"Rashin aure da wuri ba gazawa ba ce" - Matar da ta yi aure a shekara 40

    • Marubuci, Mamadou Faye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
    • Aiko rahoto daga, Dakar, Sénégal
  • Lokacin karatu: Minti 6

An haifi Amina Faty a Faransa kuma a can ta yi rayuwarta. Ta yi aure tana da shekara 40, a lokacin da maganganun mutane suka jefa ta cikin matsi. Sai dai, ganin cewa ta girma ne a gidan da akwai cakuduwar al’ada sama da daya, Aminata ta kasance mace mai son ƴanci da kuma samun cigaba. Burinta bai bari maganganun jama'a sun yi tasiri a kanta ba.

Bayan tsawon lokaci mai cike da ruɗani da kuma abubuwa da dama, ta samu mijin aure a lokacin da ta gaji da jiran tsammani, "inda ta yi na'am da yadda rayuwarta take."

Mun yi duba kan labarinta bayan cikar burinta.

"Allah ne ya sa zan haɗu da mijina, babu wani matsi ko takura. Ya kasance cikin harkokin wasanni ni kuma ina buƙatar mai horarwa. Mun fara tattaunawa ne kan samun horo kaɗai, kafin mu san juna har mu zama abokai, inda batun ya zarce zuwa ga aure," a cewar Aminata Faty.

Matashiyar ta bar duk abubuwan da take yi a Faransa, inda ta koma Senegal domin fara rayuwa da kuma kasuwanci, inda ta riƙe wasu mukamai daga 2012 zuwa 2019 har ma da shiga ayyukan taimakon al'umma.

"Kasancewata uwa bai hana ni yin tafiye-tafiye ba, ɗaukar kasada da kuma yin zaɓin da wani lokaci mutane suka kasa fahimta, sai dai hakan bai sa na sauka kan abin da nake son yi ba," kamar yadda Aminata ta bayyana.

Mafarkin ƴanci da walwala

Duk da irin wahalhalun da Aminata Faty take fuskanta, a gefe guda tana da mafarkin abin da take son cimmawa. Tana fatan samun rayuwa mai ƴanci da kuma walwala.

"A kan komai, ina da mafarkin samun ƴanci da walwala: ƴancin zaɓar irin rayuwar da nake so, yanda nake so, abubuwan da nake son yi. Ina son gina wani abu mai ma'ana da kuma zai zaburar da mutane, da zai zama mai amfani, wanda zai girma, ba tare da na keɓe kaina wuri ɗaya ba," in ji ta.

A cewarta, "aure na ɗaya daga cikin abubuwan, sai dai duk da haka ba wai yana nufin har sai ta sadaukar da kanta ba."

"Na yi mafarkin irin rayuwar da na zaɓa wa kaina, ba wai wanda wasu mutane suka yarda da shi ba. Ra'ayoyin mutane ba su taɓa zama cikas gare ni ba." kamar yadda ta bayyana.

Komawa karatu don warkar da raɗaɗi

Ba sabon abu ba ne jinkirta aure a Senegal, abin da ke janyo tambayoyi da yawa daga ɓangaren ƴan‘uwa da abokai. Ga kuma cece-kuce daga wurin al'umma. Sai dai Aminata Faty ba ta damu da hakan ba. Bayan samun saɓani da wani wanda tun da farko ta ɗauka shi ne mijinta, ta tsinci kanta a matsayin uwa wadda ba ta da aure.

"Ban yi aure da wuri ba saboda ban samu mutumin kirki ba. Na ɗauka na same shi a wani lokaci cikin rayuwata, sai dai soyayyar da muka kulla ta jefa ni cikin wani hali maimakon ƙarfafa min. Akwai wahala saboda na tsinci kaina a matsayin uwa mai reno, amma na cigaba da sauran harkokin rayuwata. Ban taɓa jin wani abu ba saboda ban yi aure da wuri ba," in ji ta.

Sai dai hakan bai shafe ta ba ko kaɗan, tun da yanzu ta saka wani buri a gabanta: komawa karatu domin magance raɗaɗin da ta shiga.

"Na bai wa karatuna fifiko matuka, har ta kai na samu digiri na biyu kan ɓangaren aiki da sauran shaidar kammala karatu a ɗaukacin rayuwata. Na jajirce sosai a kan aikina da kuma ganin na samu cigaba saboda warkas da raɗaɗin da na shiga," a cewar Aminata Faty.

Nauyin ra'ayoyin wasu mutane

Duk da irin jajircewa da ƙwarin gwiwarta, Aminata Faty ta fuskanci wasu lokuta na rashin tabbas da kuma kaɗaici kan matsin al'umma.

"A kan komai, na ki miƙa wuya kan matsin rayuwa. Maganganu ko tunanin mutane ba su saka Aminata Faty gaggawar yin aure ba. Ban ce ba zan yi aure ba, kawai dai ban yi gaggawa ba," in ji ta.

"Ba abu ne mai sauki ba. Akwai lokuta da dama na shakku da kuma kaɗaici. Amma na mayar da hankali, samun mutane masu kula a kusa da ni da kuma tuna cewa yadda mutane ke kallona yana saka su fargaba kan zaɓina," in ji ta.

"Sannu a hankali na sauya matsin zuwa ƙarfi. Za ka kauce wa matsin al'umma idan ka amince da kanka yadda ya kamata sannan ka san abin da kake yi," in ji Aminata.

"Akwai ɗabi'ar mutane cewa macen da ba ta yi aure ba idan ta kai shekara 35 ko 40 ba ta kai cikakkiyar mace ba, ko kuma za a ce ta rasa dama a rayuwarta. Waɗannan maganganu da muke yawan karantawa a shafukan sada zumunta suna da tasirin gaske, saboda suna iya hana komai: samun nasara da sauran su," in ji ta.

"A tsawon lokaci, matsayina ya ragu saboda ba ni da miji, har da manta duk abubuwan da na cimma. Duk da haka ina alfahari da abubuwan da na samu a rayuwata. Na kasance ƴar kasuwa tun shekara ta 2019, ina kuma cikin harkar sayar da gidaje da kayan noma. Na kirkiro da wani shiri kan mata, da kuma wata ƙungiya kan matan da aka yi wa kaciya," kamar yadda Aminata ta bayyana.

"Ni mace ce da ke son kawo sauyi nagari, kamar sauran mata. Ba ga aure kaɗai ba, muna kuma duba irin cigaban da muka samu."

Auren da ya sauya komai

"Komai ya sauya, babu abin da ya rage."

Lokacin da Aminata Faty ta sanar da batun aurenta da Cheikh Tidiane Diattara, a watan Nuwambar 2022, mamaki ya dabaibaye ta, kuma ta ji kamar wani nauyi ya sauka daga kanta.

"Akwai abin mamaki sosai, wani lokaci har da jin sauke nauyi. Kamar daga karshe ina cika sharaɗin abin da aka saba yi. Sai dai murna ta karaɗeni, musamman ma waɗanda suka mutunta zaɓina ba tare da sun min alkalanci ba," in ji ta.

Bayan ɗaurin auren, komai ya sauya kan yanda mutane ke kallonta.

"Yadda mutane ke kallo na ya sauya matuƙa. Nan da nan, wasu mutane suka fara kallo na da mutunci, wanda hakan ya dora ayar tambaya. Hakan ya nuna yanda batun aure a tsakanin al'ummomin mu ya zama babban abin da ake son mace ta cimma. Ba ni ce na sauya ba, sai dai yadda mutane ke kallona ne ya sauya," a cewar Aminata.

Shawara ga matan da ba su da aure

Aminata ta nemi bai wa matan da suka shiga matsala irin tata shawara.

"Ina son faɗa wa mata cewa kada su yaudari kansu domin ganin sun farantawa masu suka a cikin al'umma. Aure wani mataki ne na rayuwa, ba wai tilas ba. Ya fi maki ki kasance ke kaɗai cikin aminci kan zama da wanda zai cutar da ke. Yin abu kan daidai a kuma lokacin da kika ga ya fi miki shi ne zaman lafiyarki," in ji ta.

Sai dai, ta tuna babban darasi da ta koya kafin aurenta.

"Wannan lokaci ya koya min haƙuri da jajircewa, da kuma muhimmancin sanin kaina sosai. Na kuma koyi cewa zaman kaɗai zai iya kasancewa lokaci na cigaba, ba wai gazawa ba," in ji ta.

Aminata ta ƙara da cewa abu ne mai muhimmanci ta faɗi labarinta da irin gwagwarmayarta a kafofin sada zumunta saboda ta san akwai mata da yawa da suke "fuskantar irin haka, ko kuma waɗanda ake yi wa matsi kan aure".

Ta ce a yanzu tana zaune cikin farin ciki da mijinta Cheikh Tidiane Diattara.

Tana da shekara 41 yanzu, sannan mijinta kuma 42. Sun haifi ƴarsu ta farko Faly a watan Oktoban, 2023 kuma suna sa ran samun haihuwa na biyu nan ba da jimawa ba.