'Yadda na buɗe ido na ga ƙaton maciji kwance a kan ƙirjina'

    • Marubuci, Tiffanie Turnbull
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sydney
  • Lokacin karatu: Minti 3

A tsakiyar daren ranar Litinin, Rachel ta ɗan mirgina kaɗan a kan gadonta sai ta ji wani abu mai mugun nauyi kwance a ƙirjinta.

Duk da cewa tana cikin magagin bacci, ta yi yunƙurin taɓo karenta, wanda a mafi yawan lokaci suke kwana tare, amma sai ta ji ta cika hannu wani abu mai santsi da sulɓi.

Yayin da Rachel take ƙoƙarin mayar da hannunta cikin lulluɓi sai mijinta ya kunna hasken lantarki na gefen gado, abin da ya gani ba ƙaramin tashin hankali ba ne.

"Sai ya ce min 'Masoyiya kada ki motsa. Akwai mesa kwance a kanki, tsawonta ya kai mita 2.5," kamar yadda Rachel ta faɗa wa BBC.

Daga nan sai batun kawar da kare.

"Na yi tunanin cewa idan kare na ya gane cewa akwai maciji kusa da mu...zai hargitsa wuri."

Sai aka fitar da karen waje - ita kuma Rachel ta fara janye jikinta a hankali.

"A lokacin ina ƙoƙari ne na saɓule jikina ta ƙarƙashin mayafi... a cikin zuciyata ina cewa, anya kuwa zan tsira? Abu ne kamar mafarki'."

Rachel na ganin cewa wataƙila mesar, wadda ba ta da dafi ta shiga ɗakin ta tsakankanin ramukan ƙarfen taga, daga nan ya kwanta a jikinta lokacin da take kwance a kan gado.

Lokacin da ta samu ta sulluɓe jikinta daga ƙarƙashin mesar, Rachel ta yi ƙoƙarin kora macijin zuwa waje ta cikin tagar da ya shigo.

"Yana da tsawo, duk da cewa ya nannaɗe a kan ƙirjina, domin duk da nannaɗewar da ya yi akwai sauran jikinsa a kan taga."

Na kama macijin, amma duk da haka bai yi min wata barazana ba, sai dai na ga yana ƙoƙarin nannaɗe min hannu."

Sai dai mijin nata bai yi wannan jarumta ba, saboda ya tsorata, to amma ita Rachel ko a jikinta, wataƙila saboda ta girma ne a wuri mai yawan macizai.

"Ina ganin idan ka kwantar da hankalinka, ba za su yi maka komai ba."

Sai dai ta ce inda irin nau'in ƙaton kwaɗon nan ne da ke addabar ƙasar, da abin ya sha bamban.

"Ba zan iya jure musu ba (kwaɗi), suna tayar min da hankali. Saboda haka in da kwaɗo ne da hankalina ya tashi sosai."

An dai rabu ba tare da wani ya cutu ba, daga Rachel har macijin.

Mesar 'Carpet snake' wanda ya kwanta a jikin Rachel wani nau'in maciji ne maras dafi wanda ake yawan ganin shi a yankunan ƙasar Australia, kuma suna cin abubuwa kamar ƙwari da tsuntsaye.