Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chimamanda ta zargi asibiti da sakaci kan mutuwar ɗanta
- Marubuci, Makuochi Okafor
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 3
Dangin fitacciyar marubuciyar nan ƴar Najeriya, Chimamanda Ngozi Adichie sun zargi asibiti da sakaci wajen mutuwar ɗanta mai wata 21.
A ranar Laraba ne ɗan nata mai suna Nkanu Nnamdi ya mutu bayan wata gajeriyar jinya, lamarin da ya jefa dangin marubuciyar cikin ''kaɗuwa da jimami''.
Sai dai kwanaki bayan mutuwar danginta sun zargi asibitin da ke Legas da sakaci a mutuwar Nnamdi, ciki har da rashin ba shi iskar shaƙa ta oxygen, tare da yawanta masa maganin sanya barci, lamarin da suka ce ya haifar masa bugun zuciya.
Hukumomin asibitin dai sun bayyana ''Alhininsu'' kan rasuwar yaron, amma sun musanta sakacin da danginsa suka zarge su da aikatawa, inda suka ce suna yin aiki ne bisa ƙa'idar hukumomin lafiya na duniya.
Sun ƙara da cewa an kai Nkanu asibitin ne cikin "mawuyacin hali" kuma yanzu haka ana binciken musabbabin mutuwarsa.
Ƴar'uwar surukar Adichie, Dr Anthea Nwandu, ta gabatar da wasu jerin zarge-zarge kan asibitin a wata hira da ta yi a gidan talbijin na Arise TV a ranar Asabar.
A cikin hirar ta ce daraktan asibitin mai suna Euracare ya shaida wa Adichie cewa an bai wa ɗanta ''maganin sanya barci da ya wuce kima'', wanda shi ne ya haifar masa da bugun zuciya.
Sannan kuma Dokta Nwandu ta zargi ma'aikatan lafiyar da rashin bai wa yaron kulawa da rashin ba shi iskar shaƙa ta oxygen tare da tura shi a kan gadon asibiti ta hanyar da ''ba ta dace ba''.
Ta kuma yi zargin cewa Nkanu ya samu rauni a ƙwaƙwalwarsa saboda rashin wadatacciyar iskar shaƙa
Haka kuma ita ma Adichie ta fitar da irin waɗannan zarge-zargen ta hanyar wani saƙo da ta aike, ya kuma ɓulla a intanet.
Mai magana da yawunta, Omawumi Ogbe ta shaida wa BBC cewa an tsara saƙon ne domin tura wa ''yan'uwanta na kusa'', ba domin sauran al'umma ba.
Ms Ogbe ta ci gaba da cewa: "A yayin da muke takaicin fitar wannan bayanai mai cike da alhini da kaɗuwa, abin da saƙon ya kunsa na nuna sakaci da gazawar asibitn da ya jefa iyalin cikin mawuyacin hali''.
"Muna fatan abin da saƙon ya ƙunsa, wanda cikakken bayani ne kan laifin sakaci da likitocin asibitin suka nuna wa yaron wanda ya haifar da mutuwarsa, ya zama babban abin da muke neman ƙarin bayanai a kai''.
Nkanu na ɗaya daga cikin tagwayen maza da Adichie ta haifa da mijinta Dokta Ivara Esege.
Da yake martani kan zage-zargen, asibitin na Euracare ya aike da ta'aziyyar rasuwar yaron ga iyalansa, amma ya bayana cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa ''rahotonnin da ke yawo kan zargin ba gaskiya ba ne''.
Sanarwar ta ce Nkanu, wanda aka kai asibitin cikin mawuyacin hali, an kai shi bayan an yi masa magani a wasu asibitocin yara biyu, kuma bayan kai shi likitoci ''sun ba shi kulawar gaggawa, kamar yadda dokokin asibitoci na duniya suka tanadar, ciki har da ba shi taimakon gaggawa''.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Domin ba shi kulawa mun yi aiki da wata tawagar likitoci da ba na asibitinmu ba, kamar yadda iyalansa suka buƙata domin tabbatar da duka kulawar da ta dace.''
To sai dai duk da wannan ''ƙoƙari da muka yi'', yaron ya mutu ƙasa da kwana guda bayan kawo shi asibitin.
Kuma yanzu haka ana gudanar da "cikakken bincike" a cewar asibitin na Euracare, yana mai cewa a shirye yake ya gudanar da bincken a bayyane, kamar yadda dokokin binciken suka tsara.
Adichie mai shekara 48, ta haifi ƴarta ta farko a 2016. Sai kuma tagwayen da ta samu a 2024 ta hanyar amfani da dashen ƙwai.
Marubuciyar da ke zaune a Amurka - wadda ta taɓa lashe kyautar marubuta - ta yi ta karɓar saƙonnin ta'aziyya daga cikin da wajen Najeriya.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na daga cikin mutanen da suka aike mata da saƙon ta'aziyyar rashin ɗan nata.
Tsarin kiwon lafiya a Afirka na fuskantar matsaloli da dama kama daga ƙarancin likitoci, da aikin likitoci fiye da kima zuwa yadda likitoci ke haɗa aiki a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.
Yayin da take martani kan zage-zargen mutuwar Nkanu, wata mashawarciyar gwamnan Legas ta ce gwamnatin jihar ''na ɗaukar rayuwar mutane da matuƙar muhimmanci, sannan ba ta ɗaga ƙafa kan sakaci da aikin kiwon lafiya ko rashin ƙwarewa a fannin ba''.
Dokta Kemi Ogunyemi, mataimakawa gwamnan Legas ta musamman kan kiwon lafiya, ta tabbatar da cewa hukumar lafiyar jihar ta fara ''wani cikakken bincike mai zaman kansa da za a gudanar a fayyace kan mutuwar yaron''.
"Kuma duk wani mutum ko wata hukuma da aka samu sakaci ko rashin ƙwarewa ko saɓa wata doka zai fuskanci hukunci daidai laifin da ya aikata,'' in ji Dokta Ogunyemi.
Daga ƙarshe ta buƙaci al'umma ta yi watsi da duk wata jita-jita kan mutuwar yaron yayin da ake tsaka da bincike.