rizeigat masu amfani da harshen Larabci, wadanda ke rayuwa a yankin da ya tashi daga Darfur har zuwa cikin ƙasar Chadi.

An haife shi ne ko dai a cikin shekarar 1974 ko kuma 1975 - babu takamaiman ranar haihuwarsa da aka sani kasancewar ya fito ne daga yankin karkara.

Iyalansa sun koma birnin Khartoum ne a shekarun 1970 da 1980 ƙarƙashin jagorancin baffansa Juma Dagalo, bayan da suka tsere wa yaƙi tare da neman wurin da za su samu abin rufin asiri.

Bayan ya gaza ci gaba da karatu a shekarun yarunta, Hemeti ya koma sana'ar safarar raƙuma zuwa ƙasashen Libya da kuma Masar ta cikin rairayin hamada.

A wancan lokacin Darfur ya kasance yankin Sudan mai fama da rikici - inda talauci da rashin doka suka yi katutu - sannan gwamnatin Shugaba Omar al-bashir ta yi watsi da yankin.

Ƙungiyar ƴan tawayen Janjaweed - ciki har da wani ɓangare da ke ƙarƙashin jagorancin Juma Dagalo - sun kasance suna kai farmaki kan ƙauyukan ƴan ƙabilar Fur da ke yankin, waɗanda su ne ƙabilar asali a yankin.

Waɗannan rikice-rikice ne suka rincaɓe zuwa gagarumin tawaye a shekarar 2003, inda mayaƙan Masalit da Zaghawa da sauran su suka hade da mayakan ƙabilar Fur, inda suka zargi gwamnati, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Larabawa, da yin watsi da su.

A matsayin martani, gwamnatin Omar el-Bashir ta ƙarfafa ƙungiyar Janjaweed a ƙoƙarin daƙile ayyukan ƙungiyoyin na Darfur. Inda Janjaweed ta yi ƙaurin suna wajen ƙona ƙauyuka da kwashe dukiya, da yi wa mata fyaɗe da kuma kashe-kashe.

Tawagar Hemedti na daga cikin wadanda suka yi irin wannan ƙaurin suna, inda rahoton rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka ta ce rundunar tasa ta lalata ƙauyen Adwa a watan Nuwamban 2004, inda ta kashe mutum 126, ciki har da yara 36.

Wani binciken da Amurka ta gudanar ya tabbatar da cewa Janjaweed ta aikata kisan ƙare-dangi.

An kai batun rikicin Darfur a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, inda kotun ta tuhumi mutum hudu, ciki har da shugaba el-Bashir, wanda ya musanta aikata kisan ƙare-dangi.

Ana ganin Hemedti ya kasance ƙarami daga cikin jagororin ƙungiyar, shi ya sa kotun ba ta ambato sunansa ba.

Mutum daya ne cikin manyan jagororin Janjaweed aka iya gurfanarwa a gaban kotun, wato Ali Abdel Rahman Kushayb.

A makon da ya gabata ne kotun ta same shi da laifi a tuhume-tuhume 27 na laifukan take hakkin bil'adama, kuma za a yanke masa hukunci a ranar 19 ga watan Nuwamba.

Shekaru bayan fara lafawar ƙazancewar rikicin na Sudan, a shekarar 2004, Hemedti ya yi amfani da dabarunsa, inda ya samu zama shugabancin wata rundunar tsaro mai matuƙar ƙarfi a ƙasar.

Batu ne na amfani da dama. A wani lokaci ya yi tawaye, inda ya buƙaci gwamnati ta biya sojojinsa maƙudan kuɗaɗe, da neman ƙarin girma da kuma muƙami na siyasa ga ɗan'uwansa.

El-Bashir ya biya masa kusan dukkanin buƙatunsa, inda Hemedti ya amince ya sake komawa cikin gwamnati.

Daga baya, lokacin da wani ɓangaren na Janjaweed ya sake ɓallewa, Hemedti ya jagoranci dakarun gwamnati wajen kawar da su, a wannan lokacin ne ya samu damar karɓe iko da wurin haƙar zinare mafi girma a yankin Darfur, wanda ake kira Jebel Amir.

Nan da nan kamfanin Al-Gunaid mallakin iyalin Hemedti ya zama mafi girma wajen fitar da zinare daga ƙasar ta Sudan.

A shekarar 2013, Hemedti ya buƙaci a tabbatar masa, a hukumance, muƙamin shugaban dakarun ko-ta-kwana na RSF, inda ya kasance ƙarƙashin Shugaba El-Bashir kai tsaye.

Daga nan ne aka shigar da Janjaweed cikin dakarun RSF, inda aka ba su sabbin kayan sarki, da motoci da makamai - sannan aka shigar da sojoji daga ɓangaren gwamnati domin taimakawa wajen ba su horo.

RSF ta samu nasara sosai wajen yaƙi da ƙungiyoyin ƴan tawaye a yankin Darfur, sai dai ba ta samu nasarar a zo a gani ba wajen daƙile mayaƙa a yankin Tsaunukan Nuba, kusa da Sudan ta Kudu, sannan ƙungiyar ta karɓi kwangilar wani ɓangare na kare kan iyakar Sudan da Libya.

Dakarun na RSF sun samu gagarumar nasara wajen daƙile kwararar bakin haure ta hamada wadanda ke tsallakawa ta tekun Meditaraniya, sannan dakarun na Hemedti sun gwanance wajen tatsar kudi a hannun al'umma da kuma safarar mutane.

A shekarar 2015, ƙasashen Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa suka buƙaci Sudan ta tura dakarun da za su yaƙi ƴan Houthi a Yemen.

Dakarun da aka tura sun kasance ƙarƙashin jagorancin wani babban soji da ya yi yaƙi a Darfur, Abdel Fattah al-Burhan, wanda a yanzu shi ne shugaban ƙasar da ke yaƙi da ƙungiyar RSF.

Hemedti ya yi amfani da damar da ya samu wajen yin yarjejeniya ta daban da ƙasashen Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin samar da sojin haya na dakarun RSF.

Yarjejeniyar ta yi nasara. Kuma wannan ne abin da ya haifar da hulɗa mai ƙwari tsakanin RSF da sarkin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed.

Matasa ƴan asalin Sudan da ma waɗanda ke fitowa daga ƙasashe maƙwafta sun riƙa tuɗaɗa zuwa sansanin horo na RSF domin a ɗauke su aiki sanadiyyar kudin da ake samu, inda akan biya su kuɗi har kimanin dala 6,000 a farkon daukar su.

Haka nan Hemedti ya ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar Wagner ta Rasha, inda suke horas da dakarunsa yayin da shi kuma yake samar musu da wasu abubuwan na kasuwanci, ciki har da zinare.

Ya ziyarci Moscow domin sanya hannu a hukumance kan yarjejeniyar a ranar da Rasha ta ƙaddamar da samame a Ukraine. Bayan ɓarkewar yaƙin Sudan, Hemedti ya musanta batun cewa ƙungiyarsa na samun taimako daga Wagner.

Duk da cewa akasarin sojojin RSF sun samu horo sosai, amma lokaci zuwa lokaci sukan yi amfani da mayaƙan ƙungiyoyin ƙabilu wadanda ba su da cikakken ƙwarewa.

Lokacin da gwamnatin Omar el-Bashir ta fara fuskantar matsi mai tsanani sanadiyyar zanga-zanga, sai el-Bashir ya gayyaci Hemedti zuwa Khartoum.

A wannan lokaci Shugaba El-Bashir ya yi wa Hemedti laƙabi da 'garkuwata', inda yake kallon RSF a matsayin rundunar da za ta kare shi daga masu yunƙurin juyin mulki, musamman daga cikin sojojin gwamnati.

Sai dai wannan gurguwar shawara ce. A watan Afurilun 2019 dandazon masu zanga-zanga suka yi wa shalkwatar sojin Sudan ƙawanya suna neman a tabbatar da mulkin dimokuradiyya.

El-Bashir ya umarci sojoji su bude wuta kan masu zanga-zanga. Manyan jami'an sojojin ƙasar - cikinsu har da Hemedti - suka tattauna, inda suka yanke shawarar tuntsurar da gwamnatin Omar el-Bashir.

Wannan mataki ya faranta wa masu rajin tabbatar da dimokuraɗiyya rai.

A wancan lokacin an riƙa yi wa Hemedti kallon mutumin da zai samar wa Sudan sabuwar makoma. Saboda kasancewarsa matashi, mai alaƙa da ƙungiyoyin al'umma da dama kuma wanda ya bayyana kansa a matsayin mai ƙalubalantar tsarin gargajiya da aka ɗora ƙasar a kai.

Sai dai wannan kallo da ake yi masa bai daɗe ba.

Bayan da, shi da shugaban majalisar sojoji ta ƙasar, Burhan suka jinkirta miƙa mulki ga fararen hula, inda daga nan masu zanga-zanga suka ƙara ƙaimi, inda nan take Hemedti ya tura dakarun RSF domin murƙushe su, lamarin da ya kai ga kashe ɗaruruwan mutane, da yi wa mata fyaɗe tare da jefa mutane cikin kogin Nilu, kamar yadda rahoton ƙungiyar kare hakkin bil'adam ta Human Rights Watch ya bayyana.

Hemedti ya musanta cewa an aikata hakan.

Lokacin da matsi daga ƙasashen Amurka da Birtaniya da Saudiyya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya yi ƙamari wajen ganin an samar da zaman lafiya a Sudan, sai jagororin sojin suka ƙulla yarjejeniya da jagororin fararen hula, ƙarkashin jagorancin masu shiga tsakani na ƙasashen Afirka.

A tsawon shekara biyu, an samar da wata gwamnatin hadin gwiwa mai cike da tangarɗa, inda ake da majalisar zartasawa wadda akasarinta sojoji ne, da kuma majalisar wakilai ta fararen hula.

Bayan da kwamitin ƴan majalisa - wanda aka kafa domin binciken kamfanoni mallakin sojoji da rundunar RSF da sauran hukumomin tsaro ya kammala haɗa rahotonsa - wanda zai fallasa yadda Hemedti ke faɗaɗa daularsa, sai Burhan da Hemedti suka kori fararen hula daga gwamnati, sannan suka ƙwace iko.

To sai dai ba da dadewa ba aka ɓaɓe tsakanin manyan sojojin biyu.

Janar Burhan ya buƙaci cewa dakarun RSF su koma karƙashin sojojin gwamnatin Sudan.

Hemedti ya ƙi amincewa da hakan. Kwanaki kadan kafin ranar da aka ajiye ta warware taƙaddamar, sai dakarun RSF suka yi wa shalkwatar sojin ƙasar ƙawanya, suka ƙwace iko da wasu sansanonin soji da kuma fadar shugaban ƙasa a birnin Khartoum.

Sai dai matakin bai kai ga nasara ba. A maimakon haka sai Khartoum ya zama fagen daga yayin da aka riƙa gwabza yaƙi tsakanin dakarun a kan titunan birnin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa an kashe fararen hula kimanin 15,000, kuma Amurka ta bayyana lamarin a matsayin kisan ƙare-dangi. RSF ta musanta wannan batu.

Kwamandojin rundunar RSF sun yaɗa bidiyoyin mayaƙansu na azabtarwa da kashe mutane, lamarin da ya bayyana rashin imani da munanan ayyukan da suka aikata.

RSF da ƙungiyoyin da ke tare da ita sun mamaye wurare da dama a fadin Sudan, sun tarwatsa garuruwa da kasuwanni da jami'o'i da kuma asibitoci.

Ana sayar da tarin kayan da aka kwaso daga garuruwa a kasuwannin da ake wa laƙabi da "Kasuwannin Dagalo" har a ƙasashe irin su Chadi da wasu ƙasashe masu maƙwaftaka. RSF ta musanta cewa mayaƙanta na kwasar ganima daga garuruwa.

Bayan ƙawanyar da aka yi masa a fadar shugaban ƙasa aka riƙa yin ruwan makaman atilare, Hemedti ya samu mummunan rauni a farko-farkon yaƙin, inda ya ɓace daga bainar jama'a.

Bayan watanni ya sake ɓulla, inda bai nuna nadama ba kan ta'asar da aka tafka, sannan ya dage kan cewa sai ya samu nasara.

RSF ta samu dabaru da makaman yaƙi na zamani, ciki har da jirage marasa matuƙa masu inganci, wadanda aka yi amfani da su wajen kai hari kan birnin Port Sudan, inda Burhan ya yi sabon babban birni, kuma sun taimaka wajen hare-haren da aka kai a birnin el-Fasher.

Rahotannin binciken ƙwaƙwaf na kafafen yaɗa labarai, kamar jaridar New York Times, sun tabbatar da cewa ana safarar waɗannan makamai ne ta wani ƙaramin filin jirgin sama da cibiyar safarar makamai, wadanda Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta gina a cikin ƙasar Chadi. Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta cewa tana taimaka wa RSF da makamai.

Sanadiyyar tallafin makamai da RSF ke samu, ya sanya take ci gaba da fafatawa da dakarun Sudan, waɗanda suka yi aiki tare a baya.

Hemedti na son samar da ƙawancen siyasa da ƙungiyoyin fararen hula da kuma na masu ɗauke da makamai, cikinsu har da waɗanda suka yi gaba a baya, kamar na yankin Tuddan Nuba.

Ya kafa wata "gwamnatin zaman lafiya da hadin kai" ta daban a Sudan, wadda yake jagoranta.

Yanzu da RSF ta karɓe iko da el-Fasher, hakan na nufin ita ce ke iko da duk wani yanki da al'umma ke zaune a yammacin kogin Nilu.

Bayan rahotanni masu yawa na kisan-kiyashi da tofin Allah-tsine daga ɓangarori da dama, Hemedti ya bayyana cewa ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan abin da ya kira laifukan da sojojinsa suka yi yayin artabun ƙwace birnin el-Fasher.

Al'ummar Sudan sun yi amannar cewa ko dai Hemedti na ganin kansa a matsayin shugaban gwamnatin yankin da ya ɓalle, ko kuma har yanzu yana da burin mulkin ƙasar Sudan.

Akwai yiwuwar kuma yana kallon kansa a matsayin wani hamsahaƙin ɗan siyasa mai ƙarfin iko, wanda ya mallaki manyan kamfanoni da dakarun sojojin haya da kuma jam'iyyar siyasa.

Hakan na nufin ko da bai zama shugaban Sudan ba, zai kasance mai matuƙar tasiri.

Kuma yayin da sojojin Hemedti ke ci gaba da yi wa fararen hula kisan kiyashi a el-Fasher, yana da ƙwarin gwiwar ci gaba da nuna ƙarfi, a wata duniya wadda ba ta damu da abin da ke faruwa ba.

Alex de Waal shi ne shugaban Gidauniyar Zaman Lafiya ta Duniya a Kwalejin Horas da Lauyoyi da Diflomasiyya da ke Jami'ar Tufts a Amurka.