Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kadarorin Malami da kotu ta miƙa wa EFCC
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi na ƙwace kadarori 57 na tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, inda ta ce kadarorin mallakin Malami da ƴaƴansa biyu - Abdulziz Malami da Abiru-Rahman Malami ne, kuma tana zargin an mallake su ne ta hanyar da ba ta dace ba.
Mai shari'a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin, bayan lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho ya buƙaci hakan.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an ƙiyasta darajar kadarorin za ta kai naira N213,234,120,000, waɗanda ta ce ya mallaka a jihohin Kebbi da Kano da Kaduna da Abuja.
Kotun ta ce a wallafa hukuncin wucin-gadin ƙwace kadarorin, sannan ta yi kira ga "duk wanda da ke da alaƙa da kadarorin kuma yake ganin bai kamata a ƙwace su na dindindin a miƙa wa gwamnatin tarayya ba, da ya fito ya yi bayani a cikin kwana 14."
A ƙarshe alƙalin ya ɗage shari'ar zuwa raar 27 ga Janairu domin ci gaba.
Kadarorin da kotu ta mika
A makon da ya gabata ne hukumar EFCC ta ce ta gano wasu kadarorin da kuɗinsu ya kai naira biliyan 212, waɗanda ta ce tana zargi mallakin tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ne.
Daga cikin kadarorin akwai otel-otel da gidajen zama da fulotai da makarantu da shaguna sannan ta ce ta gano su ne a Abuja a Kano da jiharsa ta Kebbi.
Wasu daga kadarorin sun haɗa da:
Ginin Jami'ar Rayhaan
- Gidan alfarma a Maitama da darajarsa ta kai N5,950,000,000.
- Manyan gidaje biyu a Garki da darajarsu ta kai N7,000,000,000.
- Fili da a ciki akwai otel da darajarsa ya kai N8,400,000,000.
- Fuloti a Asokoro da da aka saya a Janairun 2018 a N360,000,000.
- Gini a Maitama da darajarsa ta kai N12,950,000,000.
- Fuloti a Asokoro da aka saya a Yulin 2012 a N325,000,000.
- Shago a Wuse II da aka saya a Maris ɗin 2024 a N120,000,000.
- Fuloti mai girman hekta 100 a jihar Kebbi da aka saya a 2020 a N100,000,000.
- Gida a Kebbi da aka saya a 2023 a N101,000, 000.
- Shaguna a Wuse 2 da aka saya a Yulin 2023 a N158,000,000.
- Gida a Kaduna da aka saya a Janairun 2018 a N40, 000, 000.00.
- Shagunan adana kaya biyu a Kasuwar Wuse da ke Abuja da aka saya a Yulin 2020 a N50,000,000.
- Otel a Kano mai ɗaki 131 da ya kai N11,200,000,000.00
- Wani otel a Kano da ya kai N280,000,000.00
Ban nemi ba alƙali cin hanci ba - Malami
A wata sanarwa da ofishin Malami ya fitar bayan hukuncin, ya ce ko kaɗan bai yi yunƙuri ko neman hanyar bai wa alƙacin cin hanci domin ya samu sauƙi ba.
Malami ya jawabin ne a matsayin martani, bayan an samu wani rahoto da ke cewa alƙalin ya bayyana cewa ba ya karɓar rashawa.
"Babu wani daga lauyoyin malami ko ɗan'uwa ko dangi da ya yi yunƙurin nema ko ma ya yi tunanin zuwa kotu ko zuwa wajen alƙalin kotun domin neman wani taimako. Duk wata magana da ake yaɗawa ƙarya ce kawai."
Sanarwar wadda mai magana da yawunsa, Mohammed Bello Doka ya fitar ta ƙara da cewa tsohon ministan mutum ne mai bin doka da oda, "wanda ya kai matakin babban lauyan Najeriya wato SAN, kuma tsohon ministan shari'a wanda ke matuƙar girmama ɓangaren."
Sanarwar ta ƙara da cewa malami da lauyoyinsa sun san halin alƙalin na ba sani ba sabo, "don haka ba zai taɓa yiwuwa ba a yi yunƙurin nemansa da wani abu da bai dace ba."
"Don haka ya kamata a gane cewa maganar da mai shari'a ya yi a kotu, magana ce gama-gari, inda yake gargaɗin ga dukkan lauyoyi kamar yadda ya saba jan hankali da gargaɗin lauyoyin da suka bayyana a gaban shi kan illar cin hanci. Don haka ba wai da Malami yake yi ba ko lauyoyinsa."