Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matan Gambia ke shan taba ta al'aurarsu
- Marubuci, Azeezat Olaoluwa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist Reporter, West Africa
- Aiko rahoto daga, Gambia
- Lokacin karatu: Minti 8
Gargaɗi: Wannan labarin na dauke da bayanan da ak iya tayar da hankali
Aishatou wadda mu ka sakaya sunanta na gaske, wata uwa ce da maigidanta ya rasu ya bari a ƙasar Gambia.
Ta shaida wa BBC cewa ta kasance mai amfani da ''taba'' har tsawon shekara goma sha biyar, lamarin da daga ƙarshe ya zame ma ta mummunar jaraba.
Taba suna ne da ake kiran garin ganyen taba wanda maza da mata su ka kwashe shekaru da dama su na amfani da shi a yankin yammacin Afirka. Yawancin mutane suna amfani da shi ne ta hanyar shaƙarsa ta hanci, ko cinna masa wuta su zuƙa ko kuma su zuba a baki su tauna.
Sai dai kuma da yawa daga cikin mata irin su Aishatou suna sayen taba a asirce suna niƙe shi su sanya a cikin al'aurarsu don wasu dalilai na daban?
Mun same ta a zaune a ƙofar ofishin ma'aikatan jinya a cibiyar kula da lafiyar al'umma yayin da ta ke halartar taron masu fafutukar yaƙi da amfani da taba, kuma ta bayyana yadda take nadamar fara amfani da ita.
*An sakaya sunayen duk masu amfani da taba da aka tattauna da su
Ana safararta tsakanin mata a asirce
Ana sayar da taba a asirce ta hanyar dillalai, galibi a kasuwannin cikin gida - inda mata ke saye da kuma siyarwa a duk faɗin ƙasar.
An sauya tsarin asali da ake bi na sarrafa taba a cikin ƴan shekarun da suka gabata; Yanzu ana sarrafa garin tabar ne da wasu sinadarai daban-daban da ake kwaɓa su tare.
Lokacin da ta samu juna biyu a shekarar 2021, Aishatou ta ce ta san ya kamata ta daina amfani da tabar - kamar yadda ta yi a lokutan da ta ta ke da juna biyu a baya - amma wannan karon ba ta yi nasarar yin hakan ba.
Tana da yaƙinin cewa jarabar amfani da tabar ce ta yi sanadiyar zubewar cikin da ta yi na ƙarshe da ta yi.
Ta je wurin likitanta a lokacin da ta fahimci jaririn ya daina motsi. "Likitan ya gaya mani cewa [jaririn] ya mutu, don haka sai da suka yi tiyata. Lokacin da suka fito da jaririna, fatarsa ta yi kamar ta ƙone. Na san tabar da na yi amfani da ita ce ta kashe jariri na," in ji ta.
Ba a tabbatar da iƙirarin nata a likitance ba, amma Aishatou ta ce tana jin zafi a cikin al'aurarta a duk lokacin da ta yi amfani da taba.
Aishatou ta ce ta fara amfani da taba ne shekaru da dama da suka gabata domin a tunaninta hakan zai taimaka mata wajen rage kiba da kuma samun ciki. Bai yi ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ba.
"Lokacin da jarabar amfani da taba ta kama ka, ta na mamaye duk wani tunaninka, ta zama kamar ita ke tafiyar da rayuwarka. Dole ne ka ci gaba da amfani da ita domin ka ji kamar kana cikin hayyacin ka. Taba ta sanya mun jin dadi, amma ta rage min sha'awar jima'i," in ji Aishatou.
"Na jarabtu da amfani da ita. na kan yi amfani da ita sau uku zuwa huɗu a rana."
"Na daina amfani da taba bayan da na rasa jaririna, ba tare da sanin cewa na riga na kamu da cutar kansar bakin mahaifa ba," in ji ta, ta bayyana cewa a ƙarshe an tabbatar ma ta da cewa ta kamu da cutar kansa shekara biyu da su ka gabata.
A wani waje kuma mun haɗu da Rashida (ba sunanta na gaskiya ba) tana zaune a ƙarƙashin wata bishiyar mangwaro. Ta shaida wa BBC cewa ta shafe shekara bakwai tana amfani da ita, kuma mijinta bai sani ba. Ƙwalla sun cika ma ta ido a lokacin da ta ke bayanin yadda jarabatar amfani da taba ta mamaye rayuwarta.
Yayin da ta ke tunawa da kanwarta da ta rasu a asibiti ta ce, "Sai da na yi kwana uku ina jinyarta, amma na manta da na ɗauki ƙunshin taba na ba. Sha'awar amfani da tabar ta addabe ni har sai da na fita daga hayyaci na, na kasa mayar da hankali kan komai.''
Yayin da take tafiya zuwa gidan dillalin tabar ta bayyana yadda taba ta zame ma ta tamkar abin buƙata ta yau da kullun.
Matan da BBC ta zanta da su sun shaida mana cewa amfani da taba ta hanyar sanyawa cikin al'aura abu ne mai ɗan karen zafi ga masu amfani da ita a karon farko.
"A karon farko da na yi amfani da ita sai na suma sama da sa'a guda kuma na sha alwashin ba zan sake amfani da ita ba, lokacin da na yi amfani da ita a karo na biyu sai na yi amai da yawa, wanda ta sanya mun ra;ayin amfani da tabar ta ce in ci gaba, zan warware daga baya," in ji Aishatou.
Rashida ta gaskata hakan. "Na fara jin jiri, kamar na kamu da zazzaɓin cizon sauro, daga baya na suma." Ta ce haka ta sake ji a rana ta biyu, "amma a rana ta uku, an ji kamar abin da na daɗe ina yi."
Masu sayar da taba suna ɓoye hajarsu ta hanyar baje kolin wasu kayayyakin sayarwa na daban yayin da suke sakaya garin tabar. Su na sayar wa ne ga abokan cinikinsu da suka furta wasu kalaman sirri na musamman. A kan kuma samu tabar a hannun wasu tsoffin mata da ke yakunnan karkara.
Ramat mai shekara 56 da haihuwa, ta shaida mana cewa ta shafe shekara biyu tana siyar da taba a asirce a wani ƙaramin gari a yankin North Bank.
Ta bayyana cewa ana nannaɗe garin ne a cikin leda kuma a wasu lokutan ana ƙara ƙunshewa a cikin takarda saboda warinsa. Ana sayar da fakiti ɗaya akan kusan 15 Dalasi (senti 20).
Ramat - wadda ba ta da masaniya kan abin da masu samar da tabar ke amfani da shi wurin sarrafa ta - ta ce kasuwancinta yana bunƙasa. Ta na samun ribar kashi 200 cikin 100 akan kowace lita biyar ta garin taba da ta sayar.
Lokacin da ta fara sayar da ita, ta ce ba ta san yadda ta ke jarabtar mutane ba. "Idan na samu wata sana'ar da za ta kawo mun riba, zan daina sayar da ita saboda ba na son in ci gaba da cutar da ƴan uwana."
"Na yi amfani da taba sau ɗaya don magance wata cuta, amma na kusa mutuwa, tun daga ranar, ban sake amfani da ita ba, wasu abokan ciniki sun bayyana mun cewa su ma haka suka ji bayan sun yi amfani da tabar," in ji ta.
Cibiyoyin samar da taba na ƙasa da ƙasa
Hukumomin ƙasar sun yi imanin cewa, hanyoyin da ake bi domin samar da taba sun zarce iyakokin ƙasar, inda masu sayar da taba zuwa har Guinea-Bissau da Saliyo da Casamance da ke ƙasar Senegal.
Gwamnatin Gambia ta ayyana taba a matsayin abu mai cutarwa ga mata da yan mata a shekarar 2020. Amma wannan bai yi wani tasiri ƙasa ba - har yanzu ba a ɗauki matakin doka ba don hana masu sayarwa da masu amfani ita ba.
Ko da yake amfani da taba bai saɓawa doka ba, daga shekara 18 aka amince mutum ya yi amfani da taba kuma akwai damuwa daga ƙungiyoyi irin su gidauniyar kiwon lafiyar mata da ma'aikatar kula da walwalar jinsi cewa yara ma suna amfani da shi.
"Gwamnati ta amince da taba wani sinadari ne da ke cutar da rayuwar matan Gambiya, kuma mun himmatu wajen samar da doka da tsare-tsare don magance shi," in ji Kajali Sonko, mataimakin babban sakatare a ma'aikatar jinsi, yara da jin daɗin jama'a ta Gambia.
Dokta Bai Cham, masanin cututtukan a sashin kula da harkokin kiwon lafiya a Gambiya ya wallafa takarda game da tasirin taba a jiki a shekarar 2023. Ƙungiyarsa ta gano taba "mai yiwuwa ta sami mummunan tasiri kan lafiya" bisa abin da aka riga aka sani game da tasirin sauran taba maras hayaki.
Dr Cham kuma yana yin nazarin sinadarai a kan samfuran taba a matsayin wani ɓangare na ƙarin bincike
A wani ɓangare na wannan binciken ya yi hira da mata 42 da maza 15 waɗanda galibi abokan zama ne na masu amfani da taba ne a yanzu ko kuma waɗanda suka yi amfani da ita a baya. Ya ce fiye da kashi 90 cikin 100 na matan da ya zanta da su suna da alamun cutuwa daga sinadarin nicotine - ciki har da amai da gudawa, fitsari ba ƙaƙƙautawa.
Wasu daga cikin matan da ya zanta da su sun sarrafa ganyen tabar da sinadarin caustic soda.
BBC ta kai wasu samfuran taba - da aka tattara a Essau da Banjul - zuwa ɗakin gwaje-gwaje a Jami'ar Legas don bincike. Sakamako ya nuna abubuwan da suka samo asali na sinadarin pyridine da matakan gubar da suka wuce iyakokin aminci na Hukumar Lafiya ta Duniya.
Gwamnatin Gambiya ta yi amfani da ƙwararrun masana kiwon lafiya da masu fafutuka wajen yaƙi da amfani da taba a cikin al'ummomi da cibiyoyin kula da lafiyar jama'a a faɗin ƙasar. Mista Sonko na ma'aikatar jinsi ya shaida wa BBC cewa an samar da wani shiri na wayar da kai da bayar da shawarwari.
Ƙasar ta kuma fara gina cibiyar sauya ɗabi'ar masu amfani da magunguna ba bisa ƙa'ida ba ta farko farko a watan Maris duk da haka ba a bayyana ko za ta kula masu amfani da taba ba.
Yayin da hukumomi ke la'akari da matakai na gaba da za su ɗauka, tsoffin masu amfani da taba kamar su Aishatou suna yaƙi da taba a matakin farko a cikin al'ummominsu.
"Bana son mata su shiga halin da na shiga."
Rashida ma ta yi nadama da fatan dainawa wata rana. "Idan zan iya samun taimako, tabbas zan daina amfani da ita, ba zan bai wa kowa shawarar yin amfani da taba ba don kada su gamu da jarabta irin ta wa."