Hafsatu Ahmadu Bello: Matar da ta sadaukar da ranta domin Sardauna

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shekara 60 bayan juyin mulkin soji na farko a Najeriya, har yanzu tabon da ya bari bai goge ba, kuma abin da ya faru na ci gaba da tasiri a tsarin zamantakewar al’ummar kasar.

Kimanin mutum 22 ne aka yi ittifakin an kashe a lokacin juyin mulki, wadanda suka hada da Firaiministan Nakeriya na wancan lokaci Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan jihar Arewa Ahmadu Bello da na Yamma Ladoke Akintola da kuma wasu da dama.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ita ce Hafsatu, matar Firimiyan Arewa Ahmadu Bello.

A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966 ne wasu sojojin Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Patrick Chukwuma Nzeogwu "Kaduna" suka ƙaddamar da yunƙurin kifar da gwamnatin jamhuriya ta farko.

Baya ga manyan ‘yan siyasa, juyin mulkin ya kuma rutsa da manyan jami’an sojin Najeriya.

Sai dai tabbas tarihin juyin mulkin Najeriya na farko ba zai kammalu ba ba tare da labarin Hafsatu Ahmadu Bello ba, matar da ta kasance tare da Firimiyan a lokacin da sojoji suka riske shi.

Duk da barazanar soji rike da bindiga, Hafsatu ta kasance tare da mijin nata, ta yi kokarin kare shi, lamarin da ya sa aka kashe su a tare.

Kisan Hafsatu tare da Sardauna

A ranar da sojojin suka shirya aiwatar da juyin mulkin, Chukwuma Nzeogwu ne da kansa ya jagoranci kutsawa gidan Sardauna, inda ya kashe Sardaunan, da matarsa da mai tsaron lafiyarsa wato 'Sallama'.

Duk da cewa masu juyin mulkin ba su samu nasarar kafa gwamnati ba, sun samu nasarar kashe jiga-jigan mutanen da suka tsara kashewa a ranar.

Dr. Shuaibu Aliyu, masanin tarihi, kuma shugaban gidan adana tarihi na Arewa House da ke Kaduna, ya ce “Hafsatu jaruma ce”.

"Abin da ya faru a ranar shi ne sojojin sun kutsa gidan Sardauna. Suka fara kashe 'yansanda, sannan suka banka wa gidan wuta, amma duk da haka Sardauna bai fito ba. Sai Nzeogwu ya kutsa gidan da kansa," in ji Dr. Aliyu.

Ya ce bayan Nzeogwu ya kutsa gidan ne sai ya fara kiran sunan Sardauna, "yana ta kiran sunan yana cewa 'ina Sardauna yake?' sai ya kutsa cikin asalin gidan, yana shiga sai ya tarar da shi a tare da iyalinsa," in ji shi.

Masanin tarihin ya ce Nzeogwu bai yi wata-wata ba, sai ya yi harbi domin ya kashe Sardaunan.

"Bayanai sun nuna cewa da ya yi harbin ne, sai Hafsatu ta taso ta rungume Sardauna, sai shi ma 'Sallama' (dogarin Sardauna) ya taso domin ya kare mai gidansa. Nan take su ma Nzeogwu ya harbe su," in ji Dr. Aliyu.

Masanin tarihin ya ce Hafsatu mace ce da ta cancanci yabo matuƙar gaske a tarihin Najeriya, musamman ma tarihin juyin mulkin.

Wace ce Hafsatu Ahmadu Bello?

Asalin sunanta Hafsatu Abdulƙadir Macciɗo, daga zuriyar fitaccen gidan nan na 'Wazirawa' a masarautar Sokoto.

"Da ma tana da dangantaka da shi Sardauna. Ita ƴa ce wajen Abdulƙadir Macciɗo, shi kuma Abdulƙadir jika ne a gidan 'Wazirawa' wato Waziri Giɗaɗo, wanda shi kuma miji ne ga Hadiza Usman Ɗanfodiyo," in ji Dr. Shuaibu Aliyu.

Ya ƙara da cewa shi kuma Saudauna, "jikan Abubakar Raɓah ne, ɗan Muhammad Bello."

Masanin tarihin ya ce hakan ya sa suka zama dangi na kusa, "Ita ta ɓangaren mace, shi kuma ta ɓangaren namiji a cikin zuriyar Shehu Usman Ɗanfodiyo.

Ya ce mace mai ibada ce da ƙoƙari, "ko ranar da lamarin ya auku, tun bayan buɗa-baki, tana zaune ne a ɗaki tana ta ibada har zuwa lokacin da waƙi'ar ta auka musu," in ji shi.

Ya ƙara da cewa ta sadaukar da ranta ne ta hanyar ƙoƙarin kare mijinta daga harbin da Chukwuma Nzeogwu.

"Tare aka harbe su, tare suka mutu, kuma tare aka binne su a gidan Sarkin Musulmi da ke Kaduna. Matan Sardauna uku ne, amma ita kaɗai ce suka mutu tare, aka binne su tare."

A game da ƴaƴan da marigayiyar da rasu ta bari, masanin tarihin ya ce ba ta samu haihuwa ba da marigayi Sardaunan Sokoto.

"Matansa uku ne kamar yadda aka sani, sannan ƴaƴansa uku. Ta biyu Amina Goggon Kano, wadda ta haifa masa Hajiya Inno wato Hadiza da Aisha da Lubabatu. Su ke nan ƴaƴan da ya bari," in ji shi.

Dr Shuaibu ya ƙara da cewa Sardauna ya taɓa samun haihuwar ɗa namiji, amma bai daɗe a duniya ya koma ga Alla tun yana ƙarami sosai.