Wane ne ɗan sarkin Iran na ƙarshe da masu zanga-zanga ke son dawowarsa?

    • Marubuci, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 6

Reza Pahlavi, ɗan sarkin ƙarshe na Iran da ke zaman gudun hijira, ya yi kiran sake gudanar da manyan zanga-zanga a ranar Alhamis, bayan sabon jerin zanga-zangar da suka barke a ƙasar.

Babban ɗan sarkin da juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 ya kifar da shi, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta cewa yawan mutanen da suka fito zanga-zangar ya kasance "abin mamakin da aka jima ba a ga irinsa".

Ya ce kuma ya samu rahotanni da ke nuna cewa "gwamnatin na cikin tsananin fargaba, kuma tana ƙoƙarin sake katse intanet" domin hana ci gaba da zanga-zangar.

To amma, me muka sani game da tsohon yariman da ke son dawowa tasiri a harkokin siyasar Iran?

An raini Reza Pahlavi tun daga haihuwarsa domin ya gaji kujerar sarautar Iran, ya kasance yana karɓar horon tuka jirgin yaƙi a Amurka ne a lokacin da juyin juya halin shekarar 1979 ya kawar da mulkin mahaifinsa,

Ya shaida abubuwan da ke faruwa ne daga nesa, yayin da mahaifinsa, Mohammad Reza Shah Pahlavi – wanda ke samun goyon bayan ƙasashen yamma ya yi ta fama wajen neman mafaka a wata ƙasa, kafin daga bisani ya mutu sakamakon cutar daji a Masar.

Rashin mulki da rashin ƙarfi da iyalin suka fuskanta kwatsam ya bar Reza - wanda a lokacin matashi ne, tare da iyalinsa - ba su da ƙasa kuma ba wata madafa ta siyasa, inda suka koma zaman gudun hijira a ƙasashen waje suna dogaro da ƙaramin rukunin masu goyon bayan sarauta da kuma mutanen da ke musu fatan alkhairi.

A shekarun da suka biyo baya, iyalin sun fuskanci masifu da dama.

Ƙanwarsa da ƙanensa duk sun kashe kansu, lamarin da ya sa Reza ya zama mutum ɗaya tilo da ya rage a tsohon gidan sarautar Iran, gidan da mutane da dama suka yi tunanin ya zama tarihin.

Yanzu da yake da shekaru 65, Reza Pahlavi na ƙoƙarin dawo da tasirinsa a siyasar Iran da kuma neman taka rawa wajen tsara makomar ƙasarsa.

Daga gidansa da ke wani yanki a kusa da Washington DC a Amurka, magoya bayansa na bayyana shi a matsayin mutum mai sauƙin kai, ba mai nuna kansa sosai ba.

Ana yawan ganinsa yana zuwa wuraren shan shayi na unguwa tare da matarsa Yasmine, ba tare da tsauraran matakan tsaro ba.

A shekarar 2022, lokacin da wani mutum ya tambaye shi ko yana ganin kansa a matsayin jagoran zanga-zangar Iran, shi da matarsa suka amsa tare cewa "canji dole ne ya fito daga cikin al'ummar Iran da kansu", ma'ana ba daga waje ko mutum guda ba.

Sabunta fata

A ƴan shekarun nan, kalaman Reza Pahlavi sun ƙara zama masu ƙarfi da nuna matsayi.

Bayan hare-haren sama da Isra'ila ta kai a shekarar 2025, waɗanda suka yi sanadin mutuwar wasu manyan janar-janar na Iran, Pahlavi ya bayyana a wani taron manema labarai a Paris cewa a shirye yake ya taimaka wajen jagorantar gwamnatin riƙon ƙwarya idan Iran ta rushe.

Daga bisani, ya gabatar da wani shiri na kwanaki 100 domin tafiyar da irin wannan gwamnatin wucin gadi.

Pahlavi na jaddada cewa wannan sabon ƙarfin gwiwa da yake nunawa ya samo asali ne daga darussan da ya koya a zamansa na gudun hijira, da kuma abin da ya kira "aikin da bai kammala ba" da mahaifinsa ya bari.

"Wannan ba wai yana nufin dawo da abubuwan da suka wuce ba ne," kamar yadda ya shaida wa manema labarai a birnin Paris.

"Manufarmu ita ce tabbatar da makomar dimokuraɗiyya ga dukkan 'yan Iran."

Tarbiyyar sarauta

An haifi Reza Pahlavi a watan Oktoban 1960 a Tehran.

Shi kaɗai ne ɗan sarkin da matsarsa ta biyu ta haifa bayan sauran matan sun kasa haifar masa ɗa namiji.

Ya tashi cikin jin daɗi da walwala, ya kasance a lokacin yana karatu tare da malamai na musamman, kuma tun yana ƙarami ake koya masa yadda zai kare mulkin sarauta.

A lokacin da ya kai shekara 17, an tura shi Texas domin samun horon tuka jirgin yaƙi.

Amma kafin ya dawo ya yi aiki, juyin juya hali na shekarar ya kifar da mulkin mahaifinsa.

Tun daga lokacin, Pahlavi ya zauna a Amurka inda yayi karatun kimiyyar siyasa kuma ya auri Yasmine lauya kuma Ba'amurkiya ƴa asalin Iran, sannan suka haifi 'ya'ya mata uku, Noor da Iman da kuma Farah.

'Gado da ke bambanta ra'ayi

A zaman da yake yi na gudun hijira, Reza Pahlavi ya ci gaba da kasancewa alama mai ƙarfi ga masu goyon bayan sarauta a Iran.

Wasu mutane suna tunawa da zamanin mulkin mahaifin Pahlavi a matsayin lokacin da aka samu ci gaban zamani cikin sauri da kuma alaƙa mai kyau da ƙasashen yamma.

Amma wasu suna tuna lokacin a matsayin lokacin da ake hana mutane 'yanci, da kuma tsoron 'yan andan siriri na Savak, waɗanda ake amfani da su wajen murkushe duk wanda ya nuna rashin goyon baya ga mulki, kuma aka san su da take hakkin ɗan Adam.

A tsawon shekaru, shahararsa a cikin Iran ta bambanta.

A shekarar 1980, ya gudanar da wata liyafar hawan sarauta a birnin Alqahira, inda ya bayyana kansa a matsayin shah (Sarki).

Duk da cewa hakan ba shi da tasiri sosai a aikace, wasu masu adawa sun ce hakan ya rage tasirinsa na yanzu na kira ga gyara dimokuraɗiyya.

Pahlavi ya yi ƙoƙari don ganin ya ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran ƙungiyoyin adawa, ciki har da Majalisar Kasa ta Iran domin gudanar da zaɓe mai inganci da aka ƙaddamar a 2013.

Sai dai yawancinsu sun fafata da rashin jituwa na cikin gida da ƙarancin tasiri a cikin Iran.

Ba kamar wasu ƙungiyoyin adawa da ke zaman gudun hijira ba, Pahlavi koyaushe ya ƙi tashin hankali kuma ya nisanci ƙungiyoyin makamai kamar Mojahedin-e Khalq (MEK).

Ya maimaita kiran sauyin mulki cikin lumana, kuma ya kamata a gudanar da zaɓen ƙasa domin yanke shawara kan tsarin siyasar Iran a nan gaba.

Rigima a ƙasashen waje

A 'yan shekarun nan, Reza Pahlavi ya sake janyo hankali sosai.

A yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a shekarar 2017, an ga yadda masu zanga-zangan suka riƙa tunawa da kakansa "Reza Shah inda suka riƙa yin waƙen Allah ya jikan shi" .

Mutuwar Mahsa Amini a hannun ƴan sanda a shekarar 2022 ta haifar da zanga-zangar ƙasa da ƙasa a Iran, lamarin da ya mayar da Pahlavi cikin hasken kafafen yaɗa labarai.

Ƙoƙarinsa na haɗa kan ƙungiyoyin adawa da suka rabu a Iran ya jawo hankulan ƙasashen waje, amma a ƙarshe bai samu ci gaba mai ɗorewa ba.

Masu suka sun ce har yanzu bai kafa ƙungiya mai ƙarfi ko kafar yaɗa labarai mai zaman kanta ba duk bayan shekaru arba'in yana waje.

Ziyararsa mai zuwa Isra'ila a shekarar 2023 mai cike da ce-ce-ku-ce ta ƙara raba ra'ayi.

Ya halarci taron tunawa da Holocaust kuma ya gana da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Wasu ƴan Iran sun ga wannan a matsayin mataki na dabaru, yayin da wasu suka yi masa kallon raba kawance da ƙasashen Larabawa da Musulmai.

Bayan hare-haren sama da Isra'ila suka kai a cikin Iran kwanan nan, an masa tambayoyi masu wuya.

A wata hira da Laura Kuenssberg na BBC, an tambaye shi ko yana goyon bayan hare-haren Isra'ila da ya saka rayukan fararen hula cikin haɗari da mawuyacin hali inda ya bayyana cewa ba fararen hula Isra'ila ke hari ba kuma ya ce "duk abin da zai raunana gwamnati" mutane da dama a cikin Iran za su yi maraba da shi – maganganun da suka haifar da muhawara mai zafi sosai.

Makomar da ba a rubuta ba

A yanzu, Pahlavi baya gabatar da kansa a matsayin sarki mai jiran gado, sai dai a matsayin jagora wajen tabbatar ta haɗin kai na ƙasa.

Ya ce yana son ya taimakawa Iran wajen gudanar da zaɓe kyauta da tabbatar da doka, da bayar da haƙƙoƙi iri ɗaya ga mata, yayin da ya bar shawarar ko za a dawo da mulkin sarauta ko kafa jamhuriya ga zaɓen ƙasa baki ɗaya.

Magoya bayansa suna ganin shi ne kaɗai shugaban adawa da mutane da yawa suka sani kuma mai tsawon lokaci yana goyon bayan sauyi cikin lumana.

Amma masu sukar sa na cewa yana dogaro sosai da tallafin ƙasashen waje, kuma ba a san ko 'yan Iran na cikin gida sun shirya amincewa da shugaba da ke gudun hijira ba bayan shekaru da rikice-rikicen siyasa.

Gwamnatin Iran na ganin shi a matsayin barazana, amma ba za a iya auna goyon bayan sa ba har sai an samu gudanar da siyasa ta ƙididdga mai sahihanci.

Wasu 'yan Iran har yanzu suna girmama sunan iyalinsa; wasu kuma suna tsoron maye gurbin shugaban da ba a zaɓa ba da wani, ko da a karkashin dimokuraɗiyya ne.

Jikin mahaifinsa na nan a binne a Cairo, inda masu goyon bayan sarauta ke fatan wani lokaci zai dawo zuwa Iran mai ƴanci.

Ko yariman da ke gudun hijira zai ga wannan rana, har yanzu wannan tambaya ce da ba a amsa ba game da ƙasa da ke ci gaba da fama da abubuwan da suka gabata.