Ma'aikatar shari'a ta Amurka tana binciken ƴan jam'iyyar Democrat a Minnesota
Ana binciken wasu fitattun ƴan jam’iyyar Democrat biyu a jihar Minnesota, kan zargin yunƙurin daƙile ayyukan jami'an shige da fice na tarayya (ICE), yayin da rikici ke ƙara ƙazancewa tsakanin gwamnatin Trump da shugabannin jihar.
Gwamna Tim Walz da magajin garin Minneapolis Jacob Frey na fuskantar binciken ma'aikatar shari'a ta Amurka game da kalaman da aka yi kan jami'an hukumar shige da fice ta ƙasa (ICE), a cewar abokiyar hulɗar BBC a Amurka CBS News.
Binciken ya zo ne a daidai lokacin da wani alƙali na tarayya ya takaita dabarun da jami'an ICE da sauran jami’an tsaro za su iya amfani da su a Minneapolis, tare da hana amfani da hayaƙi mai sanya hawaye da kuma kame masu zanga-zangar lumana.
Zanga-zangar ta ɓarke a birnin bayan da wani jami'in hukumar ICE ya harbe wata mata Renee Good, mai shekaru 37 har lahira a makon da ya gabata.
Sabbin bayanai kuma sun fito fili a ranar Juma'a game da mutuwar Good.
Jami’an agajin gaggawa sun gano aƙalla raunukan harbin bindiga guda uku a jikin matar da kuma yiwuwar na hudu a kanta, kamar yadda rahotannin da gidan talabijin na CBS ya gani suka nuna.