Ta yaya maciji ke haɗiye mutum?

Mesa ta kashe tare da haɗiye wata mata a yankin Jambi da ke Indonesoya, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar - amma ta yaya maciji ke iya hadiye mutum?

Mesar ta tare Jahrah mai shekara 50 ce a lokacin da take kan hanyarta ta komawa gida bayan tashi daga inda take aiki a ranar Lahadi da safe.

Tun daga ranar ba a ji ɗuriyarta ba, sai mutanen ƙauyen suka gano wata mesa da cikinta ya yi ɗirkeke - suka kashe ta sai suka ga gawar matar a ciki.

"An gano matar ne a cikin mesar," kamar yadda babban jami'in ƴan sandan yankin Jambi AKP S Harefa ya shaida wa kafafen yada labarai.

Ya ƙara da cewa an samu gawar matar ba wani abu da ya cire daga jikinta. Tsayin mesar ya kai mita biyar, in ji mazauna yankin.

Duk da cewa ba a cika samun irin waɗannan abubuwan ban mamakin ba, ba shi ne karo na farko da irin hakan ya faru a Indoseniya ba.

A shekarun 2017 da 2018 ma macizai sun taɓa hadiye mutum biyu.

Ta yaya maciji ke kai wa mutum hari?

An yi amanna cewa yawancin macizan da suka kashe mutane a Indonesiya a cikin shekara biyar da suka gabata manyan mesa ne.

Tsawonsu kan kai ƙafa 32 ko fiye kuma suna da ƙarfi sosai.

Sukan yi kwanton ɓauna ne idan za su kai wa mutum hari, sai su nannaɗe mutum a jikinsu su murƙushe shi - su kanannaɗe mutum ta yadda zai kasa shaƙar numfashi.

Yawanci rashin shaƙar numfashi ko buguwar zuciya ke kashe mutum cikin mintuna kaɗan.

Mesa kan haɗiye duk abin da ta kashe ɗungurungum. Bakinsu kan wage sosai ta yadda duk abin da suka hadiye yakan shige cikinsu.

Idan mutum suka zo haɗiyewa, "to sukan ci karo da ƴar tangarɗa saboda kafaɗun mutum ba sa tanƙwarewa cikin sauƙi," a cewar Mary-Ruth Low, wata mai bincike kan namun daji kuma ƙwararriya kan abin da ya shafi macizai a Singapore, kamar yadda ta taɓa shaida wa BBC.

Suna cin sauran dabbobi?

Ms Low ta ce "Yawanci abincin mesa mutune ne da dabbobi masu shayarwa, duk da ba su faye cin dabbobi masu jan ciki kamar su kada ba.

Sannan sukan ci ɓeraye da sauran ƙananan dabbobi, in ji ta, "amma akwai wani matakin girma da idan suka kai ba su faye damuwa da cin ɓera ba saboda namansa ba ya isarsu."

"A taƙaice dai za su iya yin girman da za su kai duk wani waje da abincinsu yake."

Hakan kan haɗa da dabbobi masu girma irin su aladu da shanu.

A wasu lokutan sai a ga kamar ba za su iya cinye wasu abubuwan ba saboda girmansu.

A shekarar 2005 wata mesa ta haɗiye wata kada a birnin Florida na Amurka.

A garin hadiyewar ne sai suka yi mutuwar kasko, daga baya mafarauta suka gano gawarwakinsu.

Amma sai dai a wasu lokutan waɗannan macizan kan zama masu tsirfa.

Idan ba su samu abin farautar da suke so ba, sukan ɗauki lokaci ba su ci wani abin kirki ba har sai sun ga babbar dabba da za ta ishe su.

Wannan ne karon farko da mesa ta haɗiye mutum?

A'a, sau biyu irin wannan lamari na faruwa a Indonesia cikin shekara biyar da suka gabata.

A shekarar 2018, an nemi wata mata an rasa a lokacin da take duba shukar kayan miyarta a yankin Sulawesi.

Washe gari aka ga takalmanta da adda da kuma wata mesa kwance a can gefe cikinta ya yi ɓulele.

"Mazauna wajen sun yi zargin cewa maciji ne ya haɗiye matar, don haka suka kashe shi, sannan suka fitar da shi daga lambun," kamar yadda babban jami'in ƴan sandan yankin ya shaida wa AFP.

"An farke cikin macijin aka ga matar a ciki."

Sannan a shekarar 2002, an samu labarin yadda mesa ta hadiye wani yaro ɗan shekara 10 a wajen wasu tsaunuka a Afirka ta Kudu.

A watan Maris ɗin 2017 kuma mesa mai tsawon mita bakwai ta hadiye wani manomi a Sulawesi da ke Indonesia.

A shekarar dai kuma da ƙyar wani mutum daga yankin Suamtra na Indonesiya ya ceci kansa a hannun wata mesa mai tsawon mita 7.8 da ta so hadiye shi a gonar kwakwar manja. Ya tsira amma ya ji raunuka.

Wasu labarai da ake bayarwa sun ce abin na faruwa sosai sai dai ba a samun labaran ne kawai.

Wani masanin tarihin rayuwar ɗan adam Thomas Headland, wanda ya shafe gomman shakaru a cikin ƙabilar Agta, waɗanda mafarauta ne a Philippines, ya ce kashi ɗaya bisa ukun mazan ƙabilar, mesa ke kashe su.